Sojojin Najeriya sun zargi 'yan Ipob da fille kan wasu jami'ansu da ke shirin aure

Asalin hoton, Audu M Linus and Gloria Matthew
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai kuma ya nuna ɓacin ransa dangane da fille kan wasu sojoji biyu da ke shirin aure waɗanda ake zargin ƴan IPOB da aikatawa.
An fille kawunan mutanen ne a karshen mako yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Jihar Imo domin yin bikin aurensu na gargajiya.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Malam Garba Shehu ya yi, Shugaba Buhari ya yi ta'aziyya ga rundunar sojin Najeriya da kuma iyalan Master Warrant Officer Audu Linus da kuma Private Gloria Mattew waɗanda ƴan IPOB suka fille kawunansu bayan sun harbe su.
Shugaban ƙasar ya nuna kaɗuwarsa kan wannan lamari inda ya alaƙanta wannan kisa da dabbanci inda ya ce wannan aika-aika ta saɓa wa al'adu da zamantakewa.
Haka kuma shugaban ya yi kira ga jagororin al'ummomi da na yankuna da na ƙasa baki ɗaya da su yi magana da murya ɗaya domin nuna cewa Najeriya ƙasa ɗaya ce kuma al'umma ɗaya ce kuma ba ta goyon bayan abin da ya kira irin wannan kisa na dabbanci.
Haka kuma shugaban ya bayar da umarni ga sojojin ƙasar da sauran hukumomin tsaro da su ganoi da kuma hukunta waɗanda ke da hannu a wannan aika-aika.
Sai dai a wata sanarwa da ƙungiyar ta IPOB ta fitar, mai magana da yawun ƙungiyar Emma Powerful ya musanta cewa ƙungiyarsu ce ta yi kisan inda ya ce sojojin ƙasar ba su gudanar da bincike ba hakanan suka laƙa musu sharri.
Me Rundunar sojin Najeriya ta ce?

Asalin hoton, Getty Images
Rudunar sojin Najeriya ta zargi 'yan kungiyar Ipob da ke neman ballewa daga kasar da hannu a fille kawunan wasu sojoji biyu da ke shirin yin aure a jihar Imo ta Kudu maso gabashin kasar.
Kakakin rundunar sojojin kasar Onyema Nwachukwu ya fitar da wata sanarwa inda ya bayyana kisan jami'an nasu a matsayin "maras dadi, kidahumanci kuma abin kyama".
Ya dora alhakin kisan kan Eastern Security Network, wani bangare na na kungiyar Ipob.
"Rundunar sojin Najeriya za ta tabbatar an hukunta wadanda suka aikata wannan mummunan aiki," a cewar sanarwar.
Kawo yanzu Ipob ba ta ce uffan ba kan wannan zargi da rundunar sojin Najeriya ta yi mata.
Wasu bidiyoyi da aka watsa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda aka kashe mutanen biyu.
A mako biyu da suka gabata, masu fafutikar ballewa daga Najeriya domin kafa kasar Biafra sun kara kaimi wajen kai hare-hare a yankin Kudu maso gabashin kasar.
Ko da a karshen makon jiya, wasu 'yan bindiga sun kashe mutum hudu, cikinsu har da wani dan-sanda a kauyuka biyu na jihar Anambra da ke Kudu maso gabashin Najeriya.
A shekarar 2014 ne Nnamdi Kanu ya kafa kungiyar Ipob domin fafutikar ballewa daga Najeriya domin kafa kasar Biafra.
A halin yanzu yana tsare a hannun hukumomin kasar inda ake zarginsa da laifuka da dama ciki har da ta'addanci, zargin da ya sha musantawa.











