Ƙungiyar masu ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa ta dakatar da shugaban Kano Pillars

Ƙungiyar masu ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa a Najeriya ta dakatar da shugaban ƙungiyar Kano Pillars, Yahaya Surajo, sakamakon zargin sa da naushin mataimakin alƙalin wasa.

Football Club Owners Association of Nigeria (FCOAN) ta dakatar da ciyaman ɗin ne bayan an zarge shi da naushin mataimakin lafarin a wuya yayin wasa tsakanin Pillars da Dakada FC da aka buga a Kano ranar Alhamis.

Wani bidiyo da ya karaɗe shafukan zumunta ya nuna yadda Yahaya Surajo mai shekara 53 ya je kusa da lafarin da ke kan layi ana tsaka da wasa kuma ya kai masa naushi.

Pillars ce ta ci kwantan wasan na mako na 31 da 1-0 bayan an ɗaga shi a baya.

Ƙungiyar ta ce siffanta abin da Surajo ya aikata da cewa "abin takaici" kuma "wanda ba za a amince da shi ba".

"Saboda haka ƙungiyar ta dakatar da Yahaya Surajo har sai baba ta gani daga dukkan ayyukanta har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan abin takaicin," a cewar sanarwar da sakataren FCOAN Alloy Chukwuemeka ya sanya wa hannu.

Shugaban FCOAN ya ce shugaban na Pillars zai gurfana a gaban wani kwamatin ladaftarwa don ya kare kansa kafin a sake mayar da shi cikinta.

Gwamnatin Kano ta naɗa Yahaya Surajo - ɗan siyasa a Kano kuma tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafa - muƙamin a watan Agustan 2019, inda ya maye gurbin Tukur Babangida.

Pillars ba ta ƙoƙari a kakar bana ta 2021-22, inda a yanzu take mataki na 15 da maki 42 bayan buga wasa 34 a kakar.

A watan Afrilun da ya gabata ma hukumar shirya gasar Firimiyar Najeriya ta ci tarar Pillars naira miliyan tara tare da mayar da ita buga wasa a Abuja sakamon cin zarafin da magoya bayanta suka yi wa tawagar Katsina United.