Sarauniyar Ingila Elizabeth II ta rasu

Sarauniyar Ingila Elizabeth II ta rasu

Sarauniyar Ingila Elizabeth ta II, basarakiyar da ta fi dadewa a kan karagar mulkin Birtaniya, ta rasu a Balmoral tana da shekaru 96.

Ta rasu ne bayan ta shafe shekaru 70 a kan mulki.

Iyalanta sun taru a fadarta da ke Scotland bayan an rika nuna damuwa game da yanayin koshin lafiyarta ranar Alhamis.