Ƙurar da ta biyo bayan ƙarin kuɗin kira da data a Najeriya

Ƴan Najeriya na ƙorafi kan

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

Tun bayan da ƙarin kuɗin kiran waya da na data da kamfanonin sadarwa suka yi, ƴan Najeriya suke ta kiraye-kiraye ga hukumomin da abin ya shafa da su ɗauki matakin da zai tilasta kamfanoni sauya sabuwar matsayar tasu.

Ƴan Najeriya dai sun wayi garin ranar Talata da sabon ƙarin ba tare da wata sanarwa ba daga kamfanonin inda hakan ya harzuƙa su har wasu na kira ƴan ƙasar su ƙaurace wa amfani da layukan kamfanonin.

Sai dai daga bisani kamfanin MTN a shafinsa na X, ya nemi afuwar ƴan ƙasar kan abin da ya kira cewa matakin dole ne kuma an yi ne domin inganta tsarin kiran wayar da amfani da data.

Bisa bincike da BBC ta yi ta gano an yi ƙarin ne da kusan kaso 150 maimakon kaso 50 da hukumar kula da sadarwar ta ƙayyade.

Wannan ne ya sa ƴan Najeriyar ke ta tambayar ko wane ne ke da alhakin ƙwato musu haƙƙinsu kan ƙarin?

Yanzu haka dai majalisar dokokin Najeriya da ƙungiyar ƙwadago ta ƙasar sun ja daga kan batun.

Ƙungiyar NLC ta nemi a ƙaurace wa kamfanonin

Joe Ajero

Asalin hoton, Others

ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya, NLC ta nemi kamfanonin sadarwar na da ke aiki a Najeriya da su janye sabon farashin su kuma koma wa tsohon farashi cikin gaggawa.

A wata takardar bayan taro da ƙungiyar ta fitar wanda ta gudanar ranar Talatar nan a birnin Lokoja na jihar Kogi, NLC ta ɗauki wasu matakai guda bakwai kan al'amarin kamar haka:

  • Janye ƙarin farashin da komawa tsohon farashi har zuwa lokacin da kwamitin da ƙungiyar ta kafa ya kammala gudanar da bincike.
  • Ƙungiyar ta buƙaci ma'aikatan Najeriya da sauran ƴan ƙasa da su ƙaurace wa kiran waya ko amfani da datar kamfanonin MTN da Airtel da Glo a kowacce rana daga ƙarfe 11:00 na safe zuwa ƙarfe 2:00 na rana na kowace rana har zuwa ƙarshen watan Fabrairu.
  • Ta umarci ƴan Najeriya da su daina sayen data daga kamfanonin
  • Ƙungiyar na buƙatar kamfanonin su dawo wa Najeriya da kuɗaɗen da suka kwashewa ƴan ƙasar
  • Ƙungiyar za ta jagoranci rufe ayyukan kamfanonin ranar 1 ga watan Maris idan dai har ba su janye sabon ƙarin da suka yi ba ya zuwa ƙarshen watan Fabrairu.
  • Ƙungiyar ta umarci dukkannin rassanta na jihohi da su zaburar da mambobinsu gabanin 1 ga watan na Maris.
  • Ƙungiyar ta umarci dukkan sauran sassanta da su ja hankalin mambobinsu wajen ƙaurace wa kira ko amfani da datar kamfanoni a sa'o'in da aka ayyana

Matakin da majalisar wakilan Najeriya da ɗauka

Majalisar wakilai

Asalin hoton, House of Reps/FACEBOOK

Majalisar wakilan Najeriya ta buƙaci hukumar da ke kula da kamfanonin sadarwa ta ƙasar, NCC ta janye karin kuɗin kira da na data da kamfanonin sadarwar suka yi.

Majalisar wakilan ta ce yin ƙari a wannan lokacin ba adalci ba ne saboda ƴanƙasar na cikin matsin rayuwa.

Hon. Umar Ajilo ɗan majalisar wakilai daga jihar Kaduna ya shaida wa BBC cewa majalisar ba za ta amince da wannan ƙarin ba.

''Duba da irin wannan yanayi da ƴanƙasa ke ciki na matsin rayuwa da rashin aikin yi da rashin abubuwan more rayuwa, ba yadda za a yi, a yi musu ƙari, wannan bai kamata ba'', a cewar ɗan majalisar.

Ya ƙara da cewa la'akari da rashin kyawun sadarwar da ake fama da ita a ƙasar, ƙarin bai dace ba.

Ɗan majalisar ya ce idan abin ta ci tura, majalisar ka iya gayyato jagororin hukumar NCC domin su su yi mata bayani kan dalilin ƙin janye matakin.

Me NCC ke yi kan lamarin?

Yanzu haka dai kallo ya koma ga hukumar da ke sa ido kan harkokin sadarwa ta Najeriya wato NCC wadda ita ce ta bai wa kamfanonin damar yin ƙarin da bai wuce kaso 50 cikin ɗari ba kamar yadda suka nema.

Har kawo yanzu hukumar ba ta uffan ba duk da cewa wata majiya daga cikin hukumar ta tabbatar wa da BBC cewa "yanzu haka ana bincike dangane da yadda kamfanonin suka yi ƙarin da wuce abin da hukumar ta sahhale musu."

Majiyar ta ƙara shaida cewa nan ba da jimawa ba hukumar ta NCC za ta fitar da sanarwa dangane da matsayarta.

Sai dai kuma wata majiyar a hukumar da ita ma ba ta son a faɗi sunanta ta shaida wa BBC cewa al'amarin ya fi ƙarfin hukumar kasancewar an "ƙwace ragamar komai daga hannunta"

"Abin kunya ace an yi wannan ƙarin ba tare da sanayyar hukumar NCC ba. Kuma hakan na faruwa sakamakon wasu da suka ƙwace ragamar ayyukan hukumar." In ji majiyar.