Afcon 2023: Za mu sa ƙwazo don kaiwa zagaye na biyu - Ekong

.

Asalin hoton, Getty Images

Ƙyaftin din Najeriya, William Troost-Ekong ya ce wannan ce tawagar Super Eagles mafi ƙyau da ƙwararrun da yake wasa a ciki.

Najeriya ta doke Ivory Coast 1-0 ranar Alhamis ta koma ta biyu a rukunin farko, wadda ke sa ran cin Guinea Bissau, domin kai wa zagaye na biyu ranar Litinin.

A ranar ce Ivory Coast mai maki uku a mataki na uku za ta fafata da Equitorial Guinea, wadda take ta daya a rukunin da maki huɗu iri daya da na Super Eagles.

Ita dai Guine Bissau ta yi rashin nasara a hannun Ivory Coast a wasan farko, sannan Equatorial Guine ta doke ta, kenan ba ta da maki a rukunin.

Najeriya ta hada maki hudu ne, bayan tashi 1-1 da Equatorial Guinea da cin Ivory Coast a wasa na biyu a rukunin farko.

''Koda yake ya yi wuri mu cika baki, amma fatan mu da burin mu shi ne taka rawar gani da za a yi alfahari da mu.'' in ji Troost-Ekong.

Mai tsaron bayan, mai shekara 30, wanda ya fara buga wa Najeriya tamaula a 2015 ya kara da cewar ''Idan ka kalli fitattun ƴan wasan da muke da su, wannan ce Super Eagles mafi kyau da nake taka leda da ita.

Mai taka leda a PAOK, wanda aka haifa a Netherlands, sannan ya yi makaranta a Ingila na buga wa Super Eagles wasanni tun daga ranar da ya fara taka mata leda.

Wannan ce gasar kofin Afirka ta uku da yake halarta, yana cikin ƴan wasan da Argentina ta yi nasara a kan Najeriya a gasar kofin duniya a Rasha a 2018.