Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sarauniya Elizabeth ta yi rayuwa ingantacciya - Sarki Charles na III
"Sarauniya Elizabeth ta yi ingantacciyar rayuwa,'' a cewar Sarki Charles na III, yayin da yake jawabi kan sadaukarwa da ta yi wa kasarta.
A wani jawabi mai sosa rai ga al'ummar Birtaniya, ya yaba wa salon rayuwar da ta yi mai nagarta da kuma son ganin mutane sun ci gaba.
Yarima Williams da Catherine, za su zama Yarima da kuma Sarauniya na Wales, in ji Sarki Charles na III, inda kuma ya nuna so da kauna ga dansa Yarima Harry da matarsa Sarauniya Meghan.
Sarauniya Elizabeth ta mutu ne salin-alin jiya Alhamis a fadarta da ke Balmoral tana kuma da shekara 96.
An yada jawabin a fadin Birtaniya a kafofin yada labarai, wanda kuma aka yi a cocin St Paul wadda aka sadaukar ga marigayiya Sarauniya Elizabeth.
A jawabinsa, Sarki Charles na III, mai shekara 73, ya ce ''Sadaukarwa da kuma bautawa kasar ta da ta yi, ba za a manta da su ba, kama daga lokutan canji da ci gaba da lokutan farin-ciki da murna da kuma na kaduwa da rashi.''
Ya sanar da cewa ya nada dansa William a matsayin Yariman Wales da kuma matarsa Catherine, a matsayin Sarauniyar Wales.
Ya kuma nuna ''kaunarsa ga Harry da Meghan a lokacin da suke ci gaba da gina rayuwarsu a kasar waje''.
Da yake magana kan matarsa Camilla, mai shekara 75, da suka shafe shekara 17 tare, wacce kuma ta dawo Sarauniya Consort a yanzu, ya ce ''Na san za ta iya gudanar da aikinta a sabon matsayinta ta hanyar bautawa kasar ta.
"Ya kuma kara da cewa rayuwarsa ta canja a yanzu, inda yake cewa '' Ba zan sake iya baiwa bangaren agaji da kuma abubuwa da nake son yi matuka ba saboda sabon nauyi da aka dora mani.''
Amma a yanzu na san cewa wannan gagarumin aiki zai tafi zuwa ga hannun mutane da aka amince da su. ''Mai jiran gadon sarautar Birtaniya, Yarima William, a yanzu ya dauki matsayin da Sarki Charles ke da shi a Scottland da kuma nauyin da ke kansa na Duchy na Cornwall.''
Kasancewar Catherine a kusa da shi, sabon Yarima da Sarauniya na Wales, na san za su ci gaba da zama abin kwatantawa a kasar mu, ta hanyar kawo taimako da ta kamata,'' a cewar Sarkin.
Da ya waiwayo kan jana'izar Sarauiyar, Sarkin ya yi fatan cewa duk da kaduwa da ake ciki na mutuwar ta a kasar da kuma mutanen Commonwealth '' za su ci gaba da tunawa da ita a matsayin abin koyi''.
Ya Karkare da cewa: "Zuwa ga mahaifiyata, a daidai lokacin da kike shirin tafiya domin riskar marigayi mahaifina, ina son in ce miki: nagode.
"Nagode da soyayyar ki da kuma sadaukarwa ga iyalin mu, ga kasa kuma, kin yi mulki mai nagarta na tsawon shekaru, wadanda ba za a taba mantawa da su ba.
Tun da farko, a wani aikinsa na farko a matsayin Sarki, Sarki Charles ya gana da Firaminista Liz Truss a fadar Buckingham da tsakar ranar yau juma’a.
Jim kadan bayan nan, lokacin da rana take haskawa, Sarkin tare da Camilla sun gaisa da mutanen da suka taru a wajen fadar Buckingham.
Dandazon mutane sun yi ta sowa da kuma furta ‘’Ran Sarki ya dade’’, wadanda kuma suka yi jerin gwano a gaban fadar.
A ranar juma’ar a Westminster, ‘yan majalisar dokoki sun yi gaisuwar ban girma ga marigayiya Sarauniya Elizabeth, inda Firaminista Liz Truss ta kwatanta ta da ‘daya daga cikin hazikan shugabanni da duniya ta taba sani’’.
Daga baya kuma, an yi ta harbin bindigogi da kuma kada kararrawa a fadin kasar domin girmama marigayiya Sarauniya Elizabeth da ta rasu a ranar Alhamis.