Nottingham Forest na daf da daukar Jesse Lingard

Jesse Lingard

Asalin hoton, Getty Images

Tsohon dan kwallon Manchester United, Jesse Lingard na daf da komawa Nottingham Forest, bayan da yarjejeniyarsa ta kare a karshen kakar da ta wuce.

Mai shekara 29, wanda ya buga wa Ingila wasa 32 ana ta alakanta shi da sabuwar kungiyar da za ta fara buga Premier League a bana, amma ba a kai ga cimma yarjejeniya ba.

Ya bar United, bayan shekara 20 a Old Trafford, bayan da kwantiraginsa ya kare a karshen watan Yuni.

Ana kuma alakanta Lingard da cewar zai koma West Ham.

Ya buga wa West Ham United wasannin aro a 2020-21, ya kuma taka rawar gani da cin kwallo tara a wasa a gasar Premier League.

Lingard, wanda ya tattauna da Everton, ya yi wasa 22 a Manchester United a kakar da ta wuce, sai dai wasa hudu ciki ne aka fara da shi a cikin fili.