Hanyoyi huɗu da za ku gane kun yi aikin Hajji karɓaɓɓe

Lokacin karatu: Minti 5

A ranar Lahadi nan ne alhazai miliyan 1.8 suka kammala aikin Hajjin bana a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya, bayan kammala jifan shaiɗan a Jamarat da ke Mina.

Ko da yake a shari'ance a ranar Litinin ne ranakkun aikin Hajjin shida ke cika, saboda yadda addini ya bai wa mahajjatan damar kammalawa cikin kwanaki biyar ko shida inda kuma mafi yawan alhazan ke zaɓar kammalawa cikin kwana biyar ɗin.

Masu son ƙarawa su ma za su kammala ne ranar Litinin da jifan shaiɗan da ake kira Jamrat a rana ta huɗu maimakon uku da dama ke yi.

Gabanin jifan Jamarat ɗin, mahajjatan sun yi hawan Arafa da kwanan Muzdalifah da Ɗawaful Ifadah da kuma Sa’ayi.

A ranar Talata ne kuma ake sa ran fara jigilar alhazan zuwa kasashensu.

Bisa tanadin addinin Musulunci dai duk mutumin da ya yi aikin hajji bisa wasu sharuɗɗan da aka gindaya to zai koma garinsu ba tare da zunubi ba, tamkar ranar da aka haife shi, sai dai kuma idan ya ɗauko wasu zunuban daga baya.

To sai dai abin tambaya a nan shi ne ta yaya alhaji zai gane ya yi aikin Hajji karɓaɓɓe?

A kwanakin bayan, BBC ta tambayi Sheikh Husaini Zakariyya na cibiyar addinin Musulunci ta Uthman Bn Affan da ke Abuja, inda ya kawo wasu hanyoyin gane karɓaɓɓen aikin hajji guda huɗu.

1) Amfani da kuɗin halal

Sheikh Hussaini Zakariyya ya ce babban mizanin da alhaji zai fahimci cewa aikin Hajjinsa karɓaɓɓe ne shi ne ya tabbatar kuɗin da ya biya domin tafiya aikin hajjin na halal ne ba haram ba.

"Duk wanda ya tafi aikin hajji da kuɗin riba ko kuɗin garkuwa da mutane ko na ƙwace ko kuma a matsayinka na shugaba ka yi ruf da ciki a kan kuɗaɗen al'umma, to lallai aikin hajjinka ɓatacce ne saboda an yi amfani da kuɗin haram.

Harwayau, halal ta shiga cikin kuɗin guzurin da mahajjaci ya tafi da su domin bai kamata ka je ibada kana ci ka sha da kuɗin haram ba." In ji shiekh Zakariyya.

2) Kyautata niyya

Malamin na addinin Musulunci ya ce ba ya ga yin amfani da kuɗin halal to wani abu kuma da ake dubawa domin gane karɓuwa ko rashin karɓuwar aikin hajji shi ne "kyautata niyya".

"Kyautata niyya a aikin hajji babban al'amari ne. Misali dole ka ƙudirce cewa za ka je aikin hajjin nan ne domin Allah - domin Allah ya umarci masu hali su je su bauta masa.

Ka ga kenan duk wanda ya tafi aikin hajji ko da da kuɗin halal ya je amma niyyar ba ta da kyau to Allah ba zai karɓi aikin hajjinsa ba. Duk wanda ya je hajji da niyyar ƙwace ko zamba ko kai ƙwaya ko kuma ka je domin ka yi shirka da dai sauransu ka ga ai niyya ba ta da kyau." In ji malamin.

3) Aiwatar da ayyukan Hajji bisa ilimi

Sheikh Hussain Zakariyya ya ce akwai yanayin da za ka ga alhazai sun biya Hajjin da kuɗin halal sannan suna da niyya mai kyau amma kuma rashin ilimin yadda za su aiwatar da ibadu da ake gudanarwa a aikin hajjin sai ka ga hajji ta lalace.

"Ya kamata duk wani alhaji ya san rukunai da wajibai da sunnoni da ma mustahabbi na aikin Hajji sannan ya san idan ya yi kaza to zai yi kaza domin gyaran ayyukan nasa. To shi ma rashin sanin irin waɗannan sharuɗɗa kan iya ɓata hajji.

Wannan ya haɗa da irin abin da Al-ur'ani mai tsarki ya faɗa kan abin da ake tsammani ga mai aikin Hajji.

"Wato idan an tafi babu yasasshiyar magana a aikin Hajji. Babu aikata fasiƙanci. Babu faɗa ko zage-zage ko jayayya. Aiki ne da ke buƙatar haƙuri mai zurfi da kawaici wato ko da an yi maka kai ka da ka yi.

Misali kamar mutumin da zai sunbaci dutsen Hajarul Aswad amma duk sai ya doddoke mutane kafin ya samu ya kai ga sumbantar dutsen. Ka ga kenan ya aikata haramun kafin ya cimma mustahabbi. Allah ba zai karɓi wannan aikin nasa ba." Kamar yadda sheikh Zakariyya ya ƙara haske.

To sai dai malam Zakariyya ya ce "idan mutum ya saɓa wa ƴan uwansa alhazai zai iya sauri ya nemi gafararsu tunda su ya saɓawa. Sai Allah ya karɓi ibadunsa."

4) Kamewa ga aikata laifuka

Shehun malamin ya ce wata alama da mutum da kansa zai iya yi wa kansa hisabi dangane da karɓa ko ƙin karɓar aikin hajjin nasa ita ce kamewa daga irin laifukan da mutum yake yi kafin tafiyarsa aikin hajjin.

"Idan mutum ya dawo daga Hajji amma sai ya ga yana ci gaba da aikata irin laifuka na saɓa wa ubangiji ko jama'a kamar cuta ko sata ko zamba ko garkuwa da dai sauransu to lallai ba a karɓi aikin hajjin nasa ba.

Abin da ake so shi ne a ga mutum ya koma garinsu ya zama wani na daban wajen ibada da mu'amila. Sai dai kuma kasancewar alhaji ɗan adam ba mala'ika zai iya kuskure ko saɓon Allah amma za ka mutum ya yi sauri ya tuba ta hanyar yawan istigfari da ambaton Allah." In ji Shehun malamin.

Ko samun biyan buƙata na nufin karɓuwar aikin hajji?

Wani abu da jama'a gamagari ke yi wa kallon mizanin karɓar aikin hajji shi ne idan mutum ya koma garinsu kuma ya ga dukkannin addu'o'insa da ya yi a lokacin aikin hajji sun karɓu.

To sai dai sheikh Zakariyya ya ce sam babu ma alaƙa tsakanin karɓuwar addu'ar da aikin hajji kaɓaɓɓe.

"Ita karɓar addu'a ai wani abu ne daban. Akwai waɗanda Allah yake yi wa talala. Misali kamar mu ne da muke kiwata dabbobi - muna ba su abinci su ci su koshi amma kuma muna yin hakan ne da nufin su girma mu yanka su.

Allah zai iya biyawa mutumin da ba lallai bawon Allah na gari ba ne buƙatu domin ya yi masa ɗaurin talala daga ƙarshe. To sai dai abun da kowanne alhaji ke fata kenan samun karɓuwar addu'a. Idan Allah ya biya masa buƙatu to haka ake so. Idan buƙatun ba su biya ba to hakan ba wai ya nuni da cewa alhaji bai yi aiki karɓaɓɓe ba ne.