Zabibi da bula da algarura: Ƴan Najeriya sun cashewa sabbin kudin naira

Asalin hoton, Presidency
Tun bayan da Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ƙaddamar da sabbin takardun naira da aka sauyawa fasali, ƴan ƙasar suka yi wa batun ca ta hanyar bayyana ra'ayoyinsu kan hakan.
Shafukan sada zumunta na Facebook da Tuwita da Instagram da Tiktok da ma Whatsapp sun zama wuraren da ba a zancen komai sai na sabbin kudin.
Da yawan mutane sun nuna rashin jin dadinsu kan tsarin sabbin kuɗin, suna cewa ba su zaci haka sauyin zai zo ba.
An ƙaddamar da kuɗaɗen ne a wajen taron mako-mako da ake yi a fadar shugaban ƙasar a Abuja a ranar Laraba.
Shugaba Buhari ya ce sababbin takardun kuɗin za su taimaka wa Najeriya ta wajen warware matsaloli da dama da suke addabar ƙasar.
A shafukan Facebook da Tuwita, sai da ya zama shi ne babban batun da aka fi tattaunawa a kansa tun daga ranar Laraba har zuwa wayewar garin Alhamis.
Tiktok ma ba a bar shi a baya ba, don yawanci matasa ƴan Najeriya da ke amfani da shafin sun mayar da hankali ne yin raha da barkwanci kan lamarin.
Yayin da Whatsapp da Instagram suka zama wajen da kusan kowa ya dinga wallafa sabbin kudin a sitatus (status) da sitori (story) ɗinsu.
Me aka dinga cewa?
A shafin Tuwita a ranar Laraba an yi amfani da maudu'in #Naira sau fiye da 200,000, yayin da a ranar Alhamis ma aka ci gaba da amfani da shi har sau fiye da 136,000.
Facebook kuwa a ranar Larabar sama da mutum 300,000 ne suka yi ta tattauna zance har zuwa Alhamis.
Ko a shafinmu na BBC Hausa Facebook, wanda yana ɗaya daga cikin shafukan da suka fara saka hotunan sabbin kudin, inda alƙaluma suka nuna cewa mutum miliyan 1,300,040 suka gani, yayin d ayawan waɗanda suka so suka yaɗa suka kuma yi tsokaci ya kai mutum 309,000, kamar yadda za a iya gani a ƙasa.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Facebook suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Facebook da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a Facebook, 1
Yawanci masu tsokacin sun ce sabbin kudin sam ba su da kyau da jan hankali, saboda irin launin da aka sauya musu.
Naira 200 dai an mayar da ita mai jan launi, naira 500 ta koma koriya, ita kuwa naira 1,000 sai ta koma toka-toka.
Hakan ya sa wasu cikin raha suka dinga cewa kawai dai an barbaɗawa 200 jawa ne, 500 kuma an barbaɗa mata algarura sai aka dulmiya naira 1,000 kuma a cikin bula.

A wani saƙon na daban kuma da BBC Hausa ta sake wallafawa don neman masu sauraro su gaya mana bambancin da ke tsakanin sabbi da tsofaffin kuɗaɗen, shi ma mutane sun yi ta bayyana ra'ayoyinsu.

End of Karin wasu labaran da za ku so ku karanta
Sabon salon hoto
Kafin a ce mene ne wannan tuni ƴan Najeriyar suka mayar da abin wani salon raha da ya zama yayi, inda suka dinga ɗaukar hotunan kansu suna gyaggyara shi da launuka suna cewa su ma ga sabon sauyin fuskokinsu tamkar na nairar.
Sai a ga mutum ya yi hotonsa cikin launi uku na ja da kore da ruwan bula, abin ma bai tsay a kansu ba kawai har hoton shugaban babban bankin Najeriyar Godwin Emefiele aka dinga sauyawa launin.
Sai aka mayar da abin yayi, kowa ya dinga sauya salon hotonsa yana wallafawa.
Ga dai abin da sauran masu tsokaci ke cewa:
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
NKEM #PeterObi2023@Nkemchor ya ce: "Waye ya yi wa Emefiele haka? Ko martanin ake mayar masa kan sauya fasalin nairarmu?
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Facebook suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Facebook da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a Facebook, 2
Akwai kuma wasu da su yabon sabon kudin suke yi kamar haka:Arabinrin
Aderonke@AderonkeWya ce: "Ya ku sabbin takardun kuɗi, ba na daga cikin masu sukarku. Ku sani cewa ina maraba da ku a cikin asusun bankinsa da gidana da kuma tabbatar da cewa za ku samu tsaro. Ku zo min da yawa a miliyoyi a launukanku.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3

Karshen labarin da aka sa a X, 4
Amfani hudu na sauya fasalin nairar
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A wajen kaddamar da sabbin kudin din Shugaba Buhari ya ce sauya fasalin kudin zai taimaka wa tsare-tsaren manufofin kudi na CBN, sanan kasancewar wannan ne karo na farko da aka buga naira a Ma’aikatar Buga Kudi ta Najeriya zai hana yaɗuwar jabun kuɗin.
1. Zai taimaka wajen rage tashin farashin kaya domin zai sa a fito da tsoffin kudin da aka bobboye.
2. Zai kuma taimaka waje tsara manufofin da suka jibanci kudi domin za mu samu sahihan alkaluma kan yawan kudin da ke akwai.
3. Sabon tsari zai taimaka wajen shigo da kowa cikin harkokin kuɗi da rage yawan hada-hadar kuɗi laƙadan da kuma tabbatar da cewa Najeriya ta bi sahun tarin hada-hadar kuɗi a zamanance.
4. Sauya fasalin kudin kuma zai taimaka wajen yaki da almundahana domin hakan zai sa a yi ta kokarin dawo da manyan takardun kudi wadanda su ne ake amfani da su wajen almudahana kuma hukumomin tsaro za su iya gani idan ana kokarin fitar da irin wadannan kudaden daga bankuna.