Alamomi biyar da za ku gane kun kamu da ciwon ƙoda

    • Marubuci, Deepak Mandal
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC
  • Lokacin karatu: Minti 3

Ƙoda na aiki mai muhimmanci a jikinmu. Sukan cire sharar da ke cikin jiki kuma su daidaita aikin ruwa da sauran kayan jiki.

Ƙoda na lura da hawa da saukar jini da kuma taimakawa wajen samar da ƙwayoyin jini da ke safarar jini daga huhu zuwa sassan jiki.

Sai dai mutane kan yi watsi da wasu alamu na ciwon ƙoda, waɗanda idan aka nasarar gane su da wuri za a iya shawo kan matsalar.

Fitsari mai kumfa

Yawan yin fitsari zai iya zama alamar matsala a ƙodar mutum.

A mafi yawan lokaci, idan mutum na yin fitsari mai kumfa akan ce yana da matsalar makasaya.

Sai dai Dr Mohsin Wali ya faɗa wa BBC cewa wasu cutukan ma ka iya jawo yin fitsari mai kumfa.

Ba matsala ba ce yin fitsari mai kumfa lokaci zuwa lokaci, amma idan mutum ya ci gaba da yi bayan ya sha ruwa mai yawa zai iya zama matsalar ƙoda ta yadda ba su iya tace fitsarin da kyau.

Kumburi a cikin jiki

Kumburin idanu da ƙafa ma zai iya zama alamun matsalar ƙoda. Idan aka lura da kumburi a ƙafafuwa bai kamata a yi watsi da shi ba.

Dr. Garima Agarwal, ƙwararren likitan ƙoda, ya ce ya kamata mutum ya kiyaye sosai game da kumburin ƙafa.

Haka nan, kumburin idanu, da fuska, da ƙafa dukkansu alamu ne na ciwon ƙoda.

Hawan jini

A cewar masana, hawan jini alama ce ta abubuwa da yawa.

Sai dai kuma cutar kan shafi aikin ƙoda, abin da ya sa masana ke gargaɗin mutane da su kula da ciwon na hawan jini.

Ciwon suga

Ciwon suga ya fi shafar ƙoda.

Dr. Garima Agarwal ya ce kashi 80 cikin 100 na masu ciwon ƙoda na da ciwon suga.

Kashi 30 zuwa 40 na masu ciwon suga kan samu matsalar ƙoda.

Ciwon ƙoda kan fara ta'azzara ne idan aka samu yawaitar suga a cikin jini a tsawon shekaru.

Gajiya, saurin fushi, tashin zuciya

Jin gajiya, da ciwo a gaɓoɓin jiki, da yawan tashin zuciya za su iya zama alamun matsalar ƙoda.

A cewar ƙwararru, ƙarancin sinadarin phosphorus ne ke jawo ƙaiƙayi a jikin mutum. Shi kuma ciwon ƙoda kan haifar da ƙarancin sinadarin.

Wasu masu ciwon ƙodar kan ji tashin zuciya, kuma ba su jin yunwa.

Masana na cewa kaffa-kaffa wajen cin abinci na taimakawa wajen kare kai daga ciwon.

Kazalika, sun ce yawan motsa jiki, da shan isasshen ruwa, da cin gishiri da suga kaɗan, su ma suna taimaka wa lafiyar ƙoda.

Hanyoyin inganta lafiyar ƙoda

Shan ruwa da yawa

Ruwa na taka muhimmiyar rawa wajen lafiyar ƙoda.

Idan muka sha ruwa da yawa, ƙodarmu za ta samu damar fitar da fitsari mai yawa wanda shi kuma yake fitar da abubuwa marasa kyau daga jininmu.

Haka ma yakan rage haɗarin samuwar duwatsu a ƙoda. Idan mutum ya sha isasshen ruwa fitsarinsa zai yi fari tas ko kuma ruwan ɗorawa mai haske.

Dr. Garima Aggarwal ya ce ya kamata mutum ya sha litar biyu ko biyu da rabi duk rana.

Rage ci gishiri

Yawaita cin gishiri ba shi da amfani da ga lafiyar mutum saboda yana jawo haɗarin kamuwa da hawan jini da kuma ciwon ƙoda.

A dinga nisantar dafaffen abincin da ke da gishiri da yawa.

Rage shan sikari

Idan kuna son guje wa kamuwa da ciwon ƙoda ku ci sikari kaɗan.

Zai ma fi kyau mutum ya guji sikari.

Abubuwa kamar cake, da alawar cakuleti na ɗauke da sikarin da aka sarrafa. Sikari na ƙara teɓa a jiki da kuma haɗarin kamuwa da cutukan ƙoda.

Rage ƙiba

Ƙwararru kan ce ya kamata mutum ya rage ƙiba saboda masu teɓa sun fi shiga haɗarin kamuwa da ciwon ƙoda.

A dinga motsa jiki maras wahala. Abu ne mai muhimmanci saboda yana taimakawa wajen fitar da abubuwa marasa amfani daga jiki.

Idan mutum ya kai shekara 50, haɗarin kamuwa da ciwon suga da hawan jini yakan ragu.

Cin lafiyayyen abinci

A dinga cin kayan marmari, da kayan miya, da 'ya'yan itatuwa. A guji soyayyun abubuwa.

Shan ruwa isasshe, da abinci mai lafiya, da motsa jiki za su taimaka wa lafiyar ƙoda da ma sauran lafiyar jiki.

Guje wa shan magani barkatai

Dr. Garima Aggarwal ya ce: "Mukan ga mutane na sayen magunguna a shaguna ba tare da likita ya ba su umarni ba."

Ya ƙara da cewa wasu kuma na yawan amfani da maganin kashe zafin ciwo.

A cewarsa: "tsofaffi kan sha maganin kashe zafin ciwo, amma kuma wasunsu kan haifar wa ƙoda matsala."