Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Waɗanne matakai ake bi wajen zaɓo manyan hafsoshin tsaron Najeriya?
- Marubuci, Daga Bashir Zubairu Ahmad
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 4
A ranar Juma'a ne Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya naɗa sababbin hafsoshin rundunar sojin ƙasar.
Tinubu ya ce ya amince da naɗin sababbin hafsoshin ne "domin ƙarfafa tsaron ƙasa da kuma kyautata aikin" rundunar sojin.
An sauke Babban Hafsan Tsaro Janar Chris Musa da sauran hafsoshi ne bayan shekara biyu da wata huɗu bayan Tinubu ya naɗa su a watan Yunin 2023.
Sababbin hafsoshin tsaron da Tinubu ya naɗa su ne:
- Janar Olufemi Oluyede - Hafsan hafsoshi (mafi girman muƙami)
- Manjo Janar W Sha'aibu - Hafsan sojojin ƙasa
- Air Vice Marshall S.K Aneke - Hafsan sojin sama
- Rear Admiral I. Abbas - Hafsan sojin ruwa
- Manjo Janar E.A.P Undiendeye - Shugaba sashen tattara bayanan sirri na soji
Ko waɗanne matakai ake bi wajen naɗa hafsoshin tsaro a Najeriya?
Kundin tsarin mulki
Kundin tsarin mulki na Najeriya ya tanadi cewa shugaban ƙasa ne yake da haƙƙin naɗa hafsoshi a rundunonin soji na ƙasa, da sama, da kuma ruwa.
Sashe na 218 (1) ya ce:
"Ikon da wannan sashe ya bai wa shugaban ƙasa ya haɗa da ikon naɗa babban hafsan tsaro, da hafsan sojin ƙasa, da hafsan sojin ruwa, da hafsan sojin sama, da kuma hafsan duk wata runduna kamar yadda dokar majalisar tarayya za ta bayar da dama."
Haka nan, sakin layi na (3) ya bai wa shugaban ƙasar damar shata wa kowane hafsan soji irin aikin da zai gudanar a rubuce a matsayinsa na babban kwamandan tsaro na ƙasa.
Sashe na 219 kuma ya sharɗanta cewa dole ne majalisar tarayya ta tabbatar cewa an bi ƙa'idar daidaito wajen nada dakarun tsaro daga yankunan siyasa na Najeriya, wanda ake kira Federal Character a Turance.
Dokar Rundunar Sojin Najeriya
Kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, dole ne sai majalisa ta yi dokar da za ta fayyace wasu batutuwa game da ayyukan rundunar sojin, da kuma shugabancinta.
Sashe na 18 na Dokar Rundunar Sojin Najeriya ya faɗi yadda za a naɗa su, har ma da laƙabin da za a dinga kiran su da shi.
"(1) Shugaban ƙasa zai iya naɗa hafsoshin rundunar soji bayan shawartar babban hafsan tsaro, da kuma samun amincewar majalisar tarayya, waɗanda za su jagoranci rundunar sojin ƙasa, da sojin ruwa, da sojin sama."
Sashe na 8(2) na dokar kuma ya jaddada cewa "dole ne hafsoshin rundunar sojin su yi ɗa'a ga duk wani umarni da shugaban ƙasa zai ba su kamar yadda sakin layi (1) na sashen ya tanada".
Sashe na 8 ɗin ya kuma ce shugaban ƙasa zai iya neman shawarar majalisar soji ko kuma Forces Council a Turance kafin ya nemi shawarar babban hafsan tsaro wajen naɗa sauran hafsoshin rundunar sojin.
Yanzu wajibi ne sai majalisar tarayya ta amince da naɗin sababbin hafsoshin tsaron, ba kamar a baya ba - inda shugaban ƙasa ke naɗa su kuma su fara aiki nan take.
A 2013 aka samu wannan sauyi sakamakon hukuncin wata babbar kotun tarayya da ya ce sharɗanta amincewar majalisar tarayya.
Yadda shugaban ƙasa ke zaɓar hafsoshin tsaro
Duk sojan da ya kai muƙamin manjo janar ya cancanci ya zama babban hafsan tsaro ko kuma hafsan wata runduna, kamar yadda Birgediya Janar (mai ritaya) Usman Kukasheka, tsohon mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya, ya shaida wa BBC.
Shugaban Najeriya a matsayinsa na babban kwamandan tsaro na ƙasa, shi ne ke da alhakin zaɓowa da naɗa hafsoshin tsaron bisa shawarar masanan da yake ganin ya amince da su.
"Daga lokacin da soja ya zauna rubuta jarabawar zama manjo janar, za a tambayi waɗanda za su yi masa jarabawar cewa ko kuna ganin wannan sojan zai iya jagoranci a matsayin babban hafsan soja?" kamar yadda Janar Kukasheka ya yi bayani.
"Ƙarin abin da ake dubawa shi ne kwamand nawa mutum ya riƙe kuma wane irin shugabanci ya yi a wurin."
A baya-bayan nan, akasarin hafsoshin sojin ƙasa da aka naɗa sun fito ne daga rundunar da ke yaƙi da Boko Haram a yankin arewa maso gabas.
"Dalili shi ne, yanzu abin da aka fi dubawa shi ne kwamandojin da suka je arewa maso gabas, ko arewa maso yamma, ko kuma arewa ta tsakiya. Dole ne mutum ya samu wannan ƙwarewar," in ji Janar Kukasheka.
Da gaske wasu manyan sojoji za su yi ritaya?
Janar Olufemi Olatubosun Oluyede, shi ne sabon hafsan hafsoshin Najeriya wanda kuma ya maye gurbin Manjo Janar Christopher Musa. Oluyede na ɗaya daga cikin sojojin da aka yaye daga aji na 39.
Shi kuma Manjo Janar Waidi Sha'aibu, shi ne sabon hafsan sojojin ƙasa, wanda ya maye gurbin Manjo Janar Gold Chibuisi, kuma yana cikin 'yan aji na 41.
Bisa al'adar aikiin soja, kasancewar Waidi Sha'aibu ɗan aji na 41, duk sojojin da ke aji na 40 za su yi ritaya saboda ba za su so su yi aiki a ƙarƙashinsa ba kasancewar siniyansu ne a aikin.
Haka nan, wasu daga cikin 'yan ajin da suka fita tare na 41 za su yi ritaya, sai dai waɗanda ya nemi su yi aiki tare da shi. Amma wannan al'ada ce kawai ta aikin soja, ba doka ba.
Zuwa yanzu babu tabbas game da yawan jami'an da za su yi ritayar sakamakon naɗin sojan da ke ƙasa da su.
Sai dai masana na cewa duk da haka akwai mafita ga sojojin da ke aji na 40, saboda shi Oluyede ɗan aji na 39 ne.
"Tun da shi ɗan aji na 39 ne, zai iya ɗaukar wasu 'yan aji na 40 domin ya yi aiki da su a hedikwatar tsaro, amma ba su da yawa," a cewar Janar Kuka Sheka.
Haka batun yake a rundunar sojin sama da ta ƙasa.