Yadda ƙarin kuɗin man fetur zai shafi hauhawar farashin kaya a Najeriya

Lokacin karatu: Minti 4

Tun bayan da kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL, ya sanar da matakin ƙarin farashin man fetur, ƴan ƙasar da dama ke ci gaba da bayyana fargabarsu kan ƙaruwar farashin kayyan masarufi a ƙasar.

Dama dai ƴan Najeriya na cikin halin matsin rayuwa da hauhawar farashin kayan masarufi, lamarin da masana da dama suka alaƙanta da cire tallafin man fetur da gwamnatin Bola Tinubu ta yi a ranar farko da ta karɓi mulki a watan Mayun 2023.

Tashin farashin kaya da matsin tattalin arziƙi ya kai ga cewa wasu al'ummar ƙasar suka gudanar da zanga-zanga a farkon watan Agusta.

To sai dai masanan sun yi hasashen cewa sabon ƙarin kuɗin zai haifar da ƙaruwar farashin kayya a kasuwannin ƙasar.

Haka su ma a nasu ɓangaren ƴan kasuwa a Najeriyar sun koka game da matakin, inda suka ce lamarin zai iya dagula yanayin farashin kaya.

A makon da ya gabata ne hukumar kare haƙƙin masu amfani da kayan masarufi a ƙasar ta bai wa ƴan kasuwar ƙasar wa'adin mako biyu su rage farashin kayyaki ko ta ɗauki mataki a kansu.

To sai dai ƴan kasuwar sun ce idan aka kwatanta matakin ƙarin kuɗin man fetur da kuma umarnin hukumar kare haƙƙin mai saye, batun tamkar tufka da warwara gwamnatin ƙasar ke yi ke yi.

'Ƴankasuwa na cikin tsaka-mai-wuya'

Shugaban ƙungiyar ƴan kasuwar Singa da ke Kano, Barista Junaidu Muhammad Zakari ya ce ƴan kasuwa na cikin damuwa kan wannan mataki saboda su ne za a fi ɗora wa alhakin duk matsin da matakin zai haifar.

Ya ce idan aka yi la'akari da umarnin hukumar kare hakkin mai saye to wannan tufka da warware ne gwamnatin ke yi.

Ya ƙara da cewa a lokuta da dama manyan masana'antun da ke samar da kayyakin da kuma masu dakon kayyakin kan fake da ƙarin kuɗin man fetur ɗin wajen ƙara wa kaya kuɗi.

''Masana'antun da muke saro kaya da masu yi mana sufurin kaya kan fake da ƙarin kuɗin man fetur wajen haifar mana da ƙarin farashin kayyakin da muke sayarwa, wanda a ƙarshe kan masu saye abin ke ƙarewa,'' in ji shi.

Ya ce manoma na shan tsada wajen sayen kayan noma, da kuma kuɗin sufuri wajen kai kayayyakinsu kasuwanni, don haka dole a samu ƙarin farashin kayyaki a ƙasar.

To sai dai shugaban ƴan kasuwar ya kore zargin da wasu ke yi cewa ƴan kasuwa na fakewa da ƙarin kuɗin man fetur ɗin a wasu lokuta don tsawwala farashin kayyaki.

''Mu ba ma goyon baya kuma muna yaƙi da masu irin wannan ɗabi'a ta tsawwala wa jama'a'', in ji shi.

Tun dai bayan sanar da matakin ƙarin kuɗin man fetur, rahotonni suka ce an samu ƙarin kuɗin sufuri da na kayyakin masarufi a kasuwannin ƙasar, wani abu da talakawan ke kokawa a kai.

'Tsadar rayuwa za ta ƙaru'

Farfesa Muhammad Muttaƙa Usman, malami a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya ya ce galibi kayayyakin da ake sayar da su a kasuwanni jigilarsu ake yi a motocin da ke amfani da man fetur ko man dizel.

"To ke nan a duk lokacin da aka ƙara kuɗin man fetur, za a samu ƙarin kuɗin da ake kashewa wajen zirga-zirga, sannan masana'antu za su ƙara kuɗin abin da suke sarrafawa saboda ƙaruwar farashin man da suke amfani da su'', in ji shi.

''Idan kuma hakan ta faru to tabbas tsadar rayuwa za ta ƙaru, kuma mutanen da ke cikin ƙangin talauci za su ƙaru, rashin aikin yi zai ƙara yin sama'', in ji farfesa Muttaƙa.

Shi ma Dakta Bashir Achida na Jami'ar Usman Ɗanfodiyo da ke Sokoto ya ce dole ne a samu ƙarin farashin kayyaki, la'akari da sufurin kayyakin da ake yi a ababen hawa.

''Kuma ka sani idan mai sana'a ya samu ƙari a kan kayansa, to dole wannan ƙari zai ɗora shi ne a kan kayan da yake sayarwa'', in ji shi.

Dakta Achida ya kuma ce ƙarin kuɗin man fetur ɗin zai shafi sauran rayuwar mutane bayan ƙaruwar farashin.

''Zirga-zirgar da jama'a za su yi da kuma ƙaruwar tsadar ayyukansu na neman abinci, za su shafi rayuwar mutane ta ɓangarori da dama'', in ji masanain tallain arzikin.

''Bayan tsadar abinci za kuma a samu ƙaruwar tsadar ayyukan ƙwadago da jama'a ke gudanarwa

Farfesa Muttaƙa ya kuma ce matakin ƙarin kuɗin man fetur ya nuna cewa babu jituwa tsakanin ɓangarori ko hukumomin gwamnatin ƙasar, la'akari da umarnin hukumar kare hakkin mai saye na sassauta farashin kayayyaki.

Mafita

Farfesa Muttaƙa ya ce abin da ya kamata gwamnati ta yi shi ne ta san abin da take son cimmawa.

''Idan ka ƙara kuɗin mai, me kake son cimmawa? Idan dai kana son cimma rage wa mutane wahalhalu da yunwa da suke ciki a ƙasar, to a wannan lokacin bai kamata ka ɗauki wannan mataki ba, saboda zai ƙara kuɗin tafiye-tafiye, da sauran tsadar rayuwa a ƙasar'', in ji masanin tattalin arzikin.

Al'umar ƙasar da kungiyoyi da dama dai na sukar gwamnatin ƙasar kan wannan mataki ciki har da ƙungiyar ƙwadagon ƙasar wadda ta ce haka ba ya cikin sharuɗan da suka cimma da gwamnatin ƙasar kafin su amince da sabon albashi mafi ƙanƙanta na naira 70,000 da suka cimma da gwamnati.

A cikin watan Yuli ne dai gwamnatin ƙasar ta cimma yarjejeniya da NLC kan sabon albashi mafi ƙanƙanta na naira 70,000, kodayake har yanzu gwamnatin tarayya ba ta fara aiwatar da ƙarin albashin ba.