Mai tsaron raga Vaessen ya farfaɗo a asibiti bayan gware da aka yi masa

 Etienne Vaessen

Asalin hoton, EPA

Mai tsaron ragar RKC Waalwijk, Etienne Vaessen ya farfaɗo a kan gadon asibiti bayan gware da aka yi masa a wasa da Ajax ranar Asabar.

An tsayar da karawar a minti na 84, bayan da golan, mai shekara 28 ya yi taho mu gama da ɗan wasan Ajax, Brian Brobbey.

Golan ya faɗi kasa wanwar ko motsi baya yi, amma daga baya ya ɗan motsa a lokacin da ake ƙoƙarin fitar da shi daga fili a kan gadon da ake ɗaukar marasa lafiya.

'Yan wasa da yawa sun yi ta kiran a kawo agajin gaggawa da wuri, wasu ma kuka suka dinga yi a lokacin da ake duba koshin lafiyar Vaessen a cikin fili.

Ba a koma wasan ba, duk da saura minti shida a tashi daga karawar, a lokacin Ajax na cin 3-2 a babbar gasar tamaula ta Netherlands a karshen mako.

RKC ta tabbatar da cewa an kai Vaessen asibiti ya kuma farfaɗo cikin koshin lafiya, amma ana ci gaba da kula da shi.