'Ƴan siyasa na mantawa da mata idan sun samu gwamnati'

Mata

Asalin hoton, Getty Images

Mata a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya, sun koka da yadda ake mantawa da su bayan ‘yan siyasa sun samu gwamnati duk da fitowar da suke kwansu da kwarkwata wajen kada kuri’a a yayin zabe.

Wannan koke na matan na zuwa ne a daidai lokacin da ake dab da gudanar da zabukan kasar na 2023.

Wannan matsala ta rashin damawa da mata a siyasa abu ne da ya dade yana ciwa wasu mata tuwo a kwarya ganin yadda suka ce ana watsi da su a lokacin da siyasa ta yi dadi. 

Matan na cewa watakila hakan baya rasa nasaba da rashin ba su cikakkiyar dama kamar takwarorinsu maza da ke mamaye fannoni daban-daban a gwamnati.

Hajiya Rabi Marafa, daya ce daga cikin matan da suke wannan korafe, ta shaida wa BBC cewa, kwalliya ba ta biyan kudin sabulu ganin yadda ake barin mata a baya. 

Ta ce,” Mata suna iya bakin kokarinsu, kuma sune ma a takaice ginshikin zabe, amma ana kallon abubuwa ana yi amma bad ai aga mat aba idan an ci zabe.”

Hajiya Rabi, ta ci gaba da cewa dakile mata ake yi ba a ba su damar fitowa a goga da su a wajen Takara.

Ta bayyana cewa wasu matsalolin da matan ke fuskanta a bangaren siyasa na da nasaba da al'ada da kuma addini. 

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ita ma Hajiya Rabi Saulawa, ta shaida wa BBC cewa, rashin bai wa mata dama ya sa aka samu koma-baya wajen magance matsalolin da ke addabarsu kamar yadda Hausawa suka ce 'ciwon ya mace na mace ne'.

Ta ce, “ Ba a bawa mata dama ne ballantana aga irin mulkin da za su yi”.

To sai dai wasu matan na ganin laifin ba na maza ba ne illa su kansu matan kasancewar wai sai bango ya tsage kadangare kan samu hanya kamar yadda Binta Muhammad Nasir wata mai sharhi kan al'amuran yau da kullum a jihar Katsina ta shaida wa BBC.

Ta ce,” Babbar matsalar um matan jihar Katsina ita ce, koda sun fito takara, sai kaji daga baya sun janye, ban san me suke ji ko suke tsoro ba, ita siyace aba ce da sai na jajirce an tsaya tsayin daka kafin ace an san da kai ko na tafi da kai kamar yadda yakamata.”

Hauwa Hamisu Musa Mashi, matashiya ce kuma a cewarta, duk da cewa matsalar rashin damawa da mata a siyasa na nan, amma a ganinta an dan samu sauyi.

Ta ce,” A yanzu akwai wayewa da shigo da mata lamuran siyasa, ina ganin kamar yanzu na dan samu ci gaba wajen damawa da mata.”

Kazalika mata a jihar ta Katsina, na sake kokawa a kan wata matsalar da matan ke fuskanta wato yadda ake bin mata ana saye kuri’unsu, ta yadda ranar zabe ma ba sa ganin kuri’unsu Sai dai kawai su ji an sanar da wanda aka ce shi ne ya yi nasara.

Hajiya Binta Muhammad, ta shaida wa BBC cewa, su fa ‘yan siyasa da zarar ranar zabe ta wuce ba a kara ganinsu sai bayan shekara hudu, sannan shi kansa sayen kuri’un cin hanci da rashawa ne.

Itama Hajiya Rabi Saulawa, cewa ta yi kuri’arka ‘yancinka, don haka duk mace da ta kuskura ta sayar da katinta na zabe to ta sayar ‘yancinta har abada.

Kungiyoyi da dama dai a Najeriya na ta kiraye-kirayen a rika ba wa mata dama a siyasa kasancewar alkaluma na nuna cewa su ne sama da kashi 49 cikin 100 na al'ummar Najeriya, baya ga irin gagarumin gudunmuwar da suke bayarwa wajen zaben shugabanni a kasar.