Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
NPFL: Kano Pillars na cikin hadari
Gombe United ta yi nasara kan Remo Stars a gasar lig din kwararru ta Najeriya 1-0.
Hakan na nufin United ta kawo karshen gudun Remo Stars na wasanni 11 ba a doke ta ba.
Yahaya Ibrahim ne ya ci kwallon daya tilo a minti 15 da fara wasa, a filin wasa na Pantami da ke birnin Gombe.
Rashin nasarar hakama na nufin Remo Stars sun sauko daga na biyu zuwa na uku a teburi da maki 23, yayin da Rivers United da ta lallasa Wikki Tourists 3-0 ke ci gaba da zama a saman teburi da maki 25.
Plateau United ce ke binta da maki 24, bayan da ta doke Kano Pillars jiya a Kaduna.
Sunday Anthony ne ya ci wa Plateau United kwallon daya mai ban haushi a minti na 84, a filin wasa na Ahmadu Bello da ke Kadunar.
A sauran wasannin Sunshine Stars sun yi kunnen doki 1-1 da Nassarawa United, sai kuma Rangers da ta doke Abia Worriors 2-1 a wasan hamayya na 'Oriental derby' a Nnewi.
Shima mai tsaron ragar Heartland Femi Thomas ya taka rawa wurin hana masu rike da kofi wato Akwa United nasara a kan kungiyarsa, bayan da ya cire bugun fenareti har sau biyu da hakan yasa wasan ya tashi 0-0.
Ana zagaye na 12 ne na gasar firimiyar ta Najeriya, kuma tun kafin aje ko'ina manyan kungiyoyi na ci gaba da shan mamaki musamman Kano Pillars, wadda ke zaune na 14 a teburi.
Pillars ta hada maki 14 ne kacal a wasanni 12, inda ta ci wasa hudu aka kuma doke ta sau shida sannan ta yi canjaras biyu.
Kuma yanzu haka maki biyun ne kacal ya rabata da ukun karshe.