Mutuwar Sarauniya Elizabeth II: Shin wanne irin sarki Charles zai zama?

Charles, wanda ya fi dadewa a matsayin yarima mai jiran gadon sarauta a tarihin Birtaniya, a yanzu ya zama sarki.

Horon da ya rika samu a matsayin magaji, wanda ya shafe tsawon shekaru 70, ya sanya shi ya zama sabon sarki da ya dade yana shiri kuma mafi tsufa da ya taba hawa karagar mulki.

Sarkin, mai shekara 73 a duniya, ya shafe tsawon lokacin da mahaifiyarsa ta dauka tana mulki yana kallon yadda aka rika samun shugabannin kasashen duniya, ciki har da Firaiminista 15 na Birtaniya da shugabannin Amurka 14.

Bayan sarautar Sarauniya Elizabeth ta biyu, wadda za a ce ta taka rawar gani, shin wanne irin sarki ne ake fatan samu? Kuma ta yaya yariman da ya saba bayyana ra’ayinsa a kan batutuwa zai kasance basaraken da ba ya goyon bayan wani bangare?

A matsayinsa na sarki , Charles ba zai kara samun fasfo dinsa ko lasisin tuki ba ko bayyana wani ra’ayi mai karfi. Zama sarki ya sha gaban kowa da kowa.

Wannan al'amari ne da ya shafi mukamai daban-daban, dokoki daban-daban, in ji Farfesa Vernon Bogdanor masanin tsarin mulki.

“Tun farko an san cewa dole ne ya sauya salo. Jama’a ba za su so sarki mai fafituka ba,” a cewar Farfesa Bogdanor.

Sarki Charles yana sane da bukatar rage yawan magana.

“Ni ba wawa ba ne. Na san mulki daban yake da sauran abubuwa ” in ji shi a hirar da ya yi da BBC.

Bayan sabon Sarki ya hau kan karagar mulki

Sarkin zai yi mulki ne a lokacin da kasar ta amince a rika tafiya da kowa da kowa fiye da wanda mahaifiyarsa ta gada kuma Farfesa Bogdanor ya yi hasashen cewa zai yi mulki ne a cikin kasar da ke da al'adu da mabiya addinai daban-daban.

Yana sa ran zai yi kokarin ganin cewa ya hada kawunan al'ummar kasar musamman tsakanin kabilu marasa rinjaye da marasa galihu

Amma Sir Lloyd Dofman, wanda ya yi aiki tare da Sarki Charles na tsawon shekaru a gidauniyarsa da ke tallafa wa mutane, ya ce ba ya tsammanin sarkin zai daina magana a kan bututuwan da suka shafi sauyin yanayi da noman da ake amfani da takin zamani da feshin magani.

“Yana da ilimi sosai, yana kuma da tasiri sosai. Yana da wuya a iya tunanin zai dakatar da wadannan abubuwa a ranar da ya zama sarki,”in ji Sir Lloyd.

Duk da wannan, babban sakon da sabon sarki zai isar shi ne dorewar ci gaba da kwanciyar hankali, in ji Victoria Murphy, mai sharhi kan al'amuran yau da kulum.

"Kada ku yi tsammanin samun gagarumin sauyi. Zai yi taka tsan-tsan," a cewarta.

Amma wanne irin salo za mu gani a mulkin sabon sarki?

Wadanda suka san shi sun ce a can kasa shi mutum ne mai kunya, mai kebewa.

Akwai alamun yaro ne da ya yi rayuwar kadaici wanda ya koka da yadda aka rika cin zalinsa da kuma kebe shi a makaranta.

“Suna jifa na da silifas har tsawon dare ko da matashin kai ko kuma su garzaya daki su buge ni da karfi,” ya rubuta a wata wasika da ya aike gida game da yadda aka rika gallaza masa a dakin kwana.

Matarsa Camilla wadda a yanzu ita ce Sarauniya Consort ta bayyana shi a matsayin mutum mai rashin hakuri, yana son a yi abubuwa cikin sauri.

Ta shaida wa wata kafar watsa labarai a hirar da aka yi da ita a lokacin da Sarki Charles ya cika shekara 70 cewa bayan kirki da mutane suke gani a bainar jama'a, yana kuma son wasa.

“Suna yi masa kallon mutumin da ba ya wasa da aiki kuma haka yake amma ina son mutane su ga wani bangare nasa da ba su taba gani ba. Mutum ne mai son wasa da yara, ya karanta musu litafin Harry Porter,“ in ji Camilla.

An haifi Charles Philip Arthur George a fadar Bukingham a ranar 14 ga Nuwamba a 1948. Lokacin da BBC ta sanar da haihuwarsa ba wai ta ba da labarin cewa sauraniya Elizabeth ta haifi da namiji ba ne amma labari ne a kan cewa mahaifyarsa ta haifi yarima.

Shekara hudu bayan haka aka nada shi yarima mai jiran gadon sarauta.

“An haife ni a cikin wannan matsayi na musamman. Kuma zan yi duk wani abin da ya kamata wajen taimako,” a hirar da aka yi da shi a 2005.

Ya kasance shugaban kungiyoyi masu zaman kansu sama da 400 kuma a 1976 ya kafa tasa kungiyar da ake kira Prince Trust ta hanyar amfani da kudin sallamarsa daga rundunar sojin ruwa.

Kungiyar ta taimaka wa matasa kusan 900,000 da suka fito daga yankunan masu fama da bakin talauci kuma wannan ya ba shi damar sanin matsalolin da mutane suke fuskanta.

Wane goyon baya Sarki Charles zai samu yayin da ya fara mulki ?

"Masaurata ba za ta dore ba idan ba ka yi la'akari da halayyar mutane ba. Idan ba sa son ka a kan mulki to ba za su ba ka hadin kai ba," a cewar Charles.

Wani bincike da aka yi a 2021 ya nuna cewa ya ci gaba da samun kwarjini da farin jini inda kashi biyu bisa uku na mutane suka yaba masa.

Amma kuri'ar jin ra’ayin jama'a ta nuna cewa ba shi da farin jini fiye da mahifiyarsa ko dansa Yarima William, don haka kawo yanzu akwai mutane da dama da ya kamata ya shawo kansu.

A yanzu Sarki Charles ya zama shugaban kasashe 14 ciki har da Ingila. Wasu daga cikin wadannan kasashe za su so su koma Jamhuriya yayin da za su ci gaba da kasancewa cikin kungiyar Commonwealth. Kuma Sarki Charles ya bayyana a sarari cewa a shirye yake don tattaunawa da wadanda suka san ya kamata domin samun sauyi.