Dan jaridar Zamfara ya ci kyautar duniya

Hoton Bello Turji

Asalin hoton, SHEIKH GUMI

Bayanan hoto, Dan jaridar ya jagoranci hada rahoto ne a kan 'yan barayin daji a jihar Zamfara

Wani dan Najeriya, Yusuf Anka ya ci babbar kyauta ta duniya da ake bai wa ‘yan jarida masu zaman kansu da ake kira Rory Peck Awards.

Ya samu kyautar ne saboda labarinsa da ya yi wa sashin binciken kwakwaf na BBC Africa Eye kan ‘yan bindiga da ke fashi tare da kashe mutane a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya.

A tattaunawarsa da BBC bayan kammala bikin karbar kyautar, wanda ya gudana a daren Laraba 17 ga watan nan na Nuwamba 2022, a birnin London, gwarzon ya ce, hakan ba komai ya nuna ba illa cewa matsalar ta jihar Zamfara, aba ce mai muhimmanci ba ga jihar ba ko Najeriya kadai, har ma ga duniya gaba daya.

Yusuf, wanda matashin dan jarida ne ya ce, rahoton da ya kai shi ga samun wannan matsayi abu ne da ya shafi rayuwar mutane – ilimi da matsaloli na cin hanci da rashawa da talauci da kuma matsalar sauyin yanayi.

Ya kara da cewa, ‘’ wannan matsala ce mai girma da mutane da yawa suka damu da ita wadda kuma da dama za su so ganin karshenta.’’

Dan jaridar ya ce yana matukar godiya da wannan nasara da ya samu; ‘’Gaskiya ba karamin abu ba ne in ga ma cewa akwai ‘yan jaridar da suka yi kusan shekara 20, 30 suna aikin jarida,’’

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

‘’Wani Zuwanshi na daya na biyu na uku, akwai wanda har zuwanshi na hudu bai taba ci ba, amma Allah Yas a ni zuwana na farko kuma Yas a na samu nasarar lashe wannan’’ in ji shi.

Idan dai za a iya tunawa Yusufu Anka ya jagoranci tawagar BBC mai binciken kwakwaf, inda suka shiga dazukan jihar Zamfara inda ya tattauna da gaggan barayin daji da ke satar mutane domin karbar kudin fansa da kuma satar dabbobi hadi da hallaka jama’a.

Wannan dai matsala ce da ta addabi jihohin Najeriya da dama musamman na yankin arewa maso yamma; galibi ita jihar Zamfara da Sokoto da Katsina.

Matsalar tsaron ta addabi al’ummar Najeriya musamman wannan yankin abin da kusan ya hana manoma aikin gona da kiwo da gudanar da harkokinsu na rayuwa, duk da irin matakan da gwamnatin kasar da ta jihohin ke cewa suna dauka.

A baya-bayan nan dakarun kasar na cewa suna samun nasarar kawar da wadannan barayin daji inda suke hallaka wasu manyansu.

Daga irin matakan da hukumomin kasar ke dauka na ganin bayan ‘yan bindigar ne rundunar tsaron Najeriya ta fitar da sunayen mutum 19 waɗanda ta ce ƴan ta’adda ne a ƙasar kuma tana neman su ruwa-a-jallo

A sanarwar da ta fitar ranar Litinin 14 ga watan nan na Nuwamba 2022, rundunar ta ce mutanen sun daɗe suna tafka ɓarna a arewa maso gabas, da arewa maso yamma da kuma arewa maso tsakiyar ƙasar ta Najeriya.

Ta kuma ce duk wanda ya bayar da bayanin da ya taimaka wajen kama kowanne daga cikin mutanen za a ba shi tukwicin naira miliyan 5.

Sunayen mutanen, kamar yadda daraktan yaɗa labaru na cibiyar tsaron na Najeriya Manjo Janar Jimmy Akpor ya fitar su ne:

· SANI DANGOTE – Dumbarum, ƙaramar hukumar Zurmi, jihar Zamfara.

· BELLO TURJI GUDDA – Fakai, jihar Zamfara.

· ALHAJI ADO ALIERO – Yankuzo, ƙaramar hukumar Tsafe, jihar Zamfara.

· MONORE – Ƴantumaki, ƙaramar hukumar Danmusa, jihar Katsina.

· LEKO – Mozoji, ƙaramar hukumar Matazu, jihar Katsina.

· DOGO NAHALI – Ƴar tsamiyar jino, ƙaramar hukumar Ƙanƙara, jihar Katsina.

· ISIYA KWASHEN GARWA – Kamfanin Daudawa, ƙaramar hukumar Faskari, jihar Katsina.

· GWASKA DANKARAMI – Shamushele, ƙaramar hukumar Zurmi, jihar Zamfara.

· HALILU SUBUBU – Sububu, ƙaramar hukumar Maradun, jihar Zamfara.

· NASANDA – Kwashabawa, ƙaramar hukumar Zurmi, jihar Zamara.

· ALI KACHALLA, wato ALI KAWAJE – Kuyambana, Dansadau, ƙaramar hukumar Maru, jihar Zamfara.

· BALERI – Ƙaramar hukumar Shinkafi, jihar Zamfara.

· NAGONA – Angwan Galadima, ƙaramar hukumar Isa, jihar Sokoto.

· ABU RADDE – Varanda, ƙaramar hukumar Batsari, jihar Katsina.

· DAN-DA – Varanda, ƙaramar hukumar Batsari, jihar Katsina.

· MAMUDU TAINANGE – Varanda, ƙaramar hukumar Batsari, jihar Katsina.

· SANI GURGU – Varanda, ƙaramar hukumar Batsari, jihar Katsina.

· UMARU DAN NIGERIA – Rafi, ƙaramar hukumar Gusau, jihar Zamfara.

· NAGALA – Ƙaramar hukumar Maru, jihar Zamfara.