'Madrid ta ɗimauce kan sukar alƙalan wasa'

Javier Tebas

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Shugaban gasar ƙwallon ƙafa ta Sifaniya - La Liga, Javier Tebas ya ce 'yan Real Madrid sun ɗimauce bayan da ƙungiyar ta yi kakkausar suka da ba a taɓa yi ba a kan alƙalan wasan gasar.

A ranar Asabar ɗin nan ne Real Madrid ta aike da takardar ƙorafi ga hukumar kula da ƙwallon ƙafa ta Sifaniya (RFEF) da kuma majalisar ƙoli ta harkokin wasannin ƙasar bayan da ta sha kashi a wasanta da masu masaukinta Espanyol.

Real Madrid na ganin ɗanbayan Espanyol Carlos Romero, wanda ya ci ƙwallon ɗaya tilo, ya kamata a ce tun a baya an kore shi daga wasan saboda ƙetar da ta ce ya yi wa Kylian Mbappe.

A wasiƙar Real Madrid ta yi zargin cewa jami'an kula da wasanni ciki har da na'urar da ke taimaka wa alƙalin wasa - VAR, na nuna mata wariya da bambanci da son-kai.

Wasiƙar ta ce yadda ake yi wa Real Madrid alƙalancin wasa abin ya kai intaha - da hakan ke neman gurɓata wasan - abin da ta ce ba za ta ci gaba da kawar da ido ba a kai.

Da yake magana a lokacin wani taro da ƙungiyoyin gasar ta La Liga da hukumar ƙwallon Sifaniyar da kuma wakilan alƙalan wasan Sifaniyar, taron da Real Madrid ba ta halarta ba a ranar Alhamis ɗin nan - Shugaban na La Liga ya ce Real Madrid na son cutar da gasar ba alƙalan wasa ba kaɗai.

Ya ce ƙungiyar ta zuzuta lamarin fiya da kima, sun ɗimauce. '' Wasan ƙwallon ƙafa ba a kan Real Madrid kaɗai ake yi ba.'' In ji Tebas.