Hanyoyi uku da ke janyo asarar manyan sojoji a Najeriya

Lokacin karatu: Minti 3

Najeriya ta rasa ɗaruruwan manyan sojoji tun bayan komawar ƙasar kan turbar dimokraɗiyya a 1999 bisa wasu dalilai da ƙwararru ke ganin hakan ba zai taimaka wa ƙasar ba musamman a burinta na gina rundunonin sojin da ake ji da su a nahiyar Afirka.

Ƙwararru dai na ganin barin sojojin aikinsu ba tare da cikar wa'adinsu ba kuma ba tare da wani ƙwaƙwƙwaran dalili ba ka iya shafar rawar da ya kamata su taka wajen koya wa sojoji masu tasowa sanin makamar aiki.

BBC ta gano wasu hanyoyi guda uku da ke sa Najeriya asarar hazikan sojojinta manya, kamar haka:

Ritayar dole

Da alama a duk lokacin da aka samu sauyin gwamnati a Najeriya ko kuma shugaba mai ci ya sauya manyan hafsoshin tsaro saboda wani dalili, to gommai ko ɗaruruwan manyan sojoji dole ne su yi ritaya.

Hakan kuwa na faruwa sakamakon naɗa na ƙasa da su a muƙamai, wanda kuma bisa al'adar soji kamar a aikin gwamnati, bai kyautu babba ya ya yi aiki a ƙasan ƙaraminsa ko kuma sa'ansa ba.

Kuma al'amarin na faruwa ne a dukkan sassan sojin guda uku - sojin ƙasa da na ruwa da na sama.

"Misali, yanzu wannan sauyin da Shugaba Tinubu ya yi na manyan hafsoshin tsaro, labarin da muke samu shi ne aƙalla janar-janar kusan 100 ne za su yi ritayar dole saboda mutanen da aka naɗa ƙannensu ne a aiki," in ji wani tsohon Janar na soja da ba ya son a ambaci sunansa.

Tsohon Janar ɗin ya ce daga shekarar 1999 kawo yanzu Najeriya ta rasa janar-janar na soji da ba a san adadinsu ba.

"Tun 1999, kama daga Olusegun Obasanjo da Umaru Musa Yar'adu'a da Goodluck da Muhamamdu Buhari da Bola Tinubu duka sun tilasta wa manyan sojoji yin ritaya. Wasu an sanar da ritayarsu wasu kuma kwata-kwata ma ba a sani ba."

To dangane kuma al'adar yi wa sojoji ritaya a duk lokacin da ƙannensu suka samu muƙami, tsohon sojan ya ce "ba doka ba ce ta ce hakan. Kawai kamar yadda ka faɗa al'ada ce kawai wadda kuma ba za ta haifar mana da ɗa mai ido ba. Ai ba soja ba ne kawai. Haka ake yi a tsarin aikin gwamnati."

Juyin mulki

Wannan ma wata hanya ce ta asarar manyan sojoji a duk lokacin da aka zarge su da hannu a kitsa juyin mulki.

Tun shekarar 1966 da aka fara juyin mulki na farko a Najeriya, ƙasar ta yi rashin zaƙaƙuran manyan sojoji walau dai sakamakon kashe su da aka yi yayin juyin mulki ko kuma yanke musu hukuncin kisa sakamakon tuhumar su da hannu a kitsa juyin mulkin.

Rahotanni sun rawaito cewa gwamnatin shugaba Tinubu za ta sallami manyan sojoji bisa zargin samun su da hannu a kitsa juyin mulkin da kafofin watsa labaran Najeriya suka yi ta rawaito yin sa.

"Mu labarin da muke ji ma shi ne aƙalla za a sallami manyan sojojin da ake tunanin suna da hannu a juyin mulkin da aka ce wai an so a yi su 60. Ka ga wannan ba ƙaramar asara ba ce duk da cewa dai haka hukuncin yake saboda laifi ne na cin amanar ƙasa. Duk wanda ya shirya juyin mulki to ai ya san idan abin bai yiwu ba to za ta kwaɓe masa," in ji tsohon sojan.

Yaƙi/Rikici

Yaƙi ko a ciki ko wajen Najeriya na ɗaya daga cikin hanyoyin da ƙasar ke rasa sojojinta manya da ƙanana.

Duk da cewa babu wata ƙididdiga dangane da yawan manyan sojojin da Najeriyar ta rasa sakamakon yaƙi a gida ko a waje, yaƙi da Boko Haram ya lashe rayukan dakarun ƙasar manya da ƙanana.

"Yaƙi da Boko Haram lallai ya lashe manya da ƙananan sojoji musamman ma ƙananan. Amma tunda muna maganar manyan ne to ai ko a ƙasa da mako ɗaya sai da ƴan Boko Haram suka kashe wani babban soja tare da ƙanana shida a Konduga da ke jihar Borno."

"Sannan idan ba ka manta ba a shekarar 2018 sojoji sun zargi mutanen wani ƙauye wai Dura-Du da ke jihar Plateau da kisan Janar Idris Alƙali wanda aka ce sun jefa a rijiya. Suna tare mutane a kan hanya saboda rikicin ƙabilanci sai Allah ya kawo shi su kuma suka afka masa," in ji tsohon sojan Najeriya.