Abin da ya kamata ku sani kan wasan Fulham da Chelsea

Pochetino

Asalin hoton, Getty Images

Fulham za ta karɓi bakuncin Chelsea a karashen wasan mako na bakwai a gasar Premier League ranar Litinin a Craven Cottage.

Fulham, wadda ta yi wasa shida mai maki takwas tana mataki na 12 a kasan teburi, Chelsea kuma tana ta 15 da makinta biyar.

Fulham za ta ci gaba da auna koshin lafiyar mai tsaron bayanta, Kenny Tete, wanda ke jinya.

Sai dai Sasa Lukic ya murmure kuma ya fara atisaye, amma har yanzu Tosin Adarabioyo da kuma Adama Traore na jinya.

Ɗan wasan Chelsea, Nicolas Jackson na hutun hukuncin dakatarwar wasa, shi kuwa Malo Gusto zai yi hutu karo na biyu daga dakatar da shi da aka yi karawa uku.

Ben Chilwell na jinya, sai dai watakila Carney Chukwuemeka da kuma Noni Madueke su samu damar buga wasan.

Karawa tsakanin kungiyoyin biyu:

Fulham ta ci wasan karshe da suka kara 2-1 a Craven Cottage ranar 12 ga watan Janairu, wasa na biyu kenan da ta yi nasara a fafatawa 32 da ta fuskanci Chelsea a Premier League.

An kori 'yan wasan Chelsea a fafatawa biyun da Fulham ta ci Chelsea a Cottage, shi ne wanda aka kori Joao Felix a bara da wanda aka bai wa William Gallas jan kati a Maris din 2006.

Dukkan wasa ukun da kungiyoyin biyu suka kara ranar Lahadi a fafatawar Litinin canjaras suka yi.

Fulham

Raheem Sterling

Asalin hoton, Getty Images

Fulham ta kasa cin wasa daga tara a jere da ta buga na hamayya da kungiyoyin birnin Landan a Premier League tun daga lokacin da ta yi nasara a kan Chelsea a watan Janairu, wadda aka doke karo biyar da canajaras huɗu.

Kwallo bakwai da ta ci 'yan wasa daban-daban ne suka zura mata a raga har da biyar a kakar nan.

Marco Silva na bukatar yin nasara ɗaya domin cin wasa na 50 a Premier League, wanda ya yi canjaras 28 aka doke shi 62 a gasar.

Andreas Pereira zai buga wasa na 200 a Premier League, idan an saka shi a karawar.

Chelsea

Mauricio Pochettino

Asalin hoton, Getty Images

Chelsea ta haɗa maki biyar daga wasa shida - kaka mafi muni da ta fara tun daga 1978/79, wadda daga lokacin ta yi kasa zuwa karamar gasa.

Kungiyar Stamford Bridge ta ci wasa biyu daga 18 na baya da ta yi da samun maki 12.

Mauricio Pochettino bai yi nasara ba a wasan waje sau 14 a jere a Premier League tun bayan da ya ja ragamar Tottenham ta yi nasara a kan Fulham 2-1 a Janairun 2019, wanda aka doke sau 10 da canjaras huɗu.

Watakila Raheem Sterling ya buga wasa na 300 da za a fara wasa da shi cikin fili a Premier League a ranar ta Litinin.