Hotuna sun nuna yadda Iran ke inganta tsaron hanyar shiga rumbun nukiliyarta

    • Marubuci, Emma Pengelly
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Verify
    • Marubuci, Ghoncheh Habibiazad
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Persian
  • Lokacin karatu: Minti 3

Hotunan tauraron ɗan'adam sun nuna yadda Iran ke ƙara inganta tsaron rumbunta na makaman nukiliya da ke ƙarkashin ƙasa.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da zaman fargaba ke ƙaruwa yayin da ake ci gaba da tattaunawa tsakanin Iran da Amurka, inda shugaba Donald Trump ke barazanar ɗaukar matakin soji kan Iran ɗin muddin ba ta amince da sabon yarjejeniya kan shirinta na nukiliya ba.

Waɗannan hotuna da cibiyar kimiyya da tsaron ƙasa da ƙasa ta fara nazari a kansu, sun nuna yadda ake ƙara inganta hanyoyin shiga ƙarkashin ƙasa a tsaunin Kolang Gaz La - wanda aka fi sani da tsaunin Pickaxe.

Ƙwararru sun ce watakila an tsara wannan tashar nukiliya ne don kare makaman Iran da kuma sinadaran uranium, saboda har yanzu ba a san manufar samar da ita ba.

Iran ta nanata cewa ɗaukacin shirinta na nukiliya an yi shi ne don zaman lafiya sannan ta musanta cewa tana shirin ƙera makaman nukiliya.

Sai dai, Trump ya bayyana a watan Yunin 2025 cewa bai fi kasa da wata ɗaya ba Iran ta mallaki makamin nukiliya, lokacin da ya ba da umarnin far wa cibiyoyin nukiliya na ƙarkashin ƙasa uku lokacin da yaƙi na kwanaki 12 ya ɓarke tsakanin Iran da Isra'ila a bara.

Trump ya ce hare-haren sun rage ƙarfin Iran wajen mallakar nukiliya, sai dai jami'an Iran na tunanin fara "gina sabon rumbun nukiliya".

Cikin wuraren da Amurka ta kai wa hari a Iran a watan Yunin 2025, sun haɗa da tsaunin adana nukiliya na Pickaxe da kuma na Natanz mai nisan kilomita biyu daga arewacin ƙasar.

Wani hoton tauraron ɗan'adam da aka ɗauka ranar 10 ga watan Fabarairu ya nuna kamar wani sabon wuri da ake ginawa a kofofin shiga tsaunin Pickaxe.

Ana kuma iya ganin injin miƙa yashin da aka kwaɓa na gini a wurin, ƙwararru da dama musamman daga cibiyar tattara bayanan sirri na Maiar a Birtaniya sun amince da hakan.

A can wani rumbu na ƙarkashin ƙasa, ana iya ganin kankare da kuma ƙasa da aka kwaɓa ana gini.

Ƙwararru daga IS sun ce waɗannan sauye-sauye za su ƙara inganta hanyoyin ƙarkashin ƙasa da kuma ƙarin tsaro ga duk wata barazanar hari da za a kai.

Sun ce ci gaba da kasancewar injunan gine-gine na nuna cewa ba yanzu za a fara aiki da rumbun nukiliyar ba.

Hotunan tauraron ɗan'adam sun nuna yadda ake ci gaba da aikin gyara rumbunan Natanz da Isfahan don kare su daga wata barazana.

A Isfahan, an toshe dukkan hanyoyi da za su shigar da mutum cikin rumbun, kamar yadda hotunan tauraron ɗan'adam suka nuna.

Toshe kofofin shiga cikin rumbun zai taimaka wajen kare su daga duk wata barazanar hari ta sama, in ji ISIS, da kuma taimakawa wajen kare hari ta ƙasa da aka kawo don kwace ko kuma lalata sinadarin uranium da ke ciki.

A can cibiyar nukiliya ta Isfahan, An gina wani sabon rufi. Ginin wanda Isra'ila ta far wa a bara, an yi tunanin cewa ana amfani da shi wajen samar da wasu sinadarai.