Keira Walsh ka iya buga wasan Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Kocin tawagar kwallon mata ta Ingila, Sarina Wiegman, ta ce 'yar wasan tsakiya ta Keira Walsh za ta iya buga wasansu na zagaye na biyu a gasar Kofin Duniya da Najeriya ranar Litinin idan ta murmure sosai a ranar Lahadi.
Walsh, mai shekaru 26, ta ji rauni ne a gwiwarta a wasan da Ingila ta doke Denmark da ci 1-0 a ranar 28 ga watan Yuli, wanda Wiegman ta tabbatar da cewa ba mummunan rauni ba ne.
'Yar wasan tsakiyar ta Barcelona ta yi atisaye da sauran ‘yan tawagar a filin wasa na Central Coast kafin suka tashi zuwa Brisbane ranar Lahadi.
An yi fargabar cewa Walsh ta ji mummunan rauni a gwiwa, amma binciken da aka yi ya tabbatar da cewa lamarin bai yi munin da ake tunani ba.
An yi ta cece-kuce kafin wasan da Ingila ta yi da China game da yadda za ta maye gurbin Walsh, wadda ta kasance jigo a kungiyar da ta lashe gasar Euro 2022.
Wiegman ta canza salo, inda ta sanya 'yan wasa uku a baya, kuma ta hada Zelem a tsakiya.
Sauyin ya yi nasara amma kociyar ba ta yi wani karin bayani kan yadda Ingila za ta fuskanci wasa da Najeriya ba.
Shi kuma a nasa bangaren, kocin Najeriya Randy Waldrum ya ce dole ne kungiyarsa ta shirya tsaf domin tunkarar kowanne irin salo Ingila za ta bullo da shi, wanda hakan a cewarsa kalubale ne a gare shi.











