Mene ne tasirin ƙara yawan shekarun ritayar likitoci a Najeriya?

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar likitoci ta Najeriya wato NMA, ta yi maraba da matakin da shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu, ya dauka na kara shekarun ritayar kwararrun ma'aikatan kiwon lafiya a kasar, daga shekara sittin zuwa sittin da biyar na haihuwa.
Shugaban kungiyar likitocin ta Najeriya Farfesa Bala Muhammad Audu, wanda kuma shi ne shugaban jami'ar kimiyyar lafiya ta tarayya da ke Azare a jihar Bauchi, ya shaida wa BBC cewa gwamnatin Najeriya ta amince da batun Karin shekaru ga jami'an lafiya ne bisa la'akari da cewa hakan na da matukar amfani.
Ya ce, "Anjima ana tattaunawa akan batun karin shekarun ritayar, sannan gwamnati ta yarda, sannan kuma akwai tasirin da matakin hakan za iyi kamar misali nan da shekaru biyar akwai likitoci 2000 da za su yi riyata, sannan babu wadanda zai maye gurbinsu, a yanzu haka likita guda na duba marassa lafiya 60 a rana guda."
" A halin da ake ciki yanzu adadin likitoci na raguwa sannan kuma al'umma na karuwa, to idan har aka ce ba a kara shekarun ritaya ba ai akwai babbar matsala, a don haka um mun ji dadi matakin shugaban kasar na kara shekarun ritayar ba ma ga likitoci ba har ma da sauran jami'na lafiya, don hakan zai kara ba su damar kula da marassa lafiya, kuma kafin su cimma shekarun ritayarsu wasu zasu rika tasowa ta yadda za su rika maye gurbin wadanda suka tafi." In ji shi.
Shugaban kungiyar likitocin, y ace yana ganin an amince da wannan doka ce saboda ba wa wadanda ke da karfin ci gaba da aiki damar ci gaba da aikinsu na taimakon al'umma.
Farfesa Bala Muhammad Audu, ya ce gwamnatin tarayya da duba alfanun da wannan mataki zai yi shi ya sa ta amince.
Harakar kula da lafiyar al'umma a Najeriya dai na bukatar ma'aikata ingantattu da kuma wadatarsu a fadin asibitocin kasar, sai dai kuma rashin wadatarsu da ƙarancin kayan aikin lafiya wani babban al'amari ne a Najeriyar.
Yawanci likitoci da sauran jami'na kiwon lafiya a Najeriya na samun aiki ne ko neman sa a kasashen yankin gabas ta tsakiya da nahiyar Turai inda ake biyan albashi da alawus mai tsoka.
Rashin wadatar likitoci da sauran jami'an fannin lafiya, ya dade yana ci wa 'yan Najeriya tuwo a kwarya, tare da karancin kayan aiki, da batun karancin albashi da rashin kyautata walwalar likitoci da ke janyo yajin aiki.
Rahotanni daban-daban sun sha nuna cewa akwai daruruwan likitoci 'yan Najeriya da ke aiki a kasashen waje, wasu ma har sun yi fice saboda kwarewarsu da kuma gudummawar da suke bayarwa wajen kare lafiyar jama'ar kasashen da suka je.
Abin jira a gani shi ne ko wannan mataki na kara shekarun ritayar likitoci da sauran jami'an lafiya a Najeriyar zai inganta bangaren kula da lafiyar al'mmar kasar? Sannan kuma ko hakan zai sa ma'aikatan lafiyar da ke bulaguro zuwa wasu kasashe don neman aiki su daina?











