Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Makomar Kano Pillars da Katsina United na hannun juna ranar Laraba
Makomar ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa masu tsananin hamayya da juna a, Kano Pillars da Katsina United, na hannun junansu a yunƙurin komawa gasar firimiyar Najeriya ta NPFL da suke yi.
Pillars za ta fafata da Katsina ne a ranar Laraba a wasan ƙarshe na cikin Rukunin Arewa a gasar Nigeria National League (NNL) a garin Asaba na Jihar Delta.
Pillars ce ke saman teburin da maki shida, yayin da Katsina ke biye mata da maki uku. Sai kuma EFCC FC mai maki 1 da kuma DMD FC maras maki.
Duk wanda ya jagoranci rukunin tsakanin abokan hamayyar shi ne zai buga wasan ƙarshe da ƙungiyar da ta lashe Rukunin Kudu, wanda Sporting Lagos ke jan ragama da maki shida, Heartland mai maki huɗu, Stormers SC mai ɗaya, sai FC One Rocket maras maki.
Tawaga biyu na saman kowane rukuni ne za su samu gurbin buga gasar NPFL a kaka mai zuwa, abin da ke nufin Katsina da Pillars duka ka iya samun gurbin.
A yanzu Pillars na da ƙwallo uku da ta zira a raga cikin wasa biyu, yayin da Katsina ta ci uku kuma aka zira mata uku - ba ta da ƙwallo ko ɗaya ke nan a yanzu.
Jim kaɗan bayan tashi daga wasan wasu magoya baya suka fara taya Pillars murnar cewa sun haura gasar NPFL a shafukan sada zumunta.
Pillars ta tsinci kan ta a ƙaramar gasar NNL ne bayan ta ƙare a mataki na 19 a gasar NPFL da ta gabata.
Wannan ne karon farko da Pillars, wadda ta lashe kofin firimiyar sau huɗu a tarihi, ta faɗa ƙaramar gasar cikin shekara 21 bayan wani kwamatin hukumar NFF ya kwashe mata maki uku sakamakon rashin ɗa'a da magoya bayanta suka nuna a wasa da Dakkada FC.
Yayin wasan, an ga shugaban ƙungiyar na lokacin, Surajo Yahaya Jambul, ya mari mai taimaka wa alƙalin wasa Daramola Olalekan a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano.