Audugar jinin al'ada ta fi ƙarfin mata a Najeriya saboda hauhawar farashi

Asalin hoton, Mcrissar Foundation
- Marubuci, Fatima Othman
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
Hauhawar farashi da 'yan Najeriya ke fama da shi a kwanan nan ya sa yanzu mata da dama ba su iya sayen audugar jinin al'ada.
Hakan na da matsaloli kamar ware mata da kuma ta'azzara harkokin lafiyarsu.
"Dole ta sa nake amfani da ƙyalle idan ina al'ada saboda ba zan iya sayen audugar mata ba," a cewar wata mazauniyar Abuja mai suna Khairat Badamasi game da ƙyallayen zani da take amfani da su.
Grace Solomon, wata mai sana'ar cirar kuɗi da na'urar POS a Abuja, ta ce tana amfani da tsimma idan ba za ta iya sayen audugar ba.
"Sannan nakan zauna a gida mafi yawan lokaci idan na saka ƙyalle, saboda ina fargabar jini zai ɓata ni kuma na ji kunya," in ji ta.
Ƙarancin samun kayan kula da tsafta yayin jinin al'ada matsala ce da ta karaɗe duniya baki ɗaya.
A shekarar 2021, tsohuwar Ministar Harkokin Mata a Najeriya Dame Pauline Tallen ta faɗa wa wani taron manema labarai cewa sama da mata miliyan 37 a ƙasar ba sa iya samun audugar saboda tsadarta.
Wani rahoton Bankin Duniya na watan Mayun 2021 ya ce ƙarancin kayan tsaftar jinin al'ada kan ta'azzara matsalolin rayuwa, ciki har da ilimi da kuma ƙaruwar barazanar da mata ke fuskanta a ɓangaren kiwon lafiya.
Dr. Anisa Ambursa, likitar mata ce a Abuja, kuma ta ce wasu abubuwa da mata kan yi lokacin jinin kan jawo matsaloli a lafiyarsu.
"Bin hanyoyin da suka dace na kula da lafiya lokacin jkinin al'ada na matuƙar amfani ga lafiyar mata da yara. Yana da kyau a yi amfani da tsaftataccen ruwa da kuma sauya audugar akai-akai," a cewarta.
"Duk macen da ba ta lura da kyau lokacin al'ada za ta kamu da cutuka daban-daban cikin har da lalurar fitsari, da cutukan da suka shafi ciki da mafitsara, waɗanda za su iya hana haihuwa idan ba a kula da su ba."

Asalin hoton, Getty Images
Kayan tsafta a kyauta
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
An sha yin yunƙurin kawo ƙarshen matsalar ƙarancin kayan tsafta a Najeriya, inda ƙungiyoyi da ɗai-ɗai-kun mutane suke gwagwarmayar sauya yadda lamarin yake a yanzu.
Rabi Adamu ɗaya ce daga cikin masu gwagwarmaya wadda ta kafa Gidauniyar Mcrissar mai tallafa wa mata da ƙananan yara.
"Muna kallon tsaftar jinin al'ada a matsayin babban al'amari game da lafiyar mata da kuma mutuncinsu. A wurare da yawa, ƙarancin wayar da kai da kuma rashin kayan tsafta na shafar ilimin mata da kuma zirga-zirgarsu a tsakanin al'umma," in ji ta.
Saboda wannan dalili ne ta ƙaddamar da wani yawon wayar da kan yara mata.
Yayin wani yawon faɗakarwa a wata makaranta da ke ƙaramar hukumar Jema'a ta jihar Kaduna, ta nemi ɗaliban su rubuta matsalolin da suke fuskanta yayin jinin al'ada.
Ɗaliban sun rubuta cewa ƙarancin kayan tsafta na sakawa su daina zuwa makaranta lokacin jinin al'adarsu.
Rabi ta ce gidauniyarta ta kafa wani rumbun ajiyar kayan tsaftar mata inda mutane da ƙungiyoyi kan ba da sadakar kayayyaki ga mata ɗalibai. Ta ce hakan zai taimaka wa yaran da a da suka daina zuwa makaranta saboda jini.
"Dole ne sai gwamnati da 'yan kasuwa sun yi da gaske wajen samar da kayan tsaftar mata," a cewarta.
"Muna ta fafutikar nema wa ɗaliban sakandare kayan tsafta kyauta. Ya kamata a ce kowace ɗaliba tana zuwa makaranta a lokacin al'ada."
Ita ma Karo Omu mai fafutikar nema wa mata kayan tsafta ce, inda take so a mayar da su kyauta ko kuma a sauƙaƙa farashinsu.
Ta kafa Gidauniyar Sanitaryaidng da ke samar da kayan tsaftar jini da kuma ilimi ga matan da ke cikin buƙata.
"Shekaru da yawa da suka gabata, ƙasar Scotland ta ƙaddamar da samar da kayan kula da jinin al'ada kyauta, ciki har da waɗanda ake iya wankewa a ci gaba da amfani da su. Idan ƙarin ƙasashe za su yi irin wannan ko kuma aƙalla su tallafa wa ƙungiyoyi a yankunan za mu iya kawo ƙarshen matsalar," in ji ta.

Asalin hoton, Getty Images
Maryam Muhammad ce ta kafa Gidauniyar PadbyRxm. Tana sane da ƙarancin audugar da kuma tasirin hakan a lokacin annobar korona ga ƙananan matan jihar Kano da ke arewacin ƙasar.
Hakan ta sa ta kafa gidauniyar kuma take amfani da ƙyallayen da ake sarrafawa daga itacen kwangwala wajen samar da kayan tsaftar matan.
"Ganin yawan talauci a Najeriya, samun damar sayen audugar da ake jefarwa idan aka gama amfani da ita yana da wuya. Abubuwan da za a iya cigaba da amfani da su za su maye gurbin masu tsadar," in ji ta.
A Abuja, Khairat Badamasi ta ce za ta yi maraba da duk wani tsari da zai ba ta damar samun auduga kyauta.
"Nakan yi amfani da tsimma a lokacin al'adata saboda ba ni da kuɗi," kamar yadda ta bayyana.
"Rayuwata za ta sauya sosai idan na samu auduga kyauta ko kuma a farashi mai sauƙi daga gwamnati."











