Abin da ya sa 'yan bindiga ke halaka 'yan siyasa a yankin ƙabilar Igbo

'Yan bindigar da ke kai hare-hare a kudu maso gabashin Najeriya

Asalin hoton, AFP

'Yan bindiga sun sake datse kan wani tsohon ɗan Majalisar Dokokin Jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya, inda ƙabilar Igbo ta fi rinjaye.

Rahotanni sun bayyana cewa a ranar Talata ne aka ga gawar Nelson Achukwu, mai lalurar nakasa, bayan danginsa sun biya kuɗin fansa kusan naira miliyan 15.

Rundunar 'yan sanda ta Anambra ta ce lamarin ya faru ne mako biyu bayan 'yan bindigar sun sace shi.

Gwamnatin Najeriya ta sha ɗora alhakin hare-hare irin waɗannan kan ƙungiyar Indeginous People of Biafra (IPOB) mai neman ɓallewa tare da kafa ƙasar Biafra a yankin na kudu maso gabas. Sai dai IPOB ta sha musanta zargin.

Yayin cire wa mutane kai

Soludo TV

Asalin hoton, Soludo TV

Wannan ne karo na uku da mahara ke cire wa 'yan siyasa ko jami'an tsaro kai yayin hare-haren, inda suka kashe mutum huɗu jimilla.

Da ma rundunar 'yan bindiga ta IPOB mai suna Eastern Security Network (ESN) ta sha kai wa mazauna yankin hare-hare da zummar tabbatar da dokar zaman gida a kowace Litinin. Ta ce tana yin hakan ne don nuna goyon baya ga jagoranta, Nnamdi Kanu, da ke kurkuku bisa zargin ta'addanci da tayar da hankalin jama'a.

Sai dai babu tabbas game da ƙungiya ko kuma wanda ya aikata kisan na baya-bayan nan.

A watan Mayu da ya gabata, mahara sun sace tare da datse kan wani soja, Linus Musa Audu, da amaryarsa ita ma soja, Gloria Mathew, yayin da suke kan haryar zuwa shagalin bikinsu a Jihar Imo.

A watan na Mayu, 'yan bindigar suka sake cire wa Ɗan Majalisar Dokokin Anambra Okechukwu Okoye kai.

Kashe-kashen gilla a jihohin na kudu maso gabas na sake ɗaukar sabon salo yayin da Najeriya ke tunkarar babban zaɓe 2023.

'Yan bindigar da ke kai hare-hare 'yan ƙabilar Igbo ne - Gwamna Saludo

Gwamnan Charles Soludo ya ba da tayin ladan miliyan 10 ga duk wanda ya ba da bayanai kan 'yan bindiga

Asalin hoton, ANSG

Gwamnan Jihar Anambra Charles Soludo ya ce akasarin 'yan bindigar da ke kai hare-hare a jihar 'yan ƙabilarsu ne ta Igbo.

Mista Soludo ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan kisan ɗan majalisa Okechukwu Okoye a watan Mayu, yana mai ba da tayin ladan naira miliyan 10 ga duk wanda ya ba da bayanai game maharan da kuma 'yan bindigar da ke tilasta wa mazauna jihar zaman gida duk Litinin.

"Bari na faɗa ƙarara, waɗannan gungun miyagun da ke haddasa fitina a Anmbra 'yan ƙabilar Igbo ne akasari daga sauran jihohin kudu maso gabas da ke son aikata laifi da kuma kallafa wa sauran mutane aƙidunsu," in ji Soludo.

"Abin baƙin ciki, kowane gungun miyagu na iƙirarin su 'yan neman 'yanci ne, abin da ya sa da wuya a iya tantance sahihiyar ƙungiuyar neman 'yanci daga na aikata laifuka. Abin haushin kuma shi ne yanzu 'yan daba sun mamaye yankin."

IPOB ta hana 'yan siyasa sakat a yankin kudu maso gabas

Ƙungiyar IPOB ta sha musanta zarge-zargen da ake yi mata na kai hare-hare

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Gabanin zaɓen gwamnan Jihar Anambra da aka yi ranar 6 ga watan Nuwamban 2021, hare-haren ƙungiyar IPOB sun sa ƴan siyasa ɓuya tare da dakatar da kusan dukkanin harkokin siyasa a jihar.

Da farko ƙungiyar ta sha alwashin hana gudanar da zaɓen baki ɗayansa kafin daga baya ta sauya shawara.

Hatta ɗan takarar gwamna na jam'iyyar All Progressive Congress (APC), Andy Uba, sai da ya dakatar da ƙaddamar da yaƙin neman zabensa da ya shirya yi.

Haka shi ma ɗan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Mista Valentine Ozigbo, ya ɗaga yaƙin neman zabensa zuwa wani lokaci.

Bayanai sun nuna cewa kungiyar ta IPOB ta zafafa hare-haren da har ta kai ga ƴan siyasa da duk wasu magoya baya na ɓoye alamun wata jam'iyya a tare da su.

Wasu rahotannin ma na bayyana cewa hatta tutar Najeriya da tambarin ƙasar ba a bayyana su a jikin wasu gine-gine don kada a kai hari wuraren.

Daga cikin hare-haren da IPOB ta kai ranar 31 ga watan Nuwamba, ƴan bindiga sun ƙona gidan wani jigo a jam'iyyar APC, Joe Igbokwe, a garin Nnewi, wanda ya wallafa bayani a shafinsa na sada zumunta game da harin.