Me yake janyo saurin balaga kuma me ya sa yake da haɗari ga yara?

Balaga.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Menstruation usually begins in adolescence in girls and continues for decades.
    • Marubuci, Deepali Jagtap, Sushila Singh
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilan BBC
  • Lokacin karatu: Minti 4

Archana, mahaifiyar wata yarinya mai shekara shida, ta lura da wasu sauye-sauye a jikin ƴarta wanda ba ta saba gani ba, abin da ya saka mata damuwa.

"Na ji tsoro saboda waɗannan abubuwa na fitowa a jikinta a shekaru ƙanƙanta, kuma ta fara nuna fushi kan waɗannan abubuwa da ba su da muhimmanci sosai, su ne suka sa min shakku," in ji ta.

Archana, wanda ba sunanta na asali ba, tana zaune a ƴan uwanta a lardin Satara da ke yammacin Indiya. Tana zaune ne tare da mijinta da kuma ƴaƴanta biyu - namiji da mace - a wani ɗan ƙaramin gida kusa da wata gona. Ta yanke shawarar ganin likita kan batun ƴarta, wanda yanayinta ya fi na shekarunta.

Ƴan makaranta a Indiya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Batun ƴan mata da ke saurin balaga na ƙaruwa a Indiya a baya-bayan nan

"Mun kasa amincewa"

Ita ma wata mata da ke zaune a birnin Delhi, Rashi, ta ce ta lura da sabbin sauye-sauye a jikinta ƴarta, sai dai ta ɗauke su a matsayin abubuwa da aka saba gani.

Ƴarta mai shekara shida tana da kilogiram 40, sai dai ta ɗauki hakan a matsayin cewa ƴarta ta na da "isasshen lafiya," har sai da watarana ta fara zub da jini. Lokacin da suka je ganin likita, alamu sun nuna cewa tana fama da jinin al'adar.

"Abu ne mawuyaci mu amince da abin da ke faruwa, kuma ƴata ta kasa fahimtar abin da ke faruwa da ita," in ji Rashi.

Lokacin da Archana Pantha ta je gurin wani likita a ƙauyensu, ya shawarceta da ta je wurin likitan da ya ƙware kan al'amuran mata.

"Lokacin da Archana ta kawo mana ƴarta, mun duba ta sannan muka gano cewa tana ɗauke da alamun balaga. Jikinta ya yi kamar na mai ƴar shekara 14-15 kuma za ta iya fara al'ada a kowane lokaci," in ji Sushil Garud, wani likita a wani asibiti a birnin Pune da ke jihar Maharashtra.

Indiya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Alamun balaga sun fara bayyana wajen ƴar Achana lokacin da take shekara shida
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Garud ta ƙara da cewa ƙwayoyin jikin yarinyar sun fi karfin shekarunta, kuma akwai dalilan da suka sa hakan ya faru.

"Arkana ta faɗamin cewa tana adana maganin feshi mai nauyin kilogram biyar a gidanta kuma a wurin da yarinyar ke zaune," in ji likitan, inda ya ce "wannan ne dalilin da ya sa yarinyar ta samu sauye-sauye a jikinta."

Balaga dai wani yanayi ne da sauye-sauye ke faruwa a jikin maza da mata, inda yawanci al'aurarsu ke girma ta kai wani mataki.

Har ila yau, murya tana sauyawa a wannan lokaci sannan gashi na fitowa a gaban maza da kuma mata. Ga ƴan mata mamarsu na ƙara girma a lokacin balaga, sai kuma su fara yin al'ada.

Balaga na farawa ne daga shekaru 8 zuwa 13 ga ƴan mata - yayin da maza kuma daga 9 zuwa 14.

Wata likitar yara, Vaishakhi Rustagi, ta faɗa wa BBC cewa ta ga sauye-sauye a jikin ƴaƴa mata da yawa a shekarun da suka wuce.

Ta ƙara da cewa: "Mun saba ganin al'ada tana farawa ne watanni 18 zuwa shekara uku bayan fara ganin alamu na sauye-sauye a jiki, sai dai a yanzu ya ragu zuwa watanni uku zuwa huɗu."

Ta lura cewa maza na fitar da gemu da gashin baki yanzu shekara ɗaya da rabi bayan balaga, idan aka kwatanta da shekara hudu a baya.

Indiya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Balaga na farawa ne tsakanin shekara 8 zuwa 13 ga ƴan mata sannan shekara 9 zuwa 14 ga maza

Wani bincike da wata cibiyar kula da ingancin haihuwa ta yi kan ƴan mata 2,000, ya gano cewa iyaye mata ba su cika gane alamun balaga ba.

"Ƴan mata 60 waɗanda ke tsakanin shekara shida zuwa tara sun nuna alamun saurin balaga, kuma wasunsu za su iya fara al'adarsu a kowane lokaci," a cewar Sudha Rao - wata likita daga sashen kula yara a wani asibiti a Delhi.

Me yake janyo saurin balaga?

Likitoci sun ce akwai dalilai da yawa da ke janyo saurin balaga, babu guda ɗaya wanda aka hakikance a kasa saboda har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike.

Wasu sun bayyana cewa maganin ƙwari, gurɓatar muhalli da kuma ƙiba na cikin dalilan da ke janyo saurin balaga.

Prashant Patel, wanda ya yi duba kan wannan batu tsakanin ƴan mata a birnin Mumbai, ya ce ƙiba shi ne babban abin da ke janyo balaga da wuri, kuma lamarin ya yi muni ne sakamakon ƙaruwar masu ƙiba tsakanin ƙananan yara lokacin annobar korona.

A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, sama da ƙananan yara miliyan 390 da kuma waɗanda suka balaga tsakanin shekara 5-19 suna da ƙiba a 2022, ciki har da masu ƙibar da ta wuce ƙima su miliyan 160.

Yawan amfani da wayoyin salula da talabijin da kuma sauran kayan kallo, da rashin motsa jiki - su ma suna iya janyo balaga da wuri.

Vaishakhi ta ce a tsawon shekara biyu zuwa uku da suka wuce, asibitin da take aiki na samun mutum biyar zuwa shida kan batun jinin al'ada a kowace rana.

Ta ƙara da cewa, "Akwai iyaye mata waɗanda suka ce sun ga sauye-sauye a jikin ƴaƴansu mata a watan Afrilun da ya wuce, sannan ƴan matan suka fara al'ada daga watan Yuni zuwa Yuli. Yanzu, ana fuskantar irin haka a wajen maza ma."

Ta ce lokaci da yara ke shafe wa a gaban abubuwna kallo, shi ma yana shafarsu wajen saurin balaga.

A yanzu ƴaƴan Archana da Rashi na samun kulawa domin dakatar da al'adarsu har sai sun kai aƙalla shekara 10 zuwa 11.

Likitoci sun ce ƴan mata da ke irin shekarunsu ba su kai matakin kula da kansu ba, har ma su tsaftace jikinsu lokacin al'ada.

Likitocin sun ƙara da cewa ƴan mata waɗanda ke fuskantar saurin balaga - za su iya fuskantar matsalolin tunani da na zamantakewa.

Bincike sun nuna cewa ƴan matan da ke yin saurin balaga, za su iya fuskantar tsangwama daga takwarorinsu saboda saurin sauye-sauye da suke samu a jikinsu.