Me ya sa Trump zai ƙara lafta harajin kashi 100 kan kayayyakin China?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Natalie Sherman
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Business reporter
- Lokacin karatu: Minti 3
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai ƙara lafta harajin kashi 100 kan kayayyakin ƙasar China daga watan gobe.
Trump ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya wallafa a shafukansa na kafofin sadarwa.
Tun kafin wannan barazanar, Trump ya yi wani jawabin a ranar Juma'a inda ya caccaki matakin China na saka wasu dokokin kan fitar da duwatsu masu daraja daga ƙasar, lamarin da Trump ya zargi China da yunƙuri "na juya ƙasashen duniya."
Ya kuma yi barazanar fasa ganawar da ake shirin yi tsakaninsa da shugaban China, Xi Jinping, duk da cewa daga baya ya ce ba soke zaman ya yi ba.
"Duk da haka zan gana da shi," in Trump a tattaunawarsa da manema labarai a fadar gwamnatin Amurka.
Alƙaluman hada-hadar kasuwannin duwatsun masu daraja sun nuna cewa kasuwancinsa na samu koma-baya tun bayan jawabin na Trump, inda kamfanin S&P 500 ya yi asarar kusan kashi 2.7, wanda shi ne mafi girma da kamfanin ya samu tun a watan Afrilu.
China ce kan gaba wajen sana'antawa da fitar da duwatsun, waɗanda suke cikin muhimman kayayyakin da ake buƙata wajen haɗa motoci da wayoyin salulu da wasu kayayyakin buƙatu musamman masu amfani da lantarki.
A lokacin baya da Beijing ta matse hanyoyin fitar da kayayyakinta bayan Trump ya ƙaƙaba wa kayayyakin ƙasar haraji a karon farko.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A sanadiyar haka ne ma kamfanonin Amurka da dama suka nuna rashin jin daɗnsu kan matakin, inda har kamfanin motoci na Ford ya dakata da aiki na wani ɗan lokaci.
Bayan matsa lamba kan dokokin fitar da duwatsun, China ta fara bincike kan zargin kaka-gida da ake yi wa wani kamfanin sadarwa na Amurka Qualcomm wanda zai iya haifar masa da cikas.
Duk da cewa kamfanin na Qualcomm a Amurka yake aiki, yawancin harkokinsa a China yake gudanarwa.
Ƙasar ta China ta kuma ce za ta fara karɓar haraji kan jiragen ruwan da suke da alaƙa da Amurka, ciki har da mallakin kamfanonin China.
"Wasu abubuwa masu ban mamaki na faruwa a China," kamar yadda Trump ya wallafa a shafukansa na sada zumunta a ranar Juma'a.
Tun a watannin baya ne dai Amurka da China suke ta fama da takun-saƙa kan haraji, kafin ƙasashen biyu suka amince su janye manyan harajin da suka ƙaƙaba wa kayayyakin juna.
A lokacin sai kayayyakin na China suka koma harajin kashi 30, wanda ragi ne a kan abin da Trump ya ayyana a farkon shekara, sai kuma kayayyakin Amurka suka koma harajin kashi 10.
Hukumomin ƙasashen biyu sun sha ganawa da juna domin tattauna batutuwa da suka shafi TikTok da kasuwancin kayayyakin noma da kasuwancin duwatsun da kayan da ake buƙata wajen kimiyya da fasaha.
Ana kuma sa ran shugabannin ƙasashen biyu za su gana a ƙasar Koriya ta Kudu.
Jonathan Czin mai bincike ne a cibiyar masana ta Brookings Institution da ke China, ya ce shugaban China Xi na ɗaukar waɗannan matakan ne domin shirin fuskantar tattaunawarsu ta gaba.
Ya ce yana tunanin China ba za ta damu ba don Amurka ta mayar da martani kan wannan matakin.
A zagayen farko, China ta buƙaci haɗin kan Amurka domin samun rangwame a harajin ƙananan na'urorin haɗa kayayyakin lantarki wato semiconductors. Haka kuma ta buƙaci a sake duba haraje-hareje domin kayayyakinta su riƙa tagomashi a cikin ƙasar ta Amurka.
A baya ma dai Xi ya yi amfani da duwatsun masu daraja wajen nuna ƙwanji ga ƙasar ta Amurka.
Amma a tsare-tsaren fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje, an ga alamar wannan karon China ta ƙara ƙaimi kan fitar da duwatsun, inda ake tunanin tana harin kamfanonin haɗa kayayyakin tsaron ƙasashen waje.
Gracelin Baskaran, darakta ce a cibiyar albarkatun ƙasa da tsaro a cibiyar Center for Strategic and International Studies da ke Washington, ta ce wannan matakin na China zai shafi Amurka sosai.
"Babu abin da yake ɗaga hankalin Amurka kamar taɓa harkokin tsaronta," in ji ta.
"Dole Amurka ta nemi sulhu saboda ba mu da yadda za mu yi. A wannan lokacin da ake ƙara samun hargitsi a duniya, dole muna buƙatar ƙara ƙaimi wajen inganta masana'antun harkokin tsaronmu," in ji ta.
Duk da cewa ganawar Trump da Xi yanzu tana lilo, ta ce har yanzu akwai yiwuwar za su gana.
MS Baskaran ta ce har yanzu akwai lokaci da damar sake shirin ganawar, saboda a cewarta, "ai dama sababbin dokokin na China ba za su fara aiki ba sai a watan Disamba mai zuwa."
"Lallai akwai damar su sasanta idan sun gana," in ji ta.











