Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Manya-manyan asarar rayuka da aka taɓa yi a wajen kallon kwallon kafa a duniya
Yamutsin masu kallon kwallon kafa na Indonesia, wanda ya kashe akalla mutum 125 a Gabashin Java ya riga ya shiga tarihin bala'o'i manya da suka faru a tarihin wasan.
Bala'in wanda ya auku a ranar Asabar, 1 ga Oktoban bana a Filin Wasan Kanjuruhan, yana kamanceceniya da irinsa da suka auku a baya, ba a rashin rayuka kadai ba.
Babban dalilin aukuwar yamutsin da ke faruwa a filin wasan ƙwallon ƙafa shi ne rashin tsari mai kyau wajen tsara masu kallon.
Filin Wasan Estadio Nacional, Peru (1964)
Akalla mutum 300 suka rasu a lokacin da ake buga wasa tsakanin Peru da Ajantina, inda aka samu yamutsi bayan an hana wani kwallo da Peru ta jefa a ragar Ajantina.
Hakan ya sa magoya bayan Peru suka kutsa filin wasan da ake bugawa domin neman gurbin shiga Gasar Olympik na 1964 da aka buga a birnin Tokyo, wanda ya sa 'yan sanda suka rika harba barkonon tsohuwa kan mai uwa da wabi a Filin Wasa na Lima Estadio Nacional.
Wannan ya jawo yamutsi a kofofin fita daga filin wasan, wadanda a kulle suke a lokacin.
A hukumance, wadanda suka mutu sun kai 328, amma akwai alama an tauye adadin domin ba a hada da wadanda aka harbe ba domin magoya bayan da jami'an tsaro sun gwabza a wajen filin wasan.
"Akwai ganau da dama da suka tabbatar da mutuwar wasu a sanadiyar harbi, amma alkalin da aka nada domin bincikar lamarin.
Mai shari'a Benjamin Castaneda bai samu gamsassun hujjoji da zai tabbatar da hakan ba," in ji wakilin wasanni na BBC, Piers Edwards a wata maƙala da ya rubuta a shekarar 2014 domin bikin cika shekara 50 da aukuwar bala'in, wanda har yanzu ake kirga shi a cikin irinsa da suka fi tsanani.
Daga bisani an yanke wa kwamandan 'yan sanda mai suna Jorge Azambuja, wanda shi ne ya bayar umarnin harba barkonon tsohuwa daurin wata 30 a gidan yari.
Filin Wasan Accra, Ghana (2001)
A wani wasan kece-raini tsakanin Heart Oak da Asante Kotoko, wadanda kungiyoyi ne guda biyu masu dimbin magoya baya da aka buga a Mayun 2001, an samu barkewar rikici bayan magoya bayan Kotoko sun nuna rashin jin dadinsu da farke kwallon da abokan karawansu suka yi a kusa da tashi.
Wannan ya sa 'yan sanda suka shiga harba barkonon tsohuwa, wanda ya sa masu kallo suka fara rububin fita, inda suka tarar kofofin na kulle.
Akalla mutum 126 suka mutu, wanda wannan ne yamutsi a wajen kallon kwallon kafa mafi muni a Afirka.
"Na ga gawarwakin matasa masu jini a jika a kwance a kasa. Na shiga tashin hankali, da har na kasa kirga yawan gawarwakin," in ji Karamin Ministan Wasannin Ghana na wancan lokacin Joe Aggrey a zantawarsa da BBC.
Kwamitin Bincike ya daura laifin ga 'yan sanda, wannan ya sa aka tuhumi 'yan sanda shida da kisan kai. Sai dai a shekarar 2003, an wanke su a wata shari'a da mutanen Ghana da dama suka yi na'am da shi kamar yadda Paul Adom Otchere, wanda dan jarida ne a tashar rediyo ta Joy FM wanda ya kasance a kotun lokacin shara'ar ya bayyana.
"Abin da mutanen gari suka so shi ne hukunta wadanda suka gina filin wasan, wanda ya tabbatar da ingancin ginin da wadanda suka kulle kofofin shiga filin a lokacin yamutsin," kamar yadda ya bayyana wa BBC bayan hukuncin.
Hillsborough, Birtaniya (1989)
Yana cikin bala'o'i manya masu daure kai da suka faru a duniyar kwallon kafa. Ya faru ne a sanadiyar rashin tsari mai kyau wajen tsara masu kallon wasan kusa da karshe na Kofin Kalubale tsakanin Liverpool da Nottingham Forest, inda magoya bayan kungiyar Liverpool guda 96 suka mutu.
Daga baya wani mai suna Andrew Devine da ya ji mummunar rauni a yamutsin ya rasu a shekarar 2021 yana da shekara 55, wanda hakan ya sa ya zama mutum na 97 da ya rasu.
'Yan sanda da wasu sashin 'yan jarida na Birtaniya suna daura laifin ne a kan magoya bayan, inda suka zarge su da zuwa filin cikin maye da rashin bin tsari.
Sai dai an yi watsi da wannan bayan an gudanar da bincike-bincike a tsakanin shekaru 30 daga baya.
A shekarar 2016, wani alkali ya tabbatar da cewa an kashe wadanda lamarin ya rutsa da su ne, sannan ya wanke 'yan kallon daga aikata wani laifin.
Filin Wasan Dasharath, Nepal (1988)
Wata tsawa mai karfi ce ta firgita masu kallon wani wasa a Birnin Nepalese a Maris na 1988.
Wannan ya sa masu kallon suka fara rige-rigen shiga gefen da ke da rufi a filin domin samun mafaka, amma 'yan sanda suka hana su, sannan wadanda suka nufi kofofin fita, suka tarar duk suna kulle.
Wannan yamutsin ne ya jawo mutuwar mutane da dama. A hukumance an ce mutum 70 suka mutu, amma kafofin yada labarai na Nepalese sun ruwaito cewa wadanda suka mutu za su kai 93.
"Na ga takalman wadanda suka mutu ko ta ko'ina a filin," in ji Anil Rupakheti, wanda tsohon dan kwallo ne da ya kasance a cikin filin lokacin da lamarin ya faru a zantawarsa da Jaridar Kathmandu Post a shekarar 2020.
Filin Wasan Port Said, Masar (2012)
A wani wasa da aka fafata tsakanin Al Masry da All Ahly na Masar, a birnin Port Said a Fabrailun 2012, an karkare wasan ne jina-jina, bayan magoya bayan Kungiyar Al Masry sun kutsa yankin magoya bayan Kungiyar Al Ahly, suka kai musu hari, inda suka samu nasarar cin musu-saboda 'yan sanda sun ki bude kofofin ficewa.
Wannan hargitsin ya haifar da mutuwar mutum 74, sannan sama da 500 suka jikkata.
An kama tare da gabatar da sama da mutum 70 ciki har da 'yan sanda tara a gaban shara'a, inda aka yanke wa 47 hukunci, ciki har da hukuncin kisa.
Wasu daga cikin magoya bayan Al Ahly da ake kira 'Utras" suna cikin wadanda suka shiga gaba lokacin zanga-zangar kiyayya ga Shugaban Kasa Hosni Mubarak, wadda ta yi sanadiyar kifar da gwamnatinsa.
Hakan ya sa wasu magoya bayan wasanni suke zargin magoya bayan Hosni Mubarak da shirya yamutsin na Port Said domin ramako, sannan suka zargi 'yan sanda da rashin tabuka abin kirki.
'Har yanzu ina tuna bala'in da na gani a wannan Daren," in ji Fabio Junior, dan wasan Brazil da a lokacin yake buga wa Kungiyar Al-Ahly leda a lokacin a zantawarsa da ESPN Brazil a 2019.
Filin Wasan Luzhniki, Russia (1982)
Filin Wasan Moscow wanda ba da dadewa ba aka buga Wasan Karshe na Gasar Cin Kofin Duniya na shekarar 2018, shi ma an taba shiga irin wannan bala'in a cikinsa.
Kimanin shekara 40 da suka gabata, a zamanin mulkin Soviet, an yi turereniya bayan wasan Kofin Turai tsakanin Spartak Moscow ta Rasha da HFC Haarlem ta Holland, inda mutane da dama suka mutu.
Sai a shekarar 1989 ce aka samu labarin adadin mutanen da suka mutu a hukumance, bayan an dade ana bayyana aukuwar lamarin ne kawai.
Shaidun ganau sun ce a ranar magoya baya da yawa sun taru ne a sashe daya na filin saboda ba a halarci kallon wasan ba sosai.
"Sai ya kasance kofa daya aka bude domin saukakawa 'yan sanda su yi aikinsu," kamar yadda Alexander Provestov, wanda fitaccen dan jarida ne na kasar Rasha da ya kasance a filin wasan a lokacin a zantawarsa da Al Jazeera.
"Ba karamin kuskure aka tafka ba."