Sunday Igboho: Mun gano ɗan majalisar da ke ɗaukar nauyin mai fafutikar kafa ƙasar Yarabawa - Malami

Asalin hoton, OTHERS
Gwamnatin Najeriya ta ce ta bankaɗo masu ɗaukar nauyin ɗan gwagwarmayar kafa ƙasar Yarabawa mai suna Sunday Adeyemo - wanda aka fi sani da Sunday Igboho.
A cewar Ministan Shari'a Abubakar Malami, daga cikinsu akwai wani ɗan majalisar tarayya, yayin da aka bai wa Igboho kuɗi ta wasu asusun banki 43.
Sai dai bai bayyana sunan ɗan majalisar ba.
Da yake magana a Abuja ranar Juma'a, ministan ya ce wani kwamati da gwamnati ta kafa ya gano cewa Igboho na da alaƙa da ayyukan Boko Haram bayan ya karɓi kuɗi daga wasu da kotu ta ɗaure a Daular Larabawa kan bai wa ƙungiyar tallafi.
Malami ya ce Igboho ya yi amfani da kamfaninsa mai suna Adesun International Concept Ltd don karɓar kuɗi kuma ya tura naira miliyan 12 ga kamfanin Abbal Bako & Sons, a cewar Malami.
"Idan ba a manta ba, kamfanin Abbal Bako & Sons da dillalinsa Abdullahi Umar Usman na cikin waɗnda ake zargi a binciken ɗauakr nauyin ta'addanci," in ji Malami. "Shi kuma Abdullahi Umar Usman an alaƙanta shi da Surajo Abubakar Muhammad (wanda aka yanke wa hukuncin ɗaurin rai-da-rai a Daular Larabawa kan tallafa wa ta'addanci [Boko Haram])."
Kazalika, Malami ya ce suna gab da binciko waɗanda suke ɗaukar nauyin ayyukan Nnamdi Kanu, wanda shi ne jagoran 'yan aware da ke son kafa ƙasar Biafra.
Ya ƙara da cewa Nnamdi na da hannu a zanga-zangar EndSars da ta girgiza Najeriya a ƙarshen shekarar 2020.
Laifukan da ake zargin Nnmadi Kanu da aikatawa

Asalin hoton, Alloy Ejimako
Abubakar Malami ya bayyana cewa kwamitin ya gano laifukan da ake zargin shugaban kungiyar 'yan aware na kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu da aikatawa.
Hakan na zuwa ne kwana ɗaya bayan gabatar da Mista Kanu a gaban kotu, inda gwamnatin tarayya ke tuhumarsa da wasu karin laifuka, dori a kan wadanda aka fara gabatarwa a lokacin farko da aka gurfanar da shi gaban shari'ar.
Kwamitin wanda shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar karkashin jagorancin Ministan shari'a na Najeriya ya ce ya gono gaskiyar cewa bisa umurnin Nnamdi Kanu, mambobin IPOB da ESN sun kai munanan hare-hare kan ofisoshin INEC da nufin kawo cikas ga tsarin dimokradiyya a Najeriya.
Gwamnatin ta bayyana hari 10 da aka kai tsakanin Oktoban 2020 zuwa watan Yunin 2021 kamar haka:
- Bisa tunzurawar Nnamdi Kanu, mambobin IPOB da na ENDSARS sun kai hari tare da kashe jami'an tsaro da dama, da lalata gine-ginen mutane da na gwamnati, da suka haɗa da ofisoshin ƴan sanda, da motocin sufuri
- A ranar 21 ga Oktoban 2020 Nnamdi Kanu ya tunzura mambobin IPOB ta kafar rediyonsa na Biafra inda suka ƙone ofishin ƴan sanda da kashe jami'an tsaro da lalata dukiyar jama'a.
- Jami'an tsaro 175 IPOB da ESN suka kashe da suka ƙunshi ƴan sanda 128 da sojoji 37 da wasu jami'an tsaro 10
- Kisan wasu fitattun ƴan Najeriya da suka haɗa da sarakunan gargajiya Obi 1 na Okwudor da Eze E. Anayochukwu Durueburuo da Eze Sampson Osunwa na Ihebineowerre da kisan Dr. Chike Akunyili da wasu mutum takwas da suka haɗa har da Alhaji Ahmed Gulak da aka kashe a ranar 30 ga Mayun 2021
- An kai hare-hare kan cibiyoyin INEC guda 19 wanda ya kai ga ƙone mota 18 da kayan zaɓe a jihohin Abia, Akwa-Ibom, Anambra, Cross River, Enugu, Ebonyi and Imo
- Hedikwatar ƴan sanda 164 IPOB ta kai wa hari ciki har da Owerri babban birnin jihar Imo wanda ya kai ga kisan ƴan sanda 128, kuma 144 suka jikkata da lalata motoci 628
- An saci makamai 396 da albarussai 17,738 a hare-haren IPOB da ESN
- An kai hare-hare uku a cibiyoyin gyara hali ciki har da babbar cibiyar NcoS da ke Owerri jihar Imo inda fursunoni 1,841 suka tsere
- IPOB ta kai hari hedikwatar hukumar kula da shige da fice ta Najeriya a Umuahia jihar Abia wanda ya kai ga kisan jami'i ɗaya.
- IPOB da ESN sun kai hare-hare da dama da lalata dukiyoyin jama'a lokacin zanga-zangar EndSARS da kuma zanga-zangar masu neman ƙasar Biafra a yankunan kudu maso gabas da kudu maso kudu musamman fadar Oba na Lagos da gidan gwamnan Imo Sanata Hope Uzodinma da aka ƙone da ƙone motoci 150 a tashar motocin fasinja a Lagos







