'Yan wasan da suka ci kwallo a ranar farko a sabbin kungiyoyinsu

Asalin hoton, Getty Images
A kakar bana kungiyoyi da dama sun sayi sabbin 'yan wasa don tunkarar kakar da za a fara daga makon farko a cikin watan Agusta.
Kawo yanzu wasu 'yan wasa hudu da aka saya a bana sun zura kwallo a wasan farko a sabuwar kungiyar da ta dauke su.
Cikinsu sun hada da Sadio Mane daga Liverpool da ya koma Bayern Munich da Matthis de Ligt daga Juventus.
Sauran sun hada da Gabriel Jesus daga Manchester City zuwa Arsenal da kuma Raphinha daga Leeds United da ya koma Barcelona.
Sadio Mane da Matthijs de Ligt dukkansu sun ci kwallo a wasan da Bayern Munich ta casa DC United da ci 6-2 ranar Laraba, duk da ta sayar da Robert Lewandowski ga Barcelona.
Shi kuwa Jesus ya buga wasan da Arsenal ta ci Nurnberg 5-3, inda tsohon dan wasan Manchester City ya ci kwallo daf da za a tashi yana da hannu daga hudun da aka zura a raga.
Shi kuwa Raphinha ya nuna da gaske yake a bana, bayan da ya ci kwallo ya kuma bayar da biyu aka zura a raga a wasan farko da ya yi wa Barcelona ranar Juma'a
Barcelona ce ta yi nasarar lallasa Inter Miami da ci 6-0.

Asalin hoton, Getty Images
Matthijs de Ligt da ya koma Bayern Munich
Bayern Munich ta kammala daukar mai tsaron baya, Matthijs de Ligt daga Juventus.
Dan kwallon tawagar Netherlands, ya amince da kunshin kwantiragin da zai kare ranar 30 ga watan Yunin 2027.
Dan wasan wanda an yi ta alakanta shi da cewar zai koma Manchester United ko Barcelona ko kuma Paris-St Germain da taka leda.
Ya fara taka leda a 2016 ya kuma lashe Eredivisie da Dutch Cup ya kuma buga wasan karshe a Europa League a 2017.
De Ligt ya ci kwallo takwas a wasa 77 a Ajax, kungiyar da ya koma taka leda yana da shekara tara, kuma ya zama matashin kyaftin din kungiyar a Maris din 2018.
Shi ne ya ci kwallon da Ajax ta doke Juventus ta kai wasan daf da karshe a Champions League, inda ta yi rashin nasara a hannun Tottenham.

Asalin hoton, Getty Images
Sadio Mane daga Liverpool da ya koma Bayern Munich
Sadio Mane ya kammala komawa Bayern Munich kan fam miliyan 35 daga Liverpool kan kwantiragin kaka uku.
Liverpool ta karbi fam miliyan 27.4 da karin yuro miliyan shida kan yawan buga wasanni da karin yuro miliyan uku kan rawar da zai taka da nasarorin da Bayern za ta samu.
Tun farko Liverpool ba ta sallama tayi biyu da Bayern ta yi wa Sadio Mane ba, dan kwallon tawagar Senegal, wanda yarjejeniyarsa zai kare a Anfield a karshen kakar da za mu shiga.
Mane ya koma Liverpool kan fam miliyan 34 daga Southampton a Yunin 2016, ya kuma ci wa kungiyar Anfield kwallo 120 a wasa 269, wanda a kakar da aka kare ya zura 23 a raga a dukkan fafatawar da ya yi mata.
Dan kwallon tawagar Senegal ya taimaka da Liverpool ta lashe Champions League da Premier League, shi ne ya ci fenaritin da Senegal ta lashe kofin Afirka a karon farko a Fabrairu a Kamaru.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Gabriel Jesus daga Man City zuwa Arsenal
Arsenal ta kamma sayen dan wasan tawagar Brazil, Gabriel Jesus, daga Manchester City kan fam miliyan 45, bisa yarjejeniya mai tsawo.
Dan wasan, mai shekara 25, ya zama na hudu da Mikel Arteta ya dauka a bana, bayan Fabio Vieira da Matt Turner da dan wasan Brazil, Marquinhos.
Arteta, wanda ya yi aiki tare da Jesus a lokacin da ya yi mataimin Pep Guardiola a Manchester City na kokarin daukar mai cin kwallaye, bayan da Alexandre Lacazette da Pierre-Emerick Aubameyang suka bar kungiyar.
Jesus, wanda ya karbi riga mai lamba tara a Gunners ya bar City, bayan kaka biyar da rabi da ya yi a Etihad.
Ya yi wasa 236 da cin kwallo 95 da lashe Premier League hudu da League Cup uku da FA Cup.
City wadda ta dauki Premier League a kakar da ta wuce ta sayar da Jesus ne, bayan da ta sayo dan kwallon Norway, Erling Haaland daga Borussia Dortmund kan fam miliyan 51.2 a watan Yuni.
Jesus ya bayar da kwallo takwas aka zura a raga a Manchester City a kakar 2021-22, wanda ya yi kan-kan-kan da Kevin de Bruyne a wannan bajintar.

Asalin hoton, Getty Images
Raphinha daga Leeds United zuwa Barcelona
Barcelona ta sayi dan wasan gaba na Brazil Raphinha daga Leeds United a kan farashin da ya kai fam miliyan 55.
Raphinha, wanda ya koma Leeds daga kungiyar kasar Faransa Rennes a kan fam miliyan 17 a 2020, ya murza leda sau 65 a Gasar Firimiya a kungiyar ta Yorkshire club, inda ya ci kwallo 17 sannan ya taimaka aka ci 12.
Leeds United ta yaba wa Raphinha a sanarwar da kungiyar ta fitar yayin da take tabbatar da rabuwa da dan wasan
Raphinha ya ci fenaretin da Leeds ta yi nasara da ci 2-1 a karawarsu da Brentford a ranar karshe a kakar wasa ta 2021/22 lamarin da ya sa suka samu gurbi a Premier League.











