Wasu zaɓaɓɓun hotunan Afirka na mako da na 'yan nahiyar a wasu sassan duniya
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Sun yi fice game da soyayyar da suke yi wa tsarin kwalliyarsu. Mutanen Jamhuriyar Dimokraoyyar Congo da suka yi fareti a Kinshasa babban birnin ƙasar a ranar Juma'a...
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Sun taru a maƙabarta domin bikin tunawa da mutuwar fitaccen mawaƙin nan Stevos Niarcos karo na 18 a tarihi....
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Mutanen da ake kira da sapeurs mutane ne da suka yi fice wajen gudanar da abubuwansu na al'ada
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Suna yin komai domin tabbatar da cewa tsarin adonsu ya isa zuwa ga 'ya'ya da jikokinsu.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Yayin da a ranar masoya ta duniya da ake kira Valentine mawaƙiyar Kenya Shariffa Wambui ta yi casu a dandalin Kibera da ke Nairobi babban birnin ƙasar.
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Haka kuma a ranar wasu Misirawa ke bikin murnan zagayowar ranar da aka haifi jikar Annabi Muhammad, Zainab a wajen wani masallaci a birnin alƙahira.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, A ranar Litinin, masu makoki sun yi bankwana da mawakin nan na Afrika ta Kudu da aka kashe wanda ake kira AKA a yankin Durban na kusa da teku.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Yayin da ake yanayin farin ciki a Cape Town a ranar Juma'a, wata matashiya ta gabatar da wasa a yayin bikin buɗe wasan kofin duniya na kurket na mata, wanda aka fara da wasa tsakanin Afrika ta Kudu da Sri Lanka.
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, A washegari 'yar wasan Kenya Sabrina Simader na wasan sululu a gasar cin kofin duniya da ke gudana a Faransa.
Asalin hoton, EPA
Bayanan hoto, Yayin da aka samu ambaliya sakamakon ruwa kamar da bakin kwarya a Mozambique, a ranar Asabar ana kwaso mutane daga yankin da abin ya shafa - wasu sun maƙale a tsibiri wasu kuma kan rufin kwanon gidaje.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Wani matashi a yankin Somali na Habasha ya kai jakinsa rafi domin ɗebo ruwa a duro.