Osimhen ya ce yana kaunar Napoli a zuciya ba iyaka

 Victor Osimhen

Asalin hoton, Getty Images

Ɗan kwallon Napoli, Victor Osimhen ya ce yana kaunar ƙungiyar ba iyaka ya kuma yi kira ga magoya baya su haɗa kai a tsakaninsu.

An yi ta caccakar ƙungiyar da ke buga Serie A, bayan da ta saka wani bidiyo a TikTok mai kamar cin mutunci ga ɗan wasan tawagar Najeriya, bayan da ya ɓarar da fenariki a makon jiya.

Amma ƙungiyar ta sanar cewa ba ta yi hakan bane da nufin ɓata ran ɗan kwallon mai shekara 24 ba.

A faifan bidiyon har da wata 'yar murza da ke cewa ''Bani fenariti''.

Bayan da ya ci kwallo a wasan da Napoli ta doke Lecce 4-0 a Serie A, Osimhen ya bayyana yadda yake kaunar ƙungiyar a shafinsa na Istagram.

''Zuwa da nayi birnin Napoli a 2020, shawara ce mai matukar mahimmanci da na yanke'' in ji Osimhen.

''Mutanen birnin sun nuna min kauna, kuma ba zan taɓa bari wani ya shiga tsakanin mu ba.

Victor Osimhen

Asalin hoton, Getty Images

''Ina da abokai da yawa a birnin Napoli, kuma sun zama ɓangaren iyalai na a koda yaushe a rayuwa. Ina jinjina ga 'yan Najeriya da duk wanda ya goyi da bayana da waɗanda suka kirani a halin da na tsinci kaina.''

''Mu ci gaba da yaɗa zaman lafiya da girmama juna da fuskantar kanmu''.

Tun farko, wakilin Osimhen ya yi barazanar ɗaukar mataki na shari'a a kan Napoli kan faifan bidiyon, wadda daga baya ta goge.

Ministan wasannin Najeriya, John Owan Enoh ya ce suna bin hanyar diflomasiyya da Italiya kan lamarin.

Osimhen ya koma Napoli a matakin wanda ta saya mafi tsada kan fam miliyan 70 a kakar 2020.

Tun daga lokacin ya zama kashin bayan kungiyar, wanda ya taimaka mata ta lashe Serie A na bara a karon farko bayan shekara 33.

Ɗan wasan ya ci kwallo 26 a kakar da ta wuce a fafatawa 32 da ya yi mata.