Fitattun ƴan takarar gwamnan Kano

Hotunan ƴan takarar gwamna a Kano

Ana ganin zaɓen gwamnan da za a yi ranar Asabar 11 ga watan Maris zai kasance ɗaya daga cikin mafiya zafi da za a fata sosai a tarihin jihar.

Alƙaluman hukumar zaɓen ƙasar sun nuna jihar tana da masu rijistar zaɓe 5,921,370.

Sai dai kamar yadda zaɓen shugaban ƙasar da aka yi ranar 25 ga watan Fabarairu ya nuna, INEC ta ce ƙasa da kashi cikin ɗari ne na masu rijista a jihar suka yi zaɓe, to amma ana sa ran a wannan zaɓen yawan waɗanda za su fito zaɓen ya fi haka.

Ana dai ɗaukar zaɓen na gwamna a matsayin fafatwa tsakanin tsohon gwamnan jihar, kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP, Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ke bayan ɗan takarar jam'iyyarsa kuma tsohon kwamishin ayyuka na gwamnatinsa Abba Kabir Yusuf, da kuma gwamnan jihar mai ci, Abdullahi Umar Ganduje, wanda ke bayan ɗan takarar gwamnan na APC kuma mataimakin gwamna a yanzu Nasiru Yusuf Gawuna.

Akwai ƴan takarar wannan kujera ta gwamnan jihar Kano har 17 a zaɓen mai zuwa, wanda za a yi lokaci ɗaya da na ƴan majalisar dokoki.

Sha'aban Ibrahim Sharada

Hoton Sha'aban Sharaɗa

Asalin hoton, FACEBOOK/IBRAHIM SHARADA

Bayanan hoto, Sha'aban Sharaɗa ya fice daga APC ne ya koma ADP

Sha'aban Sharaɗa shi ne ɗan takarar jam'iyyar Action Democratic Party (ADP), wanda kuma a yanzu shi ne ɗan majalisar wakilai na tarayya da ke wakilatr mazaɓar cikin birnin Kano.

Kafin shigarsa harkokin siyasa yana aiki ne da gidan rediyon Freedom, FM, da ke Kano.

Bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya ci mulki ne sai ya naɗa shi a matsayin mai taimaka masa na musamman a 2015.

Nasiru Yusuf Gawuna

Hoton Nasiru Yusuf Gawuna

Asalin hoton, FACEBOOK/NASIRU GAWUNA

Bayanan hoto, Nasiru Gawuna shi ne mataimakin Ganduje a yanzu

Nasiru Yusuf Gawuna wanda shi ne mataimakin gwamnan jihar a yanzu, shi ne ɗan takarar jam'iyya mai mulki APC.

Ya kasance mataimakin gwamnan jihar tun 2018 lokacin da wanda ke kan kujerar a da Farfesa Hafiz Abubakar ya sauka saboda saɓanin da ke tsakaninsa da Ganduje.

Nasiru Gawuna ya yi shugaban ƙaramar hukumar Nassrawa karo biyu kafin Kwankwaso da yake gwamna a lokacin ya naɗa shi kwamishinan gona a 2014.

Abba Kabir Yusuf

Hoton Abba Kabir Yusuf

Asalin hoton, FACEBOOK/ABBA GIDA GIDA

Bayanan hoto, Abba Kabir Yusuf, shi ne ya yi wa PDP takarar gwamnan a 2019

Abba Kabir Yusuf, wanda ake wa laƙabi da Abba Gida-gida shi ne ɗan takarar New Nigeria People's Party (NNPP).

An haife shi a ranar 3 ga watan Janairu na 1963, inda ya yi Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta tarayya da ke Mubi, wato Federal Polytechnic, Mubi, a 1985, daga baya kuma ya yi digiri na biyu a Jami'ar Bayero da ke Kano.

Ya kasance kwamishinan ayyuka a gwamnatin Kwankwaso daga 2011 zuwa 2015.

Salihu Tanko Yakasai

Hoton Salihu Tanko Yakasai

Asalin hoton, FACEBOOK/SALIHU YAKASAI

Bayanan hoto, Salihu da ne ga tsohon ɗan siyasar Najeriya, Tanko Yakasai

Salihu Tanko Yakasai wanda shi ne ɗan takarar People's Redemption Party (PRP), tsohon mai bayar da shawara ne ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Gwamnan ya kore shi daga aiki ne bayan da ya rubuta wasu abubuwa na sukar gwamnati a shafin Twitter a 2021.

Salihu wanda ake wa laƙabi da Ɗawisu ya yi aiki da tashar talabijin ta CNN a matsayin mai aikawa da rahoto mai zaman kansa.

Sheikh Ibrahim Khalil

Hoton Sheikh Ibrahim Khalil

Asalin hoton, OTHERS

Bayanan hoto, Sheikh Ibrahim Khalil na ADC shi ne shugaban majalisar malamai ta Kano

Fitaccen malamin addinin Musuluncin wanda kuma shi ne shugaban majalisar malamai ta jihar Kano, da ya jima yana nuna sha'awarsa ta tsayawa takara, a yanzu shi ne ɗan takarar kujerar gwamnan a jam'iyyar African Democratic Congress (ADC).

A da ya kasance ɗan jam'iyyar APC mai mulki a jihar, amma kuma ya fice daga cikinta a daidai lokacin da take fama da rikici tsakanin ɓangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Ibrahim Shekarau.

A fagen addini, ɗan takarar ya yi fice wajen bayar da fatawa mai sauƙi a kan al'amura, abin da kuma a wani lokaci kan janyo zazzafar muhawara

Sadiq Aminu Wali

Sadiq Wali
Bayanan hoto, Sadiq Wali

Sadiq Wali ya kasance ɗan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a jihar Kano, bayan sa-toka-sa-katsi na siyasa da kuma shari'a tsakaninsa da abokin hamayyarsa a wannan takara, Mohammed Abacha.

Sadiq ɗa ne ga tsohon ministan harkokin waje na Najeriya Aminu Bashir Wali, wanda ya yi takarar wannan kujera ta tsohuwar jihar Kano a shekarar 1979 ƙarƙashin jam'iyyar National Party of Nigeria (NPN), kuma lokacin Muhammadu Abubakar Rimi na People's Redemption Pary (PRP) ya kayar da shi.

Sauran ƴan takara

-Bala Muhammad Gwagwarwa - Social Democratic Party (SDP)

-Muhammad Abdullahi Raji - Labour Party (LP)

-JanarIbrahim Sani (murabus) - Allied Peoples Movement (APM)

- Hajiya Furaira Ahmad- Boot Party (BT)

- Hajiya Aisha Mahmud - National Rescue Movement (NRM)