Yadda harin ƴan bindiga ya jefa al'ummar arewacin Najeriya mazauna Imo cikin wani hali

,,

Asalin hoton, Getty Images

Al'ummar arewacin Najeriya da ke zaune a Jihar Imo, suna cikin wani yanayi na alhini da zaman makoki, bayan hari da ake zargin wasu 'yan bindiga sun kai kan wasu takwarorinsu. Maharan dai sun halaka akalla mutum shida, tare da raunata wasu da dama.

Wannan lamari dai ya faru ne a garin Ubaku na yankin Ƙaramar Hukumar Owerri ta yamma, kuma ya afku tsakanin ƙarfe goma zuwa sha ɗaya na daren Litinin, amma sai a ranar Talata ne aka samu ɗauko gawarwakin waɗanda suka rasa ransu sa'annan aka yi jana'izarsu.

Rundunar 'yan sandan Najeriya, wadda ta tabbatar da afkuwar lamarin, ta lashi takobin gano maharan.

Alhaji Hamza Abdullahi, wanda ɗaya ne daga cikin shugabannin ƴan arewacin Najeriya mazauna Jihar Imo, ya bayyana cewa tun da farko maharan sun zo ne sanye da kayan sojoji inda suka zauna, sai mutanen wurin suka ɗauko shayi suka ba su domin karramawa.

Ya bayyana cewa bayan sun sha shayin sai suka kama hanya za su tafi sai suka juyo suka harbe su da bindiga.

Ya bayyana cewa daga cikin mutanen da aka kashe, maharan har sai da suka cire kan mutum guda suka tafi da shi, sannan kuma ya ce akwai aƙalla mutum bakwai da suke asibiti suke karɓar magani sakamakon raunin da aka ji musu.

Haka kuma ya ce babu waɗanda suke zargi da kai wannan hari sai ƴan ƙungiyar IPOB da ke fafutikar kafa ƙasar Biafra.

Ana dai yawan samun barazana daga ƙungiyar IPOB musamman a kudu maso gabashin Najeriya inda ta kai ga har a wasu jihohin ma ƙungiyar na saka dokar hana fita.