Darajar Naira ta fara farfaɗowa a kasuwa - Za ta ɗore ko kuwa?

Takardun naira da na dala

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Naira ta farfaɗo da kashi sama da 20 cikin 100 a kwana uku
    • Marubuci, Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja

Darajar kuɗin Najeriya ta naira ta ɗan farfaɗo da kusan kashi 22 cikin 100 a kwana uku idan aka kwatanta da faɗuwar da ta dinga yi da kashi 36.52 cikin 100 a shekarar 2022.

Ɗan kasuwar canji a Kano, Sani Dada, ya faɗa wa BBC Hausa cewa kasuwar canji ta bayan-fage ta tashi a ranar Alhamis ana canzar da dalar Amurka ɗaya tsakanin N750 zuwa N760 a Kano.

A makon da ya gabata, an canzar da dala ɗaya kan N890 a kasuwar da ba ta hukuma ba, yayin da farashin bai wuce N439 ba a farashin gwamnati.

Sai dai ana danganta farfaɗowar nairar da ƙarancinta da aka fara fuskanta a kasuwar canjin sakamakon wa'adin da CBN ya bayar na soke amfani da tsofaffin takardun naira na N200 da N500 da N1,000 na ƙaratowa.

Cikin matakan da CBN zai iya ɗauka akwai ƙara yawan dalar da yake bai wa bankuna a kullum, wanda hakan zai rage yawan nemanta da 'yan kasuwa da ɗaiɗaikun mutane ke yi.

Ranar 31 ga Janairun 2023 ne CBN ya bayar a matsayin wa'adin da tsofaffin kuɗaɗen za su daina aiki, yana mai cewa ya ɗauki matakin ne saboda rage yawan garin kuɗi a hannun mutane da kuma daƙile masu buga jabun kuɗi.

A cewar CBN, matakin zai taimaka wajen rage hauhawar farashi a faɗin ƙasa, ƙari a kan sauran matakai na ƙara yawan kuɗin ruwa.

Haka abin yake a Legas da Abuja da Fatakwal

Naira

Asalin hoton, Getty Images

Rahotanni sun nuna cewa darajar nairar ta samu tagomashi har a sauran manyan birane kamar Legas da Abuja da Fatakwal - babban birnin Jihar Ribas.

Saboda yadda lamarin ke sauyawa cikin sauri da kuma rashin tabbas, babu wani takamaiman farashin da aka canzar da dalar a Legas a ranar Alhamis.

An canzar da dala kan N700 har zuwa N730.

A birnin Fatakwal ma ta sauko zuwa N700 da kuma N720.

'Yan kasuwar canji a Abuja sun ce tun daga ranar Talata suka fuskanci faɗuwar darajar dalar saboda dalilai daban-daban.

Me ya jawo faɗuwar darajar dala?

Bayanan bidiyo, Abin da ya sa darajar dala ta fadi a Najeriya

Masana tattalin arziki da sauyin kuɗaɗe na ganin cewa abin da ya sa darajar dala ta hauhawa a 'yan kwanakin nan shi ne dai dalilin da ya karya ta - sauya fasalin wasu takardun naira.

Yusha'u Aliyu, masanin tattalin arziki kuma ɗan kasuwar sauyin kuɗaɗe, ya ce dalar ta ragargazo ne bisa dalili uku.

"Na farko, duk lokacin da aka ce za a sauya fasalin kuɗi ɗabi'a ce ta mutane cewa za su yi gaggawa wajen neman dala, abin da ya ɗaga darajarta ke nan," in ji shi.

"Abin da kuma ya sauko da ita shi ne rashin saka ƙa'ida na yawan nairar da mutum zai mayar banki, kamar yadda CBN ya nema, ya sa sun zuba kuɗaɗe masu yawa. Hakan ya jawo yawan masu neman dalar ya ragu."

Dalili na biyu da ya bayar shi ne na raguwar masu tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje.

"Galibin mutanen da za su nemi dalar don su yi tafiye-tafiye, kamar ɗalibai, babu su a yanzu, sai ma masu son dawowa gida."

Dalili na uku kuwa, labarin ƙarya ne ya haddasa shi - cewa Amurka za ta daina amfani da wasu daga cikin takardun dala kamar yadda Najeriya ke shirin sauya wasu na naira.

"Duk da cewa ƙarya ne, hakan ya sa masu neman dalar sun firgita kuma suka daina nemanta."

Wani abu da ya fito fili a yanzu shi ne da ma ana sayen dalar ne akasari saboda a ɓoye ta ba don a yi kasuwanci ba.

Za ta ɗore ko murna za ta koma ciki?

Abin da talakawa da sauran gama-garin 'yan kasuwa ke fatan sani shi ne ko wannan nasara da nairar ta yi za ta ɗore ko kuwa ta ɗan lokaci ce - kafin dalar ta sake hayewa.

Masana na ganin abin ba mai ɗorewa ba ne saboda har yanzu ba a kai ga cimma abin da CBN ke son cimmawa ba game da sauya fasalin nairar.

"Za ta iya yin tashin gwauron-zabi kuma yayin da ake kusantar ranakun ƙarshe na wa'adin da CBN ya bayar na janye tsofaffin kuɗin. Mutane za su sake komawa rububin neman dala saboda rashin tabbas game da sababbin takardun.

"Haka za ta yi ta yi a wannan tsakanin har zuwa lokacin da za a gama tattara kuɗin ƙasar a bankuna daga hannun mutane."

Bugu da ƙari, yanzu mutane sun fahimci cewa labarin da ake yaɗawa cewa Amurka za ta daina karɓar takardar dala ta $100 ba gaskiya ba ne, saboda haka waɗanda suka ƙi sayen dalar saboda wannan dalili za su koma kasuwar.