Ingila ta doke Najeriya a Kofin Duniya na Mata

Asalin hoton, Getty Images
Ingila ta fitar da Najeriya daga gasar cin Kofin Duniya ta Mata, bayan wasa ya kai ga bugun fenareti, inda aka tashi 4-2.
Yanzu dai Ingila ta tsallaka zuwa zagayen daf da kusa da na ƙarshe na gasar.
Tun farko, an tashi karawar babu ci tsakanin Najeriya da Ingila, kafin a ƙara lokaci, nan ma aka tashi kowacce ƙungiya tana nema.
‘Yan wasan Najeriya biyu ne suka ɓaras da bugun fenareti a cikin huɗu da suka buga, yayin da ƙungiyar Ingila ta ci ƙwallo huɗu.
'Yar wasan Ingila Georgia Stanway ce ta fara bugawa amma ta zubar da ƙwallon, wadda ta buga da ta faɗi.
Sai dai, 'yar wasan Najeriya Desire Oparanozie ita ma ta buga ƙwallon amma sai ta yi faɗi inda ta faɗa gefen raga.
Wasan dai ya yi zafi inda kusan kowanne ɓangare ya riƙa kai hare-hare, har ma ana iya cewa Najeriya ta fi kankane wasa a mafi yawan lokuta.
Wata ƙarin dama da Najeriya ta samu ita ce wadda aka kori wata 'yar wasan Ingila, Lauren James bayan an ba ta jan kati saboda ta taka 'yar Najeriya a gadon baya.
Cikin fushi Lauren ta taka bayan Michelle Alozie wadda ta faɗi ƙasa a minti na 87, bayan ƙwallo ta kuɓuce daga ƙafarta.

Asalin hoton, Getty Images
Da wannan nasara, Ingila za ta kara ko dai da ƙasar Colombia ko kuma ƙasar Jamaica a gaba.
A tsawon lokacin da aka ƙara Ingila ta buga wasan ne da 'yan wasa 10, yayin da 'yan wasan Najeriya suka yi ta matsa kora ba tare da sun yi nasarar jefa ƙwallo a raga ba.
Zakarun na Afirka karo 11 sun gudanar da salon wasansu da matuƙar ƙwarewa, inda suka riƙa tankwaɓe damar Ingila. Sun buga ƙwallon da ta doki turken raga har sau biyu.
Golar Najeriya Nnadozie ta ɓarke da kuka a gaban raga, inda ta rufe fuska da hannuwanta. Gwiwarta ta yi sanyi har ma sai da 'yan wasan Ingila suka taimaka suka tashe ta.
Super Falcons dai, sun mamaye wasan kuma sun riɓa turken raga har sau uku, amma dai nasara ba ta su ba ce.
Nan gaba a yau kuma Australia za ta kara da Denmark a filin wasa da ke birnin Sydney.











