Ƴan IPOB sun razana ƴan siyasa sun kasa fitowa kamfe a Anambra

Mayakan IPOB

Asalin hoton, Getty Images

Hare-haren kungiyar ƴan aware ta IPOB, da ke neman kafa kasar Biafra a kudu maso gabashin Najeriya sun sa ƴan siyasa ɓuya tare da dakatar da kusan dukkanin harkokin siyasa a jihar Anambra.

Hukumar zaɓe ta Najeriya, INEC ta shirya gudanar da zaben gwamnan jihar a ranar 6 ga watan Nuwamba, domin maye gurbin gwamnan da ke kan kujera Willie Obiano na jam'iyyar APGA, wanda yake kammala wa'adinsa na biyu kasancewar ba shi da dama bisa tanadin tsarin mulki ya sake neman kujerar.

Ko ɗan takarar gwamna na jam'iyyar All Progressive Congress, APC, Mista Andy Uba ya dakatar da ƙaddamar da yaƙin neman zabensa da ya shirya yi ranar Asabar da ta gabata.

Haka shi ma dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a zaɓen Mista Valentine Ozigbo ya dakatar ta yakin neman zabensa zuwa wani lokaci.

Bayanai na nuna cewa kungiyar ta IPOB ta zafafa hare-haren da har ta kai ga ƴan siyasa da duk wasu magoya baya na ɓoye alamun wata jam'iyya a tare da su.

Wasu rahotannin ma na bayyana cewa hatta tutar Najeriya da tambarin kasar ba a bayyana su a jikin wasu gine-ginen don ka da a kai hari wuraren.

Daga cikin hare-hare wanda kungiyar ta kai ranar Lahadin da ta gabata ƴan bindiga sun ƙona gidan wani jigo a jam'iyyar APC, Joe Igbokwe, a garin Nnewi wanda ya yi bayani a shafinsa na sada zumunta da muhawara game da harin.

Mista Igbokwe ya yi godiya ga Ubangiji kan yadda ya ce harin bai rutsa da kowa daga cikin mutanen gidan nasa ba.

Mayakan IPOB

Asalin hoton, ESN

Rundunar ƴan sanda ta jihar Anambra ta tabbatar da kai harin. Haka kuma wasu rahotanni sun bayyana ƙarin hare-hare da aka kai a garin na Nnewi a ranar ta Lahadi.

Rahotannin sun ruwaito cewa an ga ƴan bindigar kungiyar awaren cikin motoci hudu inda suka far ma wata mota ta jam'ian ƴan sanda na farin-kaya DSS, inda suka ƙona ta.

Haka kuma ƴan IPOB din sun kai hari ofishin hukumar kiyaye haɗura shi ma a garin na Nnewi inda aka ce sun yi harbe-harbe, ko da yake ba a bayar da labarin ko harin ya rutsa da wani ba.

Sai dai a yayin da suka ci gaba da karaɗe sassan birnin rahotanni sun ce sun riƙa harbin mutane, a lokuta da kuma wurare daban-daban a garin.

Daga ciki har da wasu ƴan yankin arewacin Najeriya, inda daya daga ciki wanda mai sana'ar sayar da rake ne ya rasu, kamar yadda wani Bahaushe mazaunin garin ya shaida wa BBC.

A ranar Juma'a ma kamar yadda bayanai suka nuna ƴan bindiga sun bude wuta kan ƙwambar motocin wani dan majalisar tarayya mai wakiltar wani yanki na Nnewi Chris Emeka Azubogu.

A yayin harin wani dan sanda da wani direba sun rasa ransu, sannan kuma maharan an ce sun ƙona wani ofishin ƴan sanda duk a yankin.

Ko a ranar Laraba an hallaka mutum bakwai da suka hada da Dr Chike Akunyili, mijin marigayiya tsohuwar shugabar hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya kuma tsohuwar minista, Dr Dora Akunyili, a wasu hare-haren na tsakar rana.

Kungiyar IPOB ta zafafa kai hare-hare a jihar ta Anambra da ma sauran sassan kudu maso gabashin Najeriya, a yunƙurinta na ɓallewa daga kasar, yayin da hukumomi ke ci gaba da gurfanar da shugabanta Nnamdi Kanu a gaban shari'a.