Buhari ya ƙaddamar da e-naira: Abin da ya kamata ku sani game da kuɗin intanet na Najeriya

Kudi

Asalin hoton, CBN

Bayanan hoto, Wasu daga cikin alfanun kudin na intanet su ne inganta tsarin kasuwanci, wadatuwar kudade cikin sauki da kuma saukin kasafi da haraji

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ƙaddamar da kuɗin intanet na ƙasar e-Naira ko kuma nairar da ake kashewa ta intanet.

Shugaban ya ƙaddamar da kuɗin intanet ɗin ne ranar Litinin a Abuja, babban birnin ƙasar.

Tun farko an tsara ƙaddamar da kuɗin intanet ɗin ne a farkon wannan wata, amma sai Babban Bankin Nijeriya ya ɗage batun zuwa gaba.

Bankin ya ce ya shafe shekaru yana bincike a kan e-Naira kuma "an ɓullo da ita ne da zummar sauƙaƙa wa kowane ɓangare na al'umma gudanar da harkokin kuɗinsu".

Tun da farko Babban Bankin Najeriya, CBN, ya ce a watan Oktoba 'yan kasar za su soma amfani da kuɗin intanet na e-Naira.

CBN ya bayyana haka bayan ya haramta amfani da kudin Cryptocurrency saboda rashin gamsuwa da yadda tsarinsa yake.

e-Naira kudi ne da zai bai wa mutane damar yin harkokin kasuwanci ta intanet.

Tsarin zai yi aiki da kamfanin fasaha na Bitt Inc., a kokarin fara amfani da kudin intanet na e-Naira.

CBN ya zabi Bitt Inc. daga cikin manyan kamfanonin fasaha da dama da suka fafata wajen ganin sun samu kwangilar aiki tare da Bankin domin samar da wannan kudi cikin tsaro da tsari mai inganci.

Sanarwar da CBN ya fitar ta kuma bayyana wasu daga cikin alfanun kudin na intanet din da suka hada da inganta tsarin kasuwanci, wadatuwar kuɗaɗe cikin sauki da kuma saukin kasafi da haraji.

Ga wasu abubuwa da suka kamata ku sani game da kuɗin intanet na e-Naira:

Kuɗin na e-Naira zai saukaka kasuwanci cikin sauki amma yana da bambanci da sauran kuɗaɗen intanet saboda CBN ne kaɗai yake da alhakin samar da shi.

CBN ya ce kuɗin na e-Naira zai taimaka wajen gudanar da harkokin kasuwanci cikin sauki da kuma zai kunshi kowa da kowa sannan zai bunkasa tsarin kasuwanci ba tare da amfani da tsabar kuɗi ba.

Kazalika tsarin e-Naira ba ya bukatar tsabar kuɗi kwata-kwata.

Haka kuma e-Naira ba ya hawa da sauka kamar saura kuɗin intanet irin su Bitcoin, sai dai za a rika amfani da shi kamar yadda ake aiki da Naira.

Tun da tsarin e-Naira zai kasance irin na Naira ne, darajarsu za ta zama iri daya da ta Naira.

Tsarin e-Naira zai kasance daban da na yadda ake bude asusu a bankuna; za a samar da wata jaka da za a rika adana kuɗin kowanne mutum ta hanyar ba shi wasu lambobi da shi kaɗai ne yake da irin su.

Kuɗi ne da aka amince kowa ya yi amfani da su a Najeriya, kuma ba zai rika tara kuɗin ruwa ba.

Za kuma a samar masa da wasu lambobi na tsaro da za su hana gurbata shi.