Makomar Kano Pillars da Katsina United na hannun juna ranar Laraba

Kano Pillars (hagu) ta lashe kofin firimiya huɗu, yayin da Katsina United ke nema

Asalin hoton, Ikechukwu Ojibi/Katsina United

Bayanan hoto, Kano Pillars (hagu) ta lashe kofin firimiya huɗu, yayin da Katsina United ke nema

Makomar ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa masu tsananin hamayya da juna a, Kano Pillars da Katsina United, na hannun junansu a yunƙurin komawa gasar firimiyar Najeriya ta NPFL da suke yi.

Pillars za ta fafata da Katsina ne a ranar Laraba a wasan ƙarshe na cikin Rukunin Arewa a gasar Nigeria National League (NNL) a garin Asaba na Jihar Delta.

Pillars ce ke saman teburin da maki shida, yayin da Katsina ke biye mata da maki uku. Sai kuma EFCC FC mai maki 1 da kuma DMD FC maras maki.

Duk wanda ya jagoranci rukunin tsakanin abokan hamayyar shi ne zai buga wasan ƙarshe da ƙungiyar da ta lashe Rukunin Kudu, wanda Sporting Lagos ke jan ragama da maki shida, Heartland mai maki huɗu, Stormers SC mai ɗaya, sai FC One Rocket maras maki.

Tawaga biyu na saman kowane rukuni ne za su samu gurbin buga gasar NPFL a kaka mai zuwa, abin da ke nufin Katsina da Pillars duka ka iya samun gurbin.

Teburin NNL

Asalin hoton, NNL

Bayanan hoto, Pillars ta cinye wasanta biyu na cikin Rukunin Arewa

A yanzu Pillars na da ƙwallo uku da ta zira a raga cikin wasa biyu, yayin da Katsina ta ci uku kuma aka zira mata uku - ba ta da ƙwallo ko ɗaya ke nan a yanzu.

Jim kaɗan bayan tashi daga wasan wasu magoya baya suka fara taya Pillars murnar cewa sun haura gasar NPFL a shafukan sada zumunta.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X

Pillars ta tsinci kan ta a ƙaramar gasar NNL ne bayan ta ƙare a mataki na 19 a gasar NPFL da ta gabata.

Wannan ne karon farko da Pillars, wadda ta lashe kofin firimiyar sau huɗu a tarihi, ta faɗa ƙaramar gasar cikin shekara 21 bayan wani kwamatin hukumar NFF ya kwashe mata maki uku sakamakon rashin ɗa'a da magoya bayanta suka nuna a wasa da Dakkada FC.

Yayin wasan, an ga shugaban ƙungiyar na lokacin, Surajo Yahaya Jambul, ya mari mai taimaka wa alƙalin wasa Daramola Olalekan a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano.