Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Charles ya zama sabon Sarkin Ingila
Rasuwar Sarauniyar Ingila ke da wuya, sai mulkin ya koma kan ɗanta magajinta Charles, tsohon Yariman Wales, ba tare da wani bikin naɗin sarauta ba.
Amma akwai matakai na al’adu da dama da za a aiwatar masa kafin a tabbatar da shi.
Da wane suna za a dinga kiransa?
Za a dinga kiransa da Sarki Charles na III.
Wannan ne mataki na farko na zama sabon sarki. Zai iya zaɓa daga cikin sunayensa huɗu - Charles Philip Arthur George.
Ba shi ne kaɗai wanda ke samun sauyin suna ba.
Duk da cewa shi ma mai gadon sarautar ne, Yarima William ba zai zamo Yariman Wales kai tsaye ba. Sai dai, tuni ya karɓi ɗaya tsohuwar sarautar mahaifin nasa ta Duke na Cornwall.
Ita kuma matarsa Catherine za a dinga kiranta da Duchess ta Cornwall.
Matar Charles kuwa, sabon sunanta shi ne Sarauniya Consort – consort ce kalmar da ake amfani da ita wajen kiran matar sarkin da ke kan mulki.
Yadda naɗin sarautar zai kasance
A cikin sa’a 24 na farko bayan rasuwar mahaifiyar tasa, za a ayyana Charles a matsayin Sarki.
Za a yi hakan ne a Fadar St James da ke birnin Landan, a gaban masu zaɓar sarki da ake kira da Majalisar Accession.
Sun haɗa da ƴan majalisar masarautar da wata tawagar ƴan majalisar dokoki na da da na yanzu da wasu manyan ma’aikatan gwamnati, da manyan kwamishinonin ƙungiyar Commonwealth da kuma Magajin Garin birnin Landan.
Fiye da mutum 700 ne suke da damar halarta, amma da yake abin ya zo a ƙurarren lokaci, akwai yiwuwar yawan ya ragu.
A bikin naɗi na ƙarshe da aka yi kafin wannan, a shekarar 1952, kusan mutum 200 ne suka halarta.
A wajen taron, shugaban majalisar masarautar Dan Majalisa Penny Mordaunt ne zai sanar da rasuwar Elizabeth, kuma zai karanto wata sanarwa a bayyane cikin ɗaga murya.
Kalaman sanarwar ka iya sauyawa, amma a al’adance dai jerin addu’o’i ne da alkawura da yaba wa mulkin sarauniyar tare da alkawarin goyon bayan sabon sarki.
Daga nan sai manyan jami’ai da suka haɗa da firaminista da Archbishop na Cocin Canterbury da kuma shugaban majalisar masarautar su sanya hannu.
Bayan duk waɗannan matakai, za a mayar da hankali wajen gyara duk wani abu da aka cire ko aka ƙara ko aka sabunta, a matsayin wata alama ta sabon zamani.
Abu na farko da Sarki zai fara yi
Masu naɗin sarki za su sake haɗuwa – yawanci kwana daya bayan nan – amma a wannan lokaci Sarki zai halarta, tare da ƴan majalisar masarauta.
Ba a rantsar da sabon sarki a farkon lokacin da aka naɗa shi, kamar irin yadda ake yi wa shugabannin ƙasa, kamar irin su Shugaban Amurka.
Amma sabon sarkin kan yi wani bayani – sannan zai sha rantsuwar kare Coci Scotland – kamar yadda tsarin al’ada ya tanada tun daga ƙarni na 18.
Bayan kaɗa-kaɗe da bushe-bushe, za a ayyana Charles a matsayin sabon Sarki a bainar jama’a.
Za a yi hakan ne daga saman barandar Fadar St James, inda wani jami’i da ake kira Garter King of Arms ne zai yi hakan.
Zai ce: “Allah Ya tsare Sarki”, kuma a karon farko tun shekarar 1952 za a rera taken ƙasar da kalmomin “Allah Ya tsare sarki.”
Za a yi ta harbin bindiga a Hyde Park da Hasumayar Landan da kuma a cikin jiragen ruwa na yaƙi, sai kuma a karanta sanarwar ayyana Charles a matsayin Sarki a Edinburgh da Cardiff da Belfast.
Nadin sarauta
Za a bayyana Charles a matsayin sarki a hukumance, to amma saboda shirye-shiryen da ake bukatar a yi, ba za a gudanar da bikin nadin sarautar ba nan kusa.
Sarauniya Elizabeth ta hau karagar mulki a watan Fabrairun 1952, amma ba a yi bikin nadin sarautar ba sai watan Yunin 1953.
Sama da shekaru 900 ana nadin sarautar ne a cocin Westminster Abbey, kuma Sarki William ne aka fara nadawa a cikinta, yayin da Sarki Charles zai zama na 40.
Bikin addu’o’i ne da babban limamin cocin Canterbury zai jagoranta.
A karshen bikin, zai dora kambun St Edward a kan Charles. Kambu ne na zallar zinari, da aka samar tun 1661.
A lokacin bikin nadin ne kawai sarakuna ke saka kambun saboda nauyin da yake da shi ya kai kilogiram 2.23.
Sai dai ba kamar bukukuwan aure ba, nadin sarautar ya rataya ne ga wuyan gwamnati.
Ita ce ke daukar nauyin bikin, a don haka ita ke da wuka da nama kan bakin da za su halarce shi.