Najeriya: Likitoci na tururuwar barin ƙasar ana tsaka da yajin aiki

Asalin hoton, Getty Images
Yayin da likitoci masu neman kwarewa a Najeriya ke ci gaba da yajin aiki a manyan asibitoci, a bangare guda ma'aikatan kiwon lafiyar da dama na yunkurin ficewa daga kasar zuwa kasashen waje.
Kawo yanzu babu tabbas kan adadin likitoci da ke wannan yunkuri amma wasunsu na cewa matsalolin da suka haifar da yajin aikin na daga cikin abubuwan da suka sanya su daukar matakin gwada sa'arsu a kasashen waje.
BBC Hausa ta ziyarci wani wuri a Abuja babban birnin Najeriya, inda ake tantance tarin likitocin da ke zuwa domin tantance su, da niyyar samun aiki a kasar Saudiyya.
Likitoci maza da mata daga sassa daban-daban na Najeriya na zuwa wajen dauke da takardunsu, domin ganin sun samu damar tafiya Saudiyyar domin gwada sa'arsu.

Asalin hoton, NMOH
Wani likita da ke kan layi yana jiran a tantance shi, ya shaida wa BBC Hausa cewa yana son ya je waje ne domin ya ji labarin cewa an fi kula da likitoci a can.
Ya ce akwai matsaloli da dama da suke fuskanta a Najeriya, kamar wutar lantarki da kan tsayar da al'amura cik, yayin da suke tsaka da aiki, ga kuma karancin albashin da suke fama da shi, da baya isarsu wajen biyan bukatun yau da kullum.
A kullum dai gwamnatin Najeriya na cewa tana iya bakin kokarinta wajen inganta bangaren na lafiya, abin da likitocin ke cewa zance ne kawai da ba ya wuce fatar baka.
Ba sabuwar matsala bace

Asalin hoton, Wasu likitoci a Najeriya
Likitoci a Najeriya dai sun jima suna fita wasu kasashen duniya domin gwada sa'arsu, abun da masharhanta ke alakantawa da rashin kyakkyawan tsarin kula da lafiya a Najeriya.
Rahotanni daban-daban sun sha nuna cewa akwai daruruwan likitoci 'yan Najeriya da ke aiki a kasashen waje, wasu ma har sun yi fice saboda kwarewarsu da kuma gudummawar da suke bayarwa wajen kare lafiyar jama'ar kasashen da suka je.
Wasu daga cikin jama'a dai na da ra'ayin cewa akwai tsantsar rashin kishin kasa tattare da wadannan likitoci da ke barin ƙasarsu don zuwa su yi aiki a wasu kasashen yayin da aka fi bukatarsu a gida.
Yajin aiki da korafe-korafe a bangaren lafiya ba sabon abu ba ne, kuma ana ganin cewa hakan ya taimaka wajen sake durkushewar bangaren, musamman a wannan lokaci da ake tsaka da fama da annobar korona.











