Bostwana ta yi barazanar aika giwa 20,000 Jamus

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban ƙasar Botswana ya yi barazanar tura giwa 20,000 zuwa Jamus a wata taƙaddama a tsakaninta da ƙasar.
A farkon wannan shekarar ne, ma'aikatar muhalli ta Jamus ta ba da shawarar cewa kamata ya yi a tsaurara matakai wajen shigar da lambobin karramawa da aka yi su sassan jikin dabbobin dajin da aka yi farautarsu.
Shugaban Botswana Mokgweetsi Masisi ya shaida wa wata kafar yaɗa labaran Jamus cewa matakin zai jefa mutanen ƙasarsa cikin talauci ne kawai.
Ya ce adadin giwaye ya yi yawa ne saboda ƙoƙarin alkinta muhalli, farautar kuma tana taimakawa wajen rage adadinsu.
Ya kamata Jamusawa su "zauna tare da dabbobin, kamar yadda kuke ƙoƙarin faɗa mana," in ji shugaba Masisi ga jaridar Jamus Bild. "Wannan ba abin wasa ba ne."
Botswana, gida ce ga kusan kashi ɗaya cikin uku na ɗaukacin giwayen duniya - sama da 130,000 - fiye da yadda take da sararin kiwonsu.
Giwayen na yin ɓarna ga dukiyoyi, suna cin amfanin gona tare da tattake mutanen karkara a yankunan, in ji shugaban.
A baya dai, Botswana ta bai wa maƙwabciyarta Angola giwa 8,000, sannan ta bai wa Mozambique wasu ɗaruruwan giwaye, a matsayin hanyar rage yawansu a ƙasar.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Za mu so mu bayar da irin wannan kyauta ga Jamus," in ji Masisi, ya ƙara da cewa ba zai yarda da a'a a matsayin amsa ba.
Ministan namun daji na Botswana Dumezweni Mthhimkhulu a watan da ya gabata ya yi barazanar tura giwaye 10,000 zuwa filin shakatawa na Hyde da ke Landan.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin dabbobi suna jayayya cewa farautar dabbobi da harbin su sannan a sarrafa sassan jikinsu kamar kai ko fatarsu, a matsayin lambar karramawa, zalunci ne kuma ya kamata a hana.
Jamus ita ce ƙasar Tarayyar Turai ta fi shigar da lambobin karramawa da aka yi su da sassan jikin giwa a nahiyar Afirka, a cewar wani rahoto na shekara ta 2021 na ƙungiyar Humane Society International.
Botswana ta haramta yin hakan a shekarar 2014, amma ta ɗage haramcin a 2019, bayan fuskantar matsin lamba daga al'ummomin yankin.
A yanzu dai ƙasar na fitar da kason farautar dabbobi a duk shekara, inda ta ce tana samar da kyakkyawar hanyar samun kuɗin shiga ga al'ummar yankin, don haka ba su da sha'awar farautar namun daji, kuma tana da lasisi da kuma kula da su sosai.
A baya, an riƙa amfani da giwaye don yin abincin dabbobi.
Wata mai magana da yawun ma'aikatar muhalli a birnin Berlin ta shaida wa kanfanin dilancin labaren AFP cewa Botswana ba ta nuna damuwa da Jamus kan wannan batu ba.
Ta kara da cewa, "Saboda mummunan asarar da ake samu na bambancin halittu, muna da wani nauyi na musamman na yin komai don tabbatar da cewa shigo da lambobin karramawa da aka yi su sassan jikin giwa na farauta ya dore kuma ya zama doka," in ji ta.
Ma'aikatar, ta ci gaba da tattaunawa da kasashen Afirka da dokokin shigo da kayayyaki suka shafa, ciki har da Botswana, in ji kakakin.
Ostireliya da Faransa da kuma Belgium na daga cikin ƙasashen da suka haramta cinikin lambobin karramawa da aka yi su da sassan jikin giwa da aka yi farauta
A watan Maris, 'yan majalisar dokokin Burtaniya sun kada kuri'ar amincewa da dokar hana shigo da irin lambobin karramawar nan , amma dokar ta ƙara yin nazari kafin ta zama doka.
An sanya alƙawarin hana shigo da lambobin karramawa da aka yi su da sassan jikin giwa a cikin ƙundin tsarin zaɓe na shekarar 2019 na jam’iyyar Conservative.
Ita ma Botswana da makwabciyarta Zimbabwe da Namibiya, sun yi zargin cewa kamata ya yi a bar su su sayar da tarin giwayen da suke da ita, ta yadda za ta samu kudi daga dimbin giwayenta.
Ƙasashe a gabashin Afirka, da kuma ƙungiyoyin kare hakkin dabbobi, sun yi adawa da hakan, suna masu cewa hakan zai karfafa farautar dabbobi.











