Yadda jam'iyya mai mulki ta sha kaye a Botswana bayan shekara 58 tana mulki

Asalin hoton, AFP
Masu zaɓe a Botswana sun ki zaɓar jam'iyyar da ta shafe tsawon shekara 58 tana mulki a ƙasar, a wani sakamakon zaɓe da ya ba da mamaki a ƙasar mai arzikin demon da ke kudancin Afrika.
Jam'iyyar Botswana Democratic Party (BDP) – da ke kan mulki tun bayan samun ƴancin kai a shekarar 1966 - ta lashe kujera ɗaya a majalisar dokokin ƙasar zuwa safiyar Juma'a. Jam'iyyar UDC ce ke shirin maye gurbinta.
Shugaba Mokgweetsi Masisi ya amsa shan kaye, inda ya ce ta fito ƙarara cewa jam'iyyarsa ta "faɗi warwas" a babban zaɓen da aka gudanar ranar Laraba.
Duk da sauye-sauye da aka samu a Botswana, taɓarɓarewar tattalin arziki da kuma ƙaruwar rashin aikin yi su suka janyo jam'iyyar ta ƙasa samun farin jini a tsakanin al'umma.
"Zan ja gefe a tsanake kuma zan ba da haɗin-kai wajen miƙa mulki ga sabon gwamnati," in ji Masisi a wani taron manema labarai ranar Juma'a.
"Ina taya ɓangaren adawa murnar samun nasara kuma na amince na sha kaye. Ina alfahari da tsarin dimokraɗiyyarmu kuma ina mutunta zaɓin al'umma."
Ya buƙaci magoya bayansa da su kwantar da hankali da kuma mara wa sabuwar gwamnati baya.
Jam'iyyar ta UDC, wadda lauya mai kare hakkin ɗan'adam Duma Bako ke jagoranta, ta lashe kujeru 25, a cewar alkaluman da aka fitar.
Ana hasashen cewa jam'iyyar za ta samu kujeru 31 don samun rinjaye a majalisar.
Ta yi alkawarin ɓullo da sabon tsarin tattalin arziki da zai samar da ingantattun ayyukan yi da kuma za su bai wa ƴan ƙasar wadatattun kuɗaɗe.
Kgoberego Nkawana, wani sabon ɗan majalisa da aka zaɓa a jam'iyyar UDC, ya faɗa wa shirin BBC Newsday cewa matasa da yawa a Botswana na ci gaba da zama babu aikin yi duk da irin albarkatun lu'u lu'u da Allah ya yi wa ƙasar da kuma ɓangaren yawo buɗe da ke ci gaba da samun karɓuwa a faɗin ƙasar.
"Marasa aikin yi na ƙaruwa kuma mutane na rayuwa hannu baka hannu kwarya saboda babu ayyuka. Matsalar ta yi munin gaske," in ji Nkawana.
Jam'iyyar ta yi alkawarin samar da ayyukan yi da za su kai 450,000 zuwa 500,000 cikin shekara biyar.
Jam'iyyar Botswana Patriotic Front (BPF), wadda tsohon shugaban ƙasar Ian Khama ke mara wa baya da ta ɓalle daga jam'iyyar Botswana Congress (BCP), ta samu kujeru bakwai zuwa yanzu.
Yayin da ya kasance ƴan majalisa ne ke zaɓar shugaban ƙasa a Botswana, Boko na kan hanyarsa ta zama shugaban ƙasa na gaba da zarar majalisar ƙasar ta yi zamanta na farko.
Magoya bayan UDC na ci gaba da murna a Gaborone, babban birnin ƙasar da kuma wasu sassan ƙasar.
Masisi - wanda ke mulki tun 2018 - ya jagoranci yaƙin neman zaɓe da jam'iyyar ba ta samu nasara ba.
Shugaban ƙasar ya ta'allaka kamfen ɗin sa a kan cewa jam'iyyarsa za ta kawo sauyi, sai dai babu masu zaɓe isassu da suka amince cewa BDP za ta yi abin da ake so a ƙasar.
Ana sa ran hukumar zaɓen ƙasar za ta sanar da sakamakon zaɓe an jima a yau.











