Waiwaye: Suɓul-da-bakan Tinubu, rikicin jam'iyyar NNPP da wanke Babachir Lawal

Ga wasu muhimman abubuwan da suka faru a wannan makon a Najeriya daga ranar Lahadi 13 ga watan Nuwamba zuwa Asabar 19 ga wata

Suɓul-da-bakan Tinubu ya haifar da ce-ce-ku-ce a Najeriya

APC

Asalin hoton, APC

Bayanan hoto, Gangamin yakin neman zaben 2023 n jam'iyyar APC

'Yan Najeriya sun shafe kwanakin makon da ya gabata suna ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta dangane da wasu kalamai ko suɓul-da-baka da ɗan takarar shugabancin ƙasar na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya yi a wurin yaƙin neman zaɓensa.

A ranar Talata ne Bola Tinubu ya ƙaddamar da gangamin yaƙin neman zaɓen nasa a Jos, babban birnin jihar Filato, wanda Shugaba Muhammadu Buhari da sauran jiga-jigan jam'iyyar suka halarta. 

Sai dai a jawabinsa lokacin da ya hau dandamali ya yi wasu kalamai da wasu ke gani subul-da-baka ne.

Akwai kuskure da Bola Ahmed Tinubu ya yi wajen kiran sunan jam’iyyarsa ta APC, inda aka jiyo ɗan takarar na ambato harufa biyu na babbar jam'iyyar adawa wato PDP, inda ya ce "PD..." amma daga bisani ya gyara ya ce "APC".

Wannan kuskure ko suɓul-da-baka da Tinubu ya yi ya ja hankali sosai, inda mutane suka yanko daidai wajen suna ta sake wallafawa da takfa muhawara a kai.

Rikici ya dabaibaye jam’iyyar NNPP a wasu jihohin arewacin Najeriya

Kwankwaso

Asalin hoton, others

Bayanan hoto, Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso

Rikicin cikin gida na ci gaba da turnuƙewa a rassan jam’iyyar New Nigeria Peoples Party NNPP, na wasu jihohin arewa maso yammacin Najeriya.

Hakan na zuwa ne yayin da babban zaɓen ƙasar na shekara ta 2023 ke ci gaba da matsowa.

Rikicin da ya turnuƙe jam'iyyar ta NNPP a Sokoto ya yi sanadin korar wasu jiga-jiganta, ciki har da shugaban jam'iyyar na jiha da kuma mataimakin ɗan takarar gwamna.

Dan jaridar Zamfara ya ci babbar kyauta ta duniya

.

Asalin hoton, SHEIKH GUMI

Bayanan hoto, Jihar Zamfara na fama da matsalar brayin daji

Wani dan Najeriya, Yusuf Anka ya ci babbar kyauta ta duniya da ake bai wa ‘yan jarida masu zaman kansu da ake kira Rory Peck Awards.

Ya samu kyautar ne saboda labarinsa da ya yi wa sashen binciken ƙwaƙwaf na BBC Africa Eye kan ‘yan bindiga da ke fashi tare da kashe mutane a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya.

A tattaunawarsa da BBC bayan kammala bikin karɓar kyautar, wanda ya gudana a daren Laraba 17 ga watan Nuwamba 2022, a birnin London, gwarzon ɗan jaridar ya ce hakan ba komai ya nuna ba illa cewa matsalara jihar Zamfara, aba ce mai muhimmanci ba ga jihar ko Najeriya kaɗai ba, har ma ga duniya baki ɗaya.

Kotu ta wanke Babachir Lawal daga zargin badaƙalar cin hanci

Babachir Lawal

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta wanke tsohon sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya, Babachir Lawal da wasu mutum biyar daga zargin wata badaƙala ta kuɗi naira miliyan 544.

Hukumar yaƙi da cin hanci da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa ta Najeriya, EFCC ce ta gurfanar da mutanen, tana zargin su da almundahana kan wata kwangilar cire ciyawa, wadda kuɗinta ya kai naira miliyan 544.

To sai dai hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta bayyana cewa za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotu da ya wanke kuma ya sallamin tsohon Sakatare Gwamnatin Tarayya Babachir Lawal daga zargin satar kuɗin sare ciyawa.

Bankin raya Najeriya na nuna wa Arewacin kasar wariya wajen bayar da rancen kudade - Ndume

Sanata Ali Ndume

Asalin hoton, others

Majalisar Dattawan Najeriya ta ce za ta gudanar da bincike a kan zargin cewa Bankin Raya Kasa, wato Nigeria Development Bank yana nuna wariya ga arewacin kasar wajen ba da rancen bunƙasa ƙanana da manyan masana`antu.

A muhawarar da ta gudanar kan batun ranar Laraba, Majalisar ta kafa wani kwamiti na musamman domin gudanar da bincike kan lamarin.

Dan majalisar dattawan kasar daga jihar Borno, Sanata Mohammed Ali Ndume ne ya gabatar da ƙudurin, wanda kuma ya ce daga cikin kusan naira miliyan dubu ɗari biyar da bankin ya raba, kashi goma sha ɗaya kacal ya bai wa jihohin arewa.