An dakatar da Demiral na Turkiyya wasa biyu kan murnar cin kwallo

Asalin hoton, Getty Images
An dakatar da ɗan wasan bayan Turkiyya Merih Demiral wasanni biyu kan murnar da ya yi lokacin da ya ci kwallo a wasan da suka yi da Austria.
Mahukunta sun ce murnar tasa alamar girmamawa ce ga masu kishin kasa 'yan mazan jiya na Turkiyya.
Demiralmai shekara 26 shi ne ya ci wa Turkiyya kwallaye biyun da ta ci Austria 2-1 suka samu damar zuwa wasan kusa da daf da na ƙarshe wanda za su fafata da Netherlands a nan gaba.
Dan wasan bayan Al-Ahlin ya yi murnar cin kwallonsa ta biyu ne da wata alama irin ta dila, wadda ke nuna goyon baya ga masu ra'ayin rikau da suke da alaka da jam'iyyar mai mulki a Turkiyya ta National Movement Party.
Demiral ya ce murnar da ya yi wadda aka haramta a Austria da Faransa ya shirya ta ne ko da ya ci kwallonsa ta biyu.







