BBC ta bankaɗo likitan ƙara girman mazaunai da ke 'cutar da mata'

Ricky Sawyer, filmed undercover in his small pop-up clinic at a London office, sits next to a metal trolley wearing green uniform. He is a man in his 20s with straight brown hair, a moustache and beard.
Bayanan hoto, Hoton Ricky Sawyer da aka dauka a asirce a wurin da yake aiki a matsayin asibiti a birnin Landan
    • Marubuci, Shona Elliott and Ruth Clegg
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Investigations
  • Lokacin karatu: Minti 8

Wani sananne da ke yi wa mata kwaskwarimar ƙara kyau, wanda ya yi wa wasu fitattun mutane aiki, na gudanar da aiki mai hadarin gaske da bayar da magunguna ba bisa ƙa'ida ba - kamar yadda binciken BBC ta gano.

Ricky Sawyer ya yi fice wajen kara wa mata girman mazaunai - wanda ya hada da allurar dago duwawu saboda su kara girma.

BBC ta tattauna da wasu daga cikin mutane biyar da ya yi wa aiki, wadanda yanzu ke bukatar kulawar gaggawa a asibiti. Sannan mun tattaro bayanai daga mata sama da 30 da suka ce sun fuskanci yanayi masu hadari irin su lalurar sepsis da necrosis wadanda ke iya kisa.

Wata mata ta fada wa mana cewa a lokacin da ya yi mata aiki sai da ta gwammace mutuwa saboda tsananin azaba da ya biyo bayan aikin da ya yi mata.

Hukumomi da dama sun haramta wa Mista Sawyer gudanar da ayyukasa a yankunansu.

Bincikenmu na kwakwaf ya ga lokacin da Mista Sawyer ke bayar da magunguna da babu bayanai yadda za a sha a bisa ka'ida - wanda babban laifi ne. Ba shi da kwarewar bayar da magunguna ko bayanan yadda za a sha magunguna.

Ya kuma yi kokarin yin allurar kashe radadi na anaesthetic ba tare da tantance adadin ruwan allurar da zai yi amfani da shi ba - wanda hakan ya saba ka'ida - sannan bai tambayi nauyin wakiliyarmu ba, wanda hakan kokarin jefa ta ne cikin wani yanayi, idan maganin ya zarta yawan abin da jikinta zai iya dauka.

Wakiliyarmu ta je wurin likitan da tawagarta a matsayin kawaye, kuma sun nemi izinin ganinsa wanda aka ba su mintuna 45 na ganawa da Mista Sawyer ta shafinsa na Instagram. Mun fada masa cewa muna son ya ba mu mil 200 na allurar kara girman mazaunai wanda aka kiyasta a kan fam 1,200. Sai muka bayar da kudin kafin alkalami fam 200.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Duk da tallace-tallace cewa duk wata allurar karin girman mazaunai za a aiwatar ne bisa tsari da ka'ida ta kwararru, babu mutum ko guda a asibitinsa.

Yana aiki ne daga wani karamin daki a rukuni ginin ofisoshi da ke gabashin Landan. Wuri ne da bai dace da asibiti ba ko inda za a iya wannan aiki saboda barazanar cututtuka.

Cikin mintuna biyar da muka shafe a ofishinsa, Mista Sawyer ya soma kwadaita wa wakiliyarmu amfani da allurarta da shaida mata cewa za ta yi mamakin sauyin da za ta gani, kuma ba za a gane ba, a cewarsa.

Bayan ganawarmu, Mista Sawyer ya ce zai mana allurar da ta kai mil 500 a kowanne bangare na mazaunai - wanda ya kiyatsa kudin da za mu kashe kan fam 2,000.

Mun ki yarda da abin da ya ce, sai daga baya muka sake komawa domin tuhumarsa - amma sai ya ki amsa tambayoyinmu karshenta ma ya bankado mana kofa.

A lokacin da muke nuna bidiyon da muka nada, Dalvi Humzah wanda yake da kwarewa a tiyatar gyaran halitta, wanda kuma ke cikin kungiyar kwararru a wannan bangaren, ya ce ya yi mamaki da abin da ya ga Mista Sawyer na aikatawa, mai hadarin gaske, na jefa masu zuwa wurinsa cikin barazanar kamuwa da cututtuka ko ma rasa rayukansu.

Dalvi Humzah in his white clinical treatment room, holding a syringe and wearing a plastic apron and rubber gloves. In the background a sink, sharps bin and disinfectant dispensers - the kind of hygienic resources that are standard in a clinical setting.
Bayanan hoto, Dakta Dalvi Humzah

Allurar da yake amfani da su wajen aikin karin kara girman mazaunai na dauke da sinadarin hyaluronic acid, wanda ake amfani da shi wajen gyaran fuska. Amma sai ya kasance yana amfani da wannan sinadari mai yawan gaske wajen karin wajen nasa aikin na kara girman duwawu, kuma hakan na iya haifar da barazana sosai ko jini ya sandare ko kashe garkuwan jiki.

Mista Sawyer a bidiyon da muka nada yana tinkahon cewa a rana yana yi wa mutane kusan bakwai aiki, sau shida yake aiki a mako. Kuma yana samun dubban fama-famai idan zai gana da mutane.

Daya daga cikin matan da ta tsinci kanta cikin yanayi na azaba da matsaloli bayan ya yi mata aiki, mai suna Joanne, uwa ce mai yara biyu mazauniyar kudancin Wales, wadda ba ta son mu fadi cikakken sunanta, ta yi tafiyar sa'a bakwai domin a yi mata wannan allurar.

Ta ce da yake a baya an sha mata aiki da gyara na hallita, sai Ricky Sawyer ya ja hankalinta saboda irin tallace-tallacensa da kuma shahararrun mutanen da ke kai masa ziyara.

Burinta shi ne duwawunta ya dago sosai.

Amma da Joanne ta zo wurinsa, sai ta shiga tababa.

Joanne ta kamu da lalurar sepsis bayan Ricky Sawyer ya yi mata allurar ƙara girman mazaunai
Bayanan hoto, Joanne ta kamu da lalurar sepsis bayan Ricky Sawyer ya yi mata allurar ƙara girman mazaunai

Adireshin da aka aikata mata sai ta fahimci kawai inda ya kai ta rukunni gidaje ne ba wai wurin da ya yi kama da asibiti ba ne.

A karshe dai, ta iso bakin wata yar kofa ga kuma dakuna jere, sannan aka ce ta yi zaman jira a wani tsukakken wuri na tsawon mintuna 30.

"A lokacin ya kamata na juya na tsere," a cewarta, "amma na biya kudin kafin alkalami na fam 600, ga kuma nisan hanya."

An shigar da ita wani karamin daki, mai dauke da "gado daya da wata karamar kujera da riga a sagale," a nan ne ta fara haduwa da Ricky Sawyer.

A lokacin da ya fara yi mata allurar, sai ta ji duniya ta yi mata zafi saboda tsananin azabar da ta gaggara daurewa.

"Na soma jin jiri, sai zazzabi da makyarkyata. Kafafuna sun daina motsawa. Duk a cikin dakika guda da soma wannan allurar,"a cewarta. "Ina tuna lokacin da na iya dan dagowa na hango jini kaca-kaca a hannunsa,"

Lokacin da aka gama, Joanne ta shiga yanayi na bala'i: "Na shiga yanayi na radadin mai tsanani, mazaunaina sun fita hayyacinsu."

Ta ce ba ta iya zama baki daya. Tana isa gida abu ya sake muni, ta kumbura ko tafiya ba ta iyawa.

Ya kai ga cewa sai da Joanne ta nufi asibiti domin samun kulawa
Bayanan hoto, Ya kai ga cewa sai da Joanne ta nufi asibiti domin samun kulawa

"Na rinka aika wa Ricky sako domin yi masa bayanin yanayin da nake ciki na azaba da damuwar da na shiga. Amma sai ya ce mun kawai na cigaba da shan magungunan da ya bani."

A wannan lokaci garkuwan jikina ya yi rauni, na soma shiga yanayin da cututuka kawai ke sauko min.

"Jikina ya rinka tsananin zafi na tsinci kaina cikin bala'i," a cewar Joanne. " Nan take na kira 999. Ina ta gumi da ihu."

A asibiti, an sa mata magunguna taimaka wa numfashi. A wannan loakci, likitoci suka yi zane a duwawuna, inda suke shirin yankawa, saboda cutar ta shige ni kuma tana yaduwa cikin gaggawa.

Bayan aika sako zuwa ga Ricky Sawyer cewa ina asibiti saboda cutar da ake kira Sepsis, sai kawai ya toshe ta daga samunsa a shafin Instagram.

A karshe dai, Joanne ba a yi mata aiki ba, Allah ya taimake ta.

Akwai wata Louise Moller da ita kuma sai da aka shigar da ita sashen gaggawa domin ceto ranta.

Kwana hudu bayan yi mata allurai a asibitinsa da ke Essex a Oktoban 2023, sai da aka kwantar da matar mai shekara 28 a asibitin Bolton.

Ta kira mahaifiyarta, Janet a Salford tare da sanar da ita cewa "Mama, mutuwa zan yi."

Likitoci sun fada wa Louise cewa cuta ta shige ta don haka tana iya mutuwa a kowane lokaci. Domin hana yaduwar cutar a cikinta sai da aka yanke wani bangare na jikinta da kusan ya rufe mazaunanta baki daya.

Louise lokacin da take cikin farin ciki gabanin aikin ƙara girman mazaunai, amma in yanzu tana buƙatar sai an yi mata tiyata domin gyara aikin

Asalin hoton, Janet Taylor

Bayanan hoto, Louise lokacin da take cikin farin ciki gabanin aikin ƙara girman mazaunai, amma a yanzu tana buƙatar sai an yi mata tiyata domin gyara aikin

Janet ta yi wa diyarta alkawari cewa za ta kare ta da kuma sauran mutane daga shiga wannan ukuba, don haka sai ta kai karar Ricky Sawyer wajen 'yansanda a Bolton.

"Ya aka yi ya cigaba da wannan aika-aika duk da ya san cewa yana iya sanadin mutuwar wani?" kamar yadda ta shaida wa BBC.

Sai dai batun Louise ya tabbatar da wahalar da ke tattare da gurfanar da irin wadannan mutane.

Janet ta ce 'yansanda a Bolton sun fada mata cewa dole idan za ta shigar da kara ya biyo ta ofishin 'yansanda da ke Essex, inda abin ya faru.

Sai dai hukunta shi zai yi wahala, saboda Louise ta sanya hannu kan takardar amincewa da abin da za a yi mata, a cewarsu.

BBC ta tuntuɓi 'yansanda a Manchester da Essex domin samun bahasi - amma sai suka shaida cewa ana bincike kan batun.

Janet Taylor, with long blonde hair and blue eyes, wearing pearl earrings, sitting on the grey couch in her living room, looking straight at the camera

Ta fannin shari'a, ya kasance abu mai wahala a iya dakatar da Mista Sawyer.

Irin wannan allurar ana ganin kamar ba ta da alaka da tiyata kuma babu wata doka a kai, wanda hakan ke nufi kowa na iya yin ta.

A watan Satumban 2024, Alice Webb ta kasance mutum na farko da ake ganin ta rasa ranta sanadiyar wannan allurar a Birtaniya. Sai dai ba Ricky Sawyer ba ne ya yi mata allurar.

Bayan mutuwarta, kungiyoyin da ke fafutika suka hade kai wajen neman a tilasta ko haramta amfani da irin wadannan allurai in dai ba kwararru ne suka bayar da ita ko za su yi wa mutum ba a asibiti.

Kungiyar Save Face da shugabarta, Ashnton Collins, ta ce ta karbi korafe-korafe daga mata 39 kan Ricky Sawyer.

Dukkanin mata, a cewarta, sun fada mata ya bar su cikin yanayin da ya sa aka gaggauta ceto rayukansu a asibiti. Kowanne su, a cewarta, bayan allurar karin duwawun sun sha azaba da kusan sun yi tunanin mutuwa za su yi, haka kuma halittarsu ta sauya.

"Muna ba wa matan kwarin gwiwar shigar da kara gaban 'yansanda," a cewarta. Wasu sun yi, kuma babu abin da aka yi."

Ashton Collins, long blonde hair, a black top, white necklace, sits in her white office. Visible on the window is the logo of her organisation, Save Face.

Mun gabatar da korafinmu da shaidu a ma'aikatar kula da lafiya da walwala kuma ana nazartar lamain domin samar da matakai masu tsauri.

Sun ce sun yi mamakin bincikenmu, da yadda har ake samun irin wannan a cikin al'umma ba tare da shaidar kwarewa ba.

Mun yi kokarin gabatar da tuhumarsu kai tsaye ga Ricky Sawyer, a asibitinsa da ke gabashin Landan.

Amma yana ganin kyamara ya rufo mana kofa, sannan ya buya.

Mun tambaye shi cewa ko ya san yana karya doka ta hanyar bayar da magunguna da ba shi da kwarewa a kai, kuma me zai ce kan zarge-zargen da aka gabatar a kansa da wadannan mata da ya jikkata da ke bukatar taimako.

Sai ya amsa cewa da cewa ‘A'a’ - sanna ya umarci mu fice.

Hadarin irin wadannan gyaran jiki ko aiki abu ne da ya kamata ake dauka da muhimmanci, a cewar Ashton Collins.

"Abin da ake yawan ambata shi ne wadannan mata sun yi rashin tunani wajen wannan zabi da karshe ake karkarewa cikin hadari."

Dabi'a ce da dole a sauya ko kawo gyara, a cewarta: "Mutane na can suna jefa rayuwarsu cikin hadari, wasu kuma na amfani da damar wajen cin karensu babu babbaka, yanayi ne da ya zama tilas a kawo sauyi."