Ko za a iya soke afuwar da shugaban ƙasa ya yi wa mai laifi a Najeriya?

Asalin hoton, Getty Images
Babban ministan shari'a na Najeriya kuma babban lauyan gwamnati, Lateef Fagbemi, a ranar Alhamis, ya ce gwamnati ba ta kammala tantancewa da tabbatar da waɗanda shugaban ƙasar Bola Tinubu zai yi wa afuwa ba.
Ministan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ofishinsa ya fitar ranar 16 ga watan Oktoba, 2025, inda ya yi karin haske kan yadda ake tafiyar da aikin bayar da afuwar shugaban ƙasa.
Sanarwar ta bayyana cewa babu wani mai laifin da ke cikin jerin sunayen mutanen da shugaban ƙasa ya yi wa afuwa da aka saki, daga cikin wadanda ke tsare.
"Mataki na ƙarshe bayan amincewar majalisar magabata shi ne fitar da takardar izinin aiwatar da sakin waɗanda suka amfana da afuwar," in ji Fagbemi.
Me ya janyo hakan?
Tun bayan da gwamnatin tarayya ta sanar da jerin sunayen wasu masu laifi da za a yi wa afuwa, lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin al'umma, musamman kan wasu daga cikin waɗanda ake zargin sun aikata manyan laifuka.
Duk da cewa a cikin sanarwar an bayyana dalilin bincike da sake duba sunayen a matsayin dalilin jinkirin sakin waɗanda aka amince da yi musu afuwa ba, ana ganin jinkirin ba zai rasa nasaba da ce-ce-ku-cen da ƴan Najeriya ke tayi dangane da wasu daga cikin mutanen da aka yi wa afuwa ba.
Bay ga zargin cewa akwai mutanen da aka kama da laifin safarar ƙwaya a cikin jerin, wani abu da ya ɗauki hankali shi ne sanya sunan Maryam Sanda, matar da aka kama da laifin kashe mijinta.
A shekarar 2017 ne kotu ta same ta da laifin. Amma mahaifin mamacin, Alhaji Ahmed Bello Isa, ya bayyana cewa ya amince da a yi mata afuwa kuma a sake ta ba don wani dalili na siyasa ko son kai ba, amma saboda dalilai na jin ƙai da tausayi.
Mutanen da afuwarsu ta fi ɗaukar hankali
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Mutanen da suka fi ɗaukar hankalin ƴan Najeriya a cikin jerin mutane 175 da gwamnati ta ce tayi wa afuwa, su ne
- Herbert Macaulay
Ɗan gwagwarmaya ne da ya shafe tsawon lokaci yana yaƙin neman ƴancin kan Najeriya daga hannun Turwan mulkin mallka.
A shekarar 1913 Turawan Mulkin Mallaka suka same shi da laifi tare da haramta masa riƙe muƙamin gwamnati.
Duk da cewa Macaulay ya rasu a shekarar 1946, laifin da Turawan mulkin mallakar suka same shi da shi ya ya ci gaba da bin sa in ban da yanzu da gwamnatin Najeriya ta yafe masa.
- Maryam Sanda
Ita ce matar da aka yanke wa hukuncin kisa a 2020 bisa samunta da laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello.
- Hon. Farouk M. Lawan.
Tsohon ɗan majalisar wakilin da aka yanke wa hukuncin shekaru biyar a gidan yari a 2021 bisa laifin rashawa da ya shafi shirin "subsidy scam" lokacin da yake shugabantar kwamitin man fetur na majalisar.
- Mamman Batsa.
Mamman Jiya Vatsa babban jami'in soji ne da ya kai matsayin Manjo Janar a rundunar sojin ƙasa ta Najeriya.
Ya kuma riƙe muƙamin ministan Abuja, a tsakanin shekarar 1984 zuwa watan Disamban 1985.
A watan Disamban 1985 ne gwamnatin Najeriya ta zarge shi tare da wasu manyan sojoji tara da haɗa baki wajen cin amanar ƙasar.
Gwamnatin ta gurfanar da su a gaban kotun soji, inda a ƙarshe ta same su da laifukan da aka tuhume su da su, sannan aka yanke musu hukuncin kisa.
A ranar 5 ga watan Maris ɗin 1986 aka zartar masa da hukuncin ta hanyar harbe shi da bindiga.
Shin ko akwai yiwuwar rage mutanen da aka yi wa afuwa?
Masanin shari'a a Najeriya Sulaiman Santuraki ya bayyana wa BBC cewa a matakin da ake a yanzu "shugaban ƙasa na da ƴancin da zai soke sunan wasu da ke cikin jerin waɗanda za a yi wa afuwa.
"Shugaban ƙasa ne kawai yake da ikon da zai cire sunan mutum, amma ko kotu ba ta da ikon cire sunan mutum, domin kundin tsarin mulkin ƙasa ne ya ba shi ƴancin haka" in ji Dakta Sulaiman Santuraki, malami a makarantar horas da lauyoyi ta Najeriya da ke Yola.
Wannan na nuna cewa shugaban Najeriya Bola Tinubu ƙasa na da damar rage yawan mutanen da aka lissafa cikin wadanda za a yi wa afuwa.
A cewar Fagbemi, ba a kammala aiwatar da afuwar ba tukuna, domin aikin yana a matakin ƙarshe na tantancewa da sake duba jerin sunaye kafin a fitar da takardar izinin sakinsu.
Ministan ya bayyana cewa wannan mataki na ƙarshe wanda ke zuwa bayan amincewar majalisar magabata ana yin sa ne domin a sake dubawa da kuma yin gyara ko cire duk wanda aka samu ba ya bin doka ko bai cika ƙa'idojin da doka ta tanada ba.
"Wannan mataki na ƙarshe yana bai wa gwamnati damar sake kallon jerin sunayen domin gyara idan akwai wani kuskure ko wanda bai cancanta ba kafin a aika jerin sunayen zuwa ga shugaban hukumar gyaran hali don aiwatarwa," in ji Fagbemi.
Hanyoyin da ake bi kafin a yi afuwa
A game da matakan da ake bi wajen zaƙulo waɗanda suka cancanta ayi musu afuwa, ƙwararren lauya, Dr Sulaman Usman Santuraki kuma malami a makarantar zama ƙwararren lauya ta Najeriya da ke Yola a jihar Adamawa, ya ce;
- Tattara sunayen wadanda za a yi wa afuwa
Shugaban ƙasa yana da ikon zaɓar waɗanda yake ganin sun cancanci a yi wa afuwa.
- Miƙa sunayen ga majalisar magabata
Bayan tattara sunayen, shugaban ƙasa yana miƙa su ga Majalisar Magabata domin su yi nazari.
- Kafa kwamitin bincike
Majalisar ko gwamnatoci kan kafa kwamitin musamman domin bincike da tattara bayanai kan waɗanda ake so a yi wa afuwa inda zai yi nazarin dalilan neman afuwa, tarihi na laifi, da yanayin wanda ake son ayi wa afuwa daga nan kwamitin ya bayar da shawara ga shugaban ƙasa ko gwamna.
- Yanke hukunci
Wannan yana nuna cewa shugaban ƙasa shi ne babban mai hukunci a harkar afuwa, amma yana la'akari da shawarar kwamitin.











