Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda likitoci suka gano ina ɗauke da juna-biyu a cikin hanta
"Na sha fama da amai babu ƙaƙƙautawa, kullum kuma ina yawan fama da gajiya da ciwo a jiki," in ji Sarvesh lokacin da take tattaunawa da BBC.
Matar mai shekara 35 a duniya ta ce ta daɗe tana fama jinya.
"Da wuya a fahimci abin da ke faruwa da ni," ta ƙara da cewa.
A farkon lokacin da ta je asibiti a Bulandshahr, Uttar Pradesh, hoton duba ciki bai nuna komai ba. Saboda haka, aka ci gaba da ba ta maganin ciwon ciki saboda ana tunanin wayoyin cuta ne ke damu a cikin ƴaƴan hanji.
Bayan ta shafe wata ɗaya tana shan magani ba tare da ta ga wani sauyi ba, sai ta sake komawa asibiti. Wannan karon abin da aka gani ya ba kowa mamaki, har likitocinta suka kasa gaskata hoton da ke gabansu.
Dr. KK Gupta, ƙwararren likitan duba ciki da ya shafe fiye da shekaru 20 a Meerut, da ke ƙasar Indiya, ya ce:
"Hoton duba ciki ya nuna cewa tana da ɗauke da juna biyu mai makonni 12 kuma jaririn na girma ne a gefen hantarta ba a cikin mahaifarta ba wanda ake kira da 'ectopic pregnancy' . Wannan shi ne karo na farko da na taɓa ganin irin wannan lamari a hoton MRI."
Ya ce ya ɗauki hotuna da dama don tabbatar da gaskiyar abin da ya gani.
Mijinta, Paramveer, ya bayyana cewa cikin da ake kira da 'ectopic pregnancy' wanda ba kasafai ake samun irin sa ba, ya zame musu babban ƙalubale ta fuskar tunani da kuma kashe kuɗi.
Girman ciki a wajen mahaifa 'ectopic' yana faruwa ne idan ƙwai ya haɗu da maniyyi amma ya maƙale a wani waje ba a cikin mahaifa ba, yawanci a bututun ɗaukar ƙwai zuwa mahaifa yake maƙalewa.
Ana samun irin haka a kimanin ɗaya cikin juna biyu 80 da mata ke samu, kuma a wasu lokuta zai iya zama haɗari ga rayuwar uwa.
A lamarin Sarvesh, maimakon jaririn ya girma a cikin mahaifa, sai ya fara girma a cikin hanta. Hanta na taka muhimmiyar rawa wajen tace guba daga jini da kula da yawan sukarin da ke shiga cikin jini, da kuma daidaita daskarewar jini.
Girman ciki a wajen mahaifa abu ne mai matuƙar wuya, wanda ya sanya Sarvesh ta zama abin lura ga likitocin duniya.
Likitoci masu shekaru da dama a aikin likitanci sun yi mamaki sosai bayan duba hotunan juna-biyun Sarvesh.
Farfaɗowa
Ma'auratan sun ce watanni uku da suka gabata sun kasance masu ƙalubale sosai ga dukkan iyalinsu da kuma kashe kuɗi mai yawa.
BBC ta ziyarci gidan Sarvesh a ƙauyen Dastura don ganin ta. Tana hutu, har yanzu tana cikin raɗaɗi tare da babban bandeji a cikinta da aka rufe ɗunki 21 da ta samu daga tiyatar da aka yi mata. Ta kasance tana dogara ga mijinta Paramveer wajen yin komai da suka haɗa da zuwa banɗaki da tashi daga gado har zuwa sauya tufafi.
Sarvesh ta ce ta da ƙyar ta yarda da abin da likitoci suka faɗa mata kan juna biyunta saboda tana ganin al'adarta yadda ya kamata.
Dr. KK Gupta ya bayyana cewa a irin wannan ciki da ke girma a wajen mahaifa , mata kan samu zubar jini mai yawa, "don haka yana ɗaukar lokaci kafin a gano irin cikin."
Bayan yin bincike sosai, likitoci sun yanke shawarar cewa babu wani zaɓi sai tiyata don cire ɗan tayin – idan cikin ya ci gaba da girma, hanta za ta fashe kuma rayuwarta za ta shiga cikin mummunar haɗari.
Saboda rikitarwar lamarin, an ba ma'auratan shawarar su tafi Delhi, babban birnin Indiya domin a yi tiyatar, amma ba su da kuɗin yin hakan. Paramveer ya ce, "Mu talakawa ne, ba zai yiwu mu tafi Delhi mu biya kuɗin ba."
A ƙarshe, bayan watanni uku na fama da Sarvesh ta sha, ƙungiyar likitoci a wani asibitin masu zaman kansu a Meerut sun amince su yi mata tiyata wadda ta ɗauki tsawon minti 90.
Dr. Monika Anant ta bayyana cewa samun irin wannan na da matuƙar wahala.
Ko ana yawan samun irin wannan ciki?
Mace na yin ciki ne idan ƙwan da ta fitar daga mahaifarta ya haɗu da maniyyi, in ji Dr. Mamta Singh, likitan mata kuma farfesa a sashen haihuwa na asibitin BHU da ke Varanasi a ƙasar Indiya.
Bayan ƙwai da maniyyi sun haɗu, ƙwan za iyi tafiya ta bututun da ke ɗaukar ƙwai zuwa mahaifa inda jaririn zai girma.
A wasu lokuta, Dr. Singh ya ce, wannan ƙwai na iya maƙalewa a bututun maimakon ya isa mahaifa ko kuma ya maƙale a saman wata gaɓa ta cikin mace.
A lamarin Sarvesh, jaririn ya maƙale ne a hantarta. Tunda jinin hanta yana da kyau, hakan ya sa ta zama ta iya riƙe tayi a kwanakin farko, amma daga baya tayin ba zai iya rayuwa ba, in ji Dr. Singh.
A duniya, ana samun kimanin kashi ɗaya na juna-biyu da ake samu su zama a wajen mahaifa, in ji Dr. Monika Anant, Farfesa a sashen haihuwa a Patna AIIMS.
"An ƙiyasta cewa a cikin juna-biyu miliyan bakwai zuwa takwas, ɗaya ne kawai zai iya zama ciki da ke girma a hanta," in ji ta.
Kafin lamarin Sarvesh, Dr. Anant ta ce an taɓa ganin inda aka samu juna biyu a jikin hanta sau 45 a tarihi – uku daga cikinsu a Indiya aka samu.
An ruwaito lamarin farko a 2012 a asibitin Lady da ke Delhi.