Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sarauniyar Ingila Elizabeth ta II ta rasu, a cewar Fadar Buckingham
Sarauniyar Ingila Elizabeth ta II, basarakiyar da ta fi dadewa a kan karagar mulkin Birtaniya, ta rasu a Balmoral tana da shekaru 96.
Ta rasu ne bayan ta shafe shekaru 70 a kan mulki.
Iyalanta sun taru a fadarta da ke Scotland bayan an rika nuna damuwa game da yanayin koshin lafiyarta ranar Alhamis.
Sarauniyar Ingila ta hau kan mulki ne a 1952 kuma ta ga sauye-sauye da dama.
Babban danta Charles, tsohon Yarima na Wales, ne zai jagoranci kasar wajen jimami a matsayinsa na sabon Sarki da kuma shugaban kasashe 14 na kungiyar Commonwealth.
A wata sanarwa, Mai Martaba sabon Sarki ya ce: "Mutuwar mahaifiyata abar kaunata Mai Martaba Sarauniya, lokaci ne na matukar bakin ciki a gare ni da dukkan iyalaina.
"Muna matukar jimamin rasuwar Basarakiya abar bege kuma mahaifiyata abar kaunata. Na sani cewa rashinta zai matukar yi wa 'yan kasar nan da Commonwealth zafi."
Ya kara da cewa a yayin da suke jimamin rasuwarta da kuma sauyin da aka samu, shi da iyalansa za su "nutsuwa da kwanciyar hankali ne bisa sanin cewa duk fadin duniya ana girmamawa da kuma kaunar Sarauniya".
A sanarwar da Fadar Buckingham ta fitar ta ce: "Sarauniya ta rasu salin-alin a Balmoral da rana.
"Sarki da mai dakinsa za su ci gaba da kasancewa a Balmoral da wannan maraice kuma za su koma London gobe."
Dukkan 'ya'yan Sarauniya sun tafi Balmoral, kusa da Aberdeen, bayan likitoci sun sanya ido sosai kan Sarauniya.
Jikanta, Yarima William, shi ma yana can, tare da dan uwansa, Yarima Harry, yana kan hanyar zuwa Balmoral.
Firaminista Liz Truss, wacce sarauniyar ta Ingila ta nada a ranar Talata, ta ce sarauniyar ''ta samar mana da abubuwan da muke so da kuma karfafa gwuiwar mu ako da yaushe''.
Ta ce daga yanzu za a san Charles a matsayin Sarki na III.
Mulkin Elizabeth ta II a matsayin sarauniya ya biyo bayan yakin basasa, sauyi daga Sarauta zuwa Commonwealth, da karshen yakin cacar-baka da kuma shiga da kuma ficewar Birtaniya daga Kungiyar Tarayyar Turai.
An samu firaministoci 15 lokacin mulkinta fara wa da Winston Churchill wanda aka haifa a shekarar 1874 hada da Ms Truss, da aka haifa a 1975, shekara 101 bayan nan.
Ta kasance tana ganawa da firaminista a kowane mako tsawon mulkinta.
A fadar Buckingham da ke birnin Landan, dandazon mutane da ke jiran sanin halin da sarauniyar ke ciki sun barke da kuka bayan jin labarin mutuwar ta.
An yi kasa-kasa da tutar da ke saman fadar da misalin 18:30 na yamma.
An haifi sarauniya Elizabeth Alexandra Mary Windsor ne a Mayfair, da ke birnin Landan ranar 21 ga watan Afrilun 1926.
Mutane kalilan ne suka yi tunanin za ta zama sarauniya amma a watan Disambar 1936 kanen mahaifinta, Edward VIII, ya sauka daga sarauta inda ya auri wata Ba'amurkiya, Wallis Simpson, wadda sau biyu aurenta na mutuwa.
Daga nan ne mahaifin Elizabeth, King George VI ya zama sarki, kuma Lilibet, kamar yadda 'yan uwanta suke kiranta a wancan lokacin da take 'yar shekara goma, ta zama mai jiran gadon sarautar kasar.
Cikin shekaru uku, Birtaniya ta gwabza yaki da Jamus karkashin mulkin 'yan Nazi. Elizabeth da kanwarta, Gimbiya Margaret, sun kwashe galibin lokacin yakin a fadar Windsor bayan iyayensu sun ki amincewa da shawarar da aka ba su cewa su tsere zuwa Canada.
Yayin da ta kai shekara 18, Elizabeth ta kwashe wata biyar tana koyon kanikancin mota da sanin dabarun tuka mota.
Daga bisani ta bayyana cewa "Na soma fahimtar irin juriyar da ake yi a yayin da ake fuskantar kalubale."
Sadaukarwa da kaunar da Sarauniya ke yi wa kasashen Commonwealth
Lokacin yaki ta rika musayar wasiku da dan uwanta Philip, Yariman Girka, da ke aiki da rundunar sojin ruwan Burtaniya.
Soyayyarsu ta zurfafa kuma sun yi aure a cocin Westminster Abbey a ranar 20 ga watan Nuwamban 1947, a lokacin da aka bai wa Yariman sarautar Duke na Edinburgh.
Daga baya ta rika kiran shi da ‘’mai karfafa mini’‘ tsawon shekaru 74 kafin mutuwarsa a 2021 yana da shekaru 99.
Dansu na farko, Charles, an haife shi ne a 1948, sai Gimbiya Anne, wadda aka Haifa a 1950, sai Yarima Andrew a 1960, sai Yarima Edward da aka haifa a 1964.
Sun samar da jikoki takwas ga iyayen nasu, da tattaba kunne 12.
Gimbiya Elizabeth na Kenya a 1952, tana wakiltar mahaifinta da ke jinya, a lokacin da Philip ya sanar da ita cewa mahaifinta ya rasu.
Ba tare da ɓata lokaci ba ta koma London a matsayin Sarauniya.
‘’Nada ni wani abu ne da ya zo bagatatan kuma dole in yi iya kokari na," kamar yadda ta sanar daga baya.
An nada Elizabeth a cocin Westminster Abbey a ranar 2 ga watan Yunin 1953 tana da shekara 27, a bikin da masu kallo a akwatin talabijin miliyan 20 suka kalla.
Shekarun mulkinta sun zo da sauye sauye masu ma’ana da suka hada da kawo karshe mulkin Burtaniya a kasashen waje.
Elizabeth ta yi wa masarautar Burtaniya garambawul, inda ta rika ganawa da al’umma da kuma halartar tarukansu.
Sadaukarwar da ta nuna ga kasashe renon Ingila na Commonwealth ba karama bace, don ta ziyarci duka kasashen akalla sal daya.
Amma akwai lokutan da abubuwa marasa dadi suka faru.
Shekarar 1992 ta zama ta bakin ciki ga Sarauniya, don a lokacin ne aka yi wata gobara a gidanta da ke Windsor Castle, kuma auren uku daga cikin ‘ya’yanta ya mutu.
Bayan mutuwar Diana, Gimbiyar Wales a wani hatsarin mota a birnin Paris a 1997, Sarauniya ta sha suka saboda rashin bayyana alhininta cikin jama’a.
Akwai kuma tambayoyi a kan tasirin masarautar ga wannan zamanin.
Ta taba fadar cewa ‘’ba bu wata hukuma da za ta yi tsammanin na za ta fuskanci matsi daga wadanda ke goyon bayanta, ba maganar wadanda ke adawa da ita ake yi ba.’’
A matsayin ta gimbiya mai shekaru 21, Elizabeth ta sha alwashin sadaukar da rayuwarta ga yi wa al’umma aiki.
Da take tuna kalaman da ta yi bayan shekaru da dama a 1977, ta bayyana cewa ‘’duk da na yi kalaman ne da tunanin komai zai tafi lami lafiya, har yanzu ba na da na sanin yin su.’’
Ta kuma maimaita kalaman sadaukar da rayuwarta ga al’umma cikin watan Yuni a lokacin da ta cika shekara 70 a kan mulki.
An gudanar da bukukuwan azo a gani bisa al’ada, duk da rashin isassar lafiya ba ta bari Sarauniya ta halarci wasu daga cikin bukukuwan ba, to amma a lokacin ta sanar da al’ummarta cewa ‘’ Zuciyata na tare da ku.’’
Ta kuma gana da jama’a tare da ‘ya’yanta da jikokinta da tattaba kunnenta a fadar Buckingham a wani biki da aka gudanar don karramata bayan cika shekaru 70 tana mulkin.